DASHEN ZUCIYA

741 14 0
                                    

💔 *DASHEN* 💔
       *ZUCIYA*

   
   
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_👄

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘


2⃣

Nikam nece kwarai, alokacinda suka kusa kammala karatun su ne, suka xama hanta da jini soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu, Wanda tazame musu jiki kowa maganarsu yake dama suyi aure, Hamdan ne mai cewa "ai idan kukaga ban auri Bisma ba toh ajaline yaxomun baka tatan,
"Banda abunka mai sanyina ai rana daya zamu mutu mubar duniya, don inhar katafi kabarni Rayuwa zata kasance mai zafi a gareni".

"Haka nima Bisma bana fatan ki tafi kibarni inrayu dawa ingawa inji dadii, Dan Allah adaina maganan mutuwa saboda hankalina yana mugun tashi Gashi muna gab da mukammala karatu Mu koma gida Nigeria, Meye next target dinki?"
Bisma kallon soyayya takemai
"Ai banida Wani buri anan gaba saina inganni tareda dakai matsayin matarka halak malak dinka".

"Gaskiya ne Bisma fatana Allah ya albarkaci soyayyar Mu, Allah yasa iyayen Mu su aminche ma bukatar mu cikin kankanin lokaci donnni ta bangarena banida wata matsala".

"Nima haka *Hamdan* nasan iyayena bazasu ki abunda nake muradi ba, tun yanzu sunfara yimun maganan aure kuma nasanar dasu cewa nifa nayi gamo da katar a kasar Florida kuma insha Allah shine Wanda za'ayi dashi".

"Nikam ai Tuni nayi introducing dinki a family na, yanzu haka kowa yakosa daya ganki, Kinsan farin jini gareki da banyi da gaske ba inajin da NURU yamun kafa, dayake jarumine nidin shiyasa na rike fire".

Dariya Bisma tayi tace, "nikam kana bani mamaki waikai a tunaninka nuru sona yake? Toh koh kafado kawaidai mutunci mukeyi dashi saboda daga gari daya muka fito, Shikafi"
"Bisma kenan kin manta aminta yanasa ayi aure koh a dasa soyayya? Lallai fatana Allah yayi mana jagora"
"Amin".

NIGERIA SHIKAFI

Shirye shirye akeyi kwarai saboda, dawowar yar gaban goshi hatta fentin gidan sabone, an gyara ko ina donya kawata kallon yar'Gaban goshi,
Inkaga mutane acikin gidan babu Wanda yake zaune kowa sabgar gabansa yakeyi, an shirya liyafa wacce babu irinta a fadin Gusau, abinchi ne kala kala sannan ga yan tarban bakuwa yan uwa sa abokan arzuka duk an halacci gidan, daga birni da kauyuk'a
Ummi kuwa takasa zaune takasa tsaye tilon yarta zata dawo daga USA,
Shikam Abbeey yana chan danasa mukarraban, ana hiran irin cigaba da nasaran da Bisma tasamo daga Florida.

FLORIDA

Acanma bikin yayesu akeyi, lokacin sunrigada sun kammala, hada kayansu dayan tsarabe tsarabe, shikam Hamdan ziri muzin shi zai koma, daman dayawa mata ke jigilan yin tsaraba koda kasa mai Girma akaje dayawa inka leka kasuwanni da dare mata ke hidima.
Bayan an kammala ne, hankulansu duk yabi ya tashi saboda rabuwa da juna da zasuyi, Bisma takasa cin komai gashi garinsu guda amma kowa da shiyarshi, nikaina saida na tausayawa Bisma saboda irin shakuwar dasukayi tun haduwarsu a makaranta.

DASHEN ZUCIYADonde viven las historias. Descúbrelo ahora