DASHEN ZUCIYA

416 6 0
                                    

💔 *DASHEN* 💔
       *ZUCIYA*

   
   
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_👄

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘

5⃣

Bata iya amsawa ba saboda, wani haushin kanta da takeji tashi tayi lokacin kowa yabita da kallo, kafin ta karasa daki taji karar wayarta dafe kai Tayi a tunaninta Hamdan ne yake kiranta amma saitaga Akasin haka Nuru ne yaketa kiranta amma takasa ta daga wayarsa saboda abubuwan dake dawainiya da zuciyanta, da shigarta daki ta taradda ikram kwance sai minshari takeyi wani wawan Duka ta daka mata a duwawu tace "Maza ki tashi ke har wani lok'acin bacci gareki toh bari kiji in gayamiki abunda baki sani ba Daddy aure zaiyi mana kuma yace kowacce cikinmu tafito da miji don yagaji da surutun mutane",

Ai ikram batasan lokacin data nanawa Rumaisa dukaba, tace               "maxa kitashi kiji wani sabon Al'amari daddy yace kowaccen mu tafito da miji, Zare ido rumaisa tayi tace kalu inna-nallahi wa'inna ilaihir rajiun, tashi tayi ta zauna daga ita sai half vest,
Ikram tace
"a gaskiya nidai a yanzu saidai Daddy ya zabamun miji Donni ubanwa nake saurara bare akaiga wani zancen aure tab wanga abun Alkhairi haka dame yayi kama?".

Bisma dake zaune tace "hmm ke ikram saurayinne bakida toh ni wallahi Wallahi inada amma tunda muka zakkuwa kasar nan muka rabu airport shikenan niya babu waya babu sako, ke koda lambarsa nakira bata shiga switch off, kinga damuwata guda kenan,"
Rumaisa da karatun ya kare mata cikin kwakwalwa tace "Nifa bari kuji wani zancen banza zancen wofi chan kasar America saurayin nawa yake acan yake karatu muna masifan son juna amma kwana biyu nima shuru, ikram bakijin wayar damukeyi dashi, wallahi 24 waya mukeyi Donni bani sauraran kowa cikin garin ga mazan garinnan koh yan ataru a lalace".

Wata safiyar Asabar gari ya daure yayi dind'um, saboda wani gagarumin hadari dake haduwa daga gabas, amma Bisma, Rumaisa da ikram shirin fita sukeyi, basu damu da yanayin garinba lace iri daya sukasa amma kowacce da kalan nata, biki akeyi na yayan Hutu yara masuji da kyau da isa basuda maraba da larabawa Wato zuri'a Wamban Gusau kenan, amma in fedewa mai karatu wani sirri Bayan fari wallahi da dukkan su bola  za'ayi  dasu dama dama ikram, gasu gajeru Kamar a kife da kwarya.

Fitowa suk'ayi saida suka ratsa tacikin falon Ummi suka gaidata binsu kawai takeda kallo tarasa wacce zata yaba cikin su, tashi tayi ta zagayesu tace "Tabbas dawisu daban yake cikin tsuntsaye, Giwa kenan dole aganku a kyaleku, Tabbas kunyi kyau yadda ake bukata amma kun mata Abu guda" daki tashiga ta dauko Wasu warwaraye, Masu kyau da tsada tace wannan wani sirrine dake karawa mace kyau duk inda tayi sai an kalleta, Bisma tsaye tayi amma ranta yayi masifan sosuwa ganin yadda yan'uwanta sukayi mugun kyau.

DASHEN ZUCIYAWhere stories live. Discover now