DASHEN ZUCIYA

512 13 1
                                    

💔 *DASHEN* 💔
       *ZUCIYA*

   
   
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_👄

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘


3⃣

Haka suka fito kowa kagani hankalinsa a tashe yake ciki har *Nuru* daya kwallafa ransa akan Bisma amma bashida yadda zaiyi tunda *Hamdan* ya rigashi dole ya hakura saboda Bayaso su samu matsala da Hamdan, amma abun takaici Bisma takasa gane cewa *Nuru* sonta yakeyi ita a tunaninta kawai jininsu ne yazo daya shiyasa ya shaku da ita, tafe suke har filin jirgin saman dake US dayake duk gari guda suka nufa, amma Hamdan da Nuru scholarship ne gwamnatin Zamfara ta daukesu saboda kwazonsu da haxaka badon iyayensu sun gaxaba, Nuru ne zan iya cewa dan talaka ne amma kuma mai wadatar zuciya, anyi musu hakanne don kara musu karfin gwiwa, sannan suna fatan idan sukaje suka dawo zasuyiwa gwamnatin Zamfara hidima.

*KASA NIGERIA*

A filin jirgi suka sauka acikin garin Gusau, inda yan'uwa da abokan arziki suka cika dankam don tarban yayan gata, Nuru yashiga damuwa wacce baxai misaltu ba amma duk Wanda yaga bisma da Hamdan saiya gane cewa suna cikin farinciki, nan danan su kayiwa junansu sallama, kowa yatafi inda matsuguninsu yake, anyi murna kwarai daga Duka bangarorin,
Bayan wasu yan kwanaki da dawowarsu Bisma tadamu kwarai saboda rashin ganin Hamdan, Nuru ne ya sauka daga cikin Motarsa ya k'wank'wasa  kofar gidansu Bisma zaune take a tsakar gida, mai gadi ya wage kofar gidan "Dan Allah bisma nake nema ko tananan?"
Mai gadi ya juya yace eh bari in sanar da ita,
"Ranki ya Dade kinyi bak'o" cikin zumudi tace "Kace ya shigo" duk a tunaninta Hamdan ne amma sai taga ak'asin hakan,
Nuru tagani yana shigowa da hancin Motarsa lokaci guda taji ranta yayi mugun baci amma saita boye dariya tayi tace "Manyan kasa Ashe Baka manta daniba" Lemo tasa aka kawomai da ruwa.

Dariya Nuru yayi yace "Banda abunki Bisma ai zumunchin mu bamai karewa bane, fatana shine Allah yakara hada kanmu baki daya"
"Tabbas wannan haka yake Nuru banida Wata kawa koh aboki Wanda ya wuce kai, ina iya gayama duk wani sirri nawa batareda naji wani dar acikin zuciyana ba, Sai kuma Hamdan Wanda yak'asance abokin rayuwana bantaba son wani da namiji yadda nakeson Hamdan ba, I really love him amma sai gashi yau Kusan satinmu uku babu Hamdan babu labarinshi koh wayarsa nakira bana samu kuma bansan yaxanyi ba, nasan ba darajata bace inje gidansu da sunan ina nemansa bansan dawani ido zasu kalleni ba".
Shuru ne yadan ratsa Nuru bakaramin dadi yajiba, yadda yaji Hamdan bai damuda Bisma ba, "My friend hakuri zakiyi zuwa wani lokaci kila dakwai wani Abu so strange daya rikeshi but nasa

DASHEN ZUCIYAWhere stories live. Discover now