DASHEN ZUCIYA

458 13 0
                                    

💔 *DASHEN* 💔
       *ZUCIYA*

   
   
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_👄

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘

4⃣

Nasan everything shall be well with him", kallon Nuru Bisma takeyi yadda duk ya damuda lamarinta yadda yanuna rashin jin Da dinsa akan rashin zuwan Hamdan, sun danyi hirarsu wacce batada maraba data masoya, Sallama sukayi daga bisani ta rakashi har gaban Motarsa, harya fita tana dagamai hannu cikin gida Bisma tashiga tana wasa da yan yatsunta tana wakan christ brown, cikin dakinta tashiga tafada kan gado, wayarta ta dauko ta hau kiran lambar Hamdan amma bata shiga, saidai taji the number you're trying to call is currently switch off nan ta zabga uban tagumi Wanda ya nuna tana cikin tashin hankali.

Gefe na koma ina tunanin yadda Hamdan yayi barin iska da lamarin Bisma, meyake nufi da itane yana nufin duk love din da sukasha a Florida USA duk ta bogi ce?
Abunda nikaina HUMAIRAH nakasa bawa kaina Amsa kenan, Chatting takeyi Wanda yaxame mata jiki, bata wannan GRP bata wancan saidai yawancin group dinta na matane sannan kuma na novel ne, wani novel ta tsinci kanta da karantawa, Wanda yayi shige da yanayin aikinta Wato NEESMA'A WAH NUSHUUF,
Wannan littafin ba karamin tafiya yayi da imaninta ba,
Karar bell din dakinta taji hakan yasata kashe data, ta mike ta bude kofa, Nabil tagani tsaye yanata dariya Wanda tarasa gane ma'anar hakan batayi kasa gwiwa ba Wajen cewa
"Nabil lafiyanka sai wani dariya kakeyi saikace Wanda akace ga Aljanna shiga?"

Nabil yace
"Aunty Bisma dole inyi farin ciki tunda Allah yasa appointment dinki na aiki yafito shine nace bari inzama mutum na farko daxaiyi miki albishir"
"Naji dadii kwarai nabil amma hakan baxai sani farinciki ba matukar banga Hamdan ba, shine mutum na farko daya karbi ragamar zuciyata, amma tunda muka Dawo yau kusan sati uku bashi ba labarinsa".

Dukda nabil karamin yarone Wanda shakarunsa bazasu wuce Sha takwas ba, yasan cewa yar'uwarsa tana cikin halin kunci na rashin mosoyinta,
Washe gari suna zaune a katuwar darduma wacce itace tazama kamar dining dinsu anan ake baje kayan abinchi kuma kowa anan yake zama doncin abinchin,
Daddyn sune zaune Bayan sun kammala cin abinchi,
"yabo ya tabbata ga Allah madaukakin tsarki dayasa Bisma ta karkare karatunta, nazama kwararrar likita a fannin maza da mata, har ila yau gashi tasamu aiki a Federal medical center dake garin Gusau, an dauketa a matsayin consultant, yanzu Abu daya yarage mata a Rayuwa shine tafito da mijin aure Wanda shine zaisa tacika mace".

Yana zuwa nan yayi shuru, Bisma koh tashiga rudani
"mai daddy yake nufi dani toh ni yanzu idan ance infito da miji yazanyi after ol Hamdan ya watsar dani dukda moment din da mukayi spending tare a USA"
Muryan daddy ne yadawo da ita daga tunanin da takeyi, "Bisma yanzu Sha'awara yarage naki kiyi gaggawan fitarda miji don hadaku zanyi dasu Rumaisa da Ikram duk inyi muku aure in huta da surutun mutane".

DASHEN ZUCIYAWhere stories live. Discover now