DASHEN ZUCIYA PG 29

232 5 0
                                    

💔 *DASHEN* 💔
       *ZUCIYA*

   
   
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_👄

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘

        2⃣9⃣

"Na kira su hajiya na sanar dasu amma batace dani komai ba nakira alhaji na fadamai shima shuru yayi ya kashe wayar kinsan irin zaman da akeyi na doya da manja" Bisma ta dafe kai tace
"ai case bata kareba yanzu zan sanarda hukuma ayi mai tarariya" Hamdan ya rude waya kawai bisma ta dauka takira Acp Bello ta sanar dashi batareda bata lokaci ba suka isa gidan su hamdan.
Hamdan ya kalli NURU yace "Dan Allah kasa baki kar a kama kannina".

NURU yace "Kanaso kacemun kafison kanninka akan ran matarka? Oh Hamdan banga laifin yan'uwanka ba Dan sunzo sun Daki Ruma da goyon bayanka kuma kaima saika fuskanci hukuma" tsaki nuru yayi yaja hannun matarsa suka shiga inda Ruma take Yadda ta koma abun tausayi cikin yan lokaci ta rame takoma Kamar bulala, bacci suka tarar tanayi yan gida duksun hallaro da wayanda zasuyi jinya, bisma kuwa zuciyarta ce ke tashi bayan sun gaisa ne Ummi ta umurci bisma dataje gida don taga kaman yar tata takamu.

Haka Nuru ya rike hannun bisma har gida, ya bude mata murfin mota ya dauketa cik har cikin gida sannan ya ajiyeta, kofin tea ya hado mata mai zafi tasha gaba daya ya amoyo mishi ajiki sai kakari takeyi haka, nuru dukya rude yarasa mezai fara yiwa bisma, gashi Da gashi sai ita a gida, abin ne gwanin tausayi.
Tissue ya samo ya goge mata baki tareda yimata sannu koh magana bata iyawa, daukanta yayi cik zuwa toilet ya gyra mata jiki shima ya gyra nashi, suka shiga Daki ya taimaka mata tasa kaya harda sweeter saboda sanyi datakeji haka ya daura ta bisa gado ya lullubeta da bargo.

Fita yayi falo ya fara kwashe aman datayi ya gyra koh ina yasa air freshener Dakin ya dau kamshi, sallama yaji yace Am coming budewan Da zaiyi yaga abokinsa Faisal yace "Abokina lafya naganka haka a hargitse?" Cewan abokin NURU.

Nuru yace "dole ka ganni haka my princess ce ba lafya amai tayi shine na kwashe nake gyara wajen"
"Lallai nema abokina kazama mijin tace mace kake yiwa yik'i haka ina aini baxan iyaba tab Wallahi kabi a hankali koh an jikama kasha"
NURU ransa yayi mugun baci yarasa abunda ke masa dadi arai yace "Dakata Faisal banason maganar sha shanci me kake nufi toh bari kaji Wallahi akan bisma babu abunda bazanyi ba yadda kake ganina yanzu kitchen zan shiga abunda takeso shizan dafa mata".

Faisal yayi sarere, daman shi halinsa kenan mazigi ne makwangari, haka yakebi yake lalata auren abokansa amma dayake nuru yasan abunda yakeyi ya sakar mai da gwiwa, "Toh mijin hajiya ni nayinan sai anjima ka gaisheta idan ta farfado, Nuru saboda haushi bai iya cewa komai ba.

Nuru yashiga kitchen ya dafa musu abincin daza suci, bayan ya kammala yashiga mater bedroom dinsa ya tada bisma cikin dabara harta soma bude idanunta, murmushi tayi ta sakkoh riketa yayi saboda bayaso wani Abu ya sameta brush tayi sannan ta dauko abunyin test na ciki don duk symptoms din da takeji namai ciki ne.

Ilai haka tayi test din cikin ikon Allah yanuna Jan danja, dukda NURU baisan abunda yake nufiba amma saiyaga bisma tana murmushi shima saiya fara, juyowa tayi ta rungume shi hartana jin bugawan zuciyarsa, tace "My king da a asibiti muke da wasune zasu tayamu murna amma dayake likita ce da kanta ina maka albishir da cewa ina dauke da juna biyu Wato danmu nidakai".

Wani ihun dadi NURU yayi yace "Wasu sun rasa gashi mu mun samu, don haka dole muyiwa annabi salati" haka sukayi NURU yaci gaba da shafan cikin haka bisma tadinga fama yau lafya gobe ciwo dukda bawani kwantar da ita yakeba, bayan kwana biyu aka sallami ruma amma sai akai shinkafi da ita saboda sai anyiwa tufkar hanci.

Baitu ce kwance bayan SATI ciwo yakici yaki cinyewa, bisma tace "Baitu dole ayimiki dashen zuciya gida" takoma da damuwan halinda Baitu take ciki NURU yace "princess gaskiya ki rage tunani akan patient dinnan wai ita kadaice kike dubawa? Haba gaskiya ki kula saboda lafiyarki data abunda ke cikinki, ko kuma ki ajiye aiki har saikin haihu".

Cikin rudu da tashin hankali, Bisma tace
"My king katuna Alkawarin dakayimun akan cewa zaka tsaya tsayin daka ganin na comma nasara akan aikina amma meye na canza raayi katuna rai zan ce ta"
"BISMA dakata akanki da abunda ke cikinki bakida abunda zakice mini saboda dole kidaina zurfafa tunani"
Bisma tace karka damu my king ana dasa mata zuciya shikenan zan dauki Hutu pls kasaki ranka.

DASHEN ZUCIYADove le storie prendono vita. Scoprilo ora