DASHE ZUCIYA BABI NA Ashirin Da daya 21

293 4 0
                                    

💔 *DASHEN* 💔
*ZUCIYA*



_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_👄

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘

2⃣1⃣

Hamdan yace "Aunty ya za'ayi?"
Tace "duk yadda za'ayi ka dauko Rumaisa ka kawota gidannan, nasan za'a bazama nemanka babu Wanda yasan inda zakuje, sai kuzo nan dakwai wajen dazan ajiyeku sannan, duk sauran plan din saidai kayi nasaran dauko Ruma matukar tana sonka toh dole ta biyoka" hamdan yaji abun ban barakwai anya zai iya yake yambayan kansa wani tunani yashiga inda batareda bata lokaci ba, Aunty dinsa tace "Maza ka kama hanyan Shinkafi ka aiwatar da abunda nakeso".

Cikin gaggawa ya kama hanyan, cikin haddadiyar Motarsa, sai shinkafi kofar gidansu Ruma ya tsaya ya aika akirata amma batareda yafadi sunaba, cikin ikon Allah kamar taji a jikinta hamdan ne, tafito sanye da doguwar Riga wacce ta lullube kafarta da hannunta daman daganan matsalar take, kallon juna sukayi suka sakarwa juna wani murmushi mai kawata zuciya, hamdan yayi saurin cewa "Nasan sak'o ya isheku daddy na yace kowa ya watse babu biki, Rumaisa inasonki zanyi duk yadda zanyi ganin kinzama mallakina don haka tafiya zamuyi karkiji komai babu abunda zai faru matukar kina sona dole kiyi abunda nakeso" tuni idanunta sukayi rau rau "yanzu My blood meye makomar guduna daga gida kana ganin haka bazai kawomun matsala ba?"

Hamdan yace "babu abunda zai faru matukar su hajiya suka aminche na aureki tom zanyiwa kowa bayanin dalilina nayin haka, ruma kidubi girman Allah da son da nakemiki, kizo mutafi" batada wani choice saina tabi shi gudu yakeyi a mota cikin Awa daya da rabi suka isa cikin garin zamfara, basu zarce koh inaba sai Bayan Asibitin yariman bakura, cikin gidan suka shiga hankali kwance tuni Aunty din Hamdan ta tarbi Rumaisa ba tareda ta k'yamaceta ba.
Gida tuni ya rude ba'aga Rumaisa ba, har garin Gusau suka je amma iyayen Hamdan sukace aisu sunce anfasa biki saboda bazasu hada jini da musaka ba,
Yaya salim daya fusata yace "Ina danku indai muka ganshi toh sai kanwata ta fito don babu inda zamuje"
Mahaifin Hamdan yace "Kuna iya zama Ku jira shi Donni kunga tafiyata".
Fita zaiyi yaya salim yace "Babu inda zaka saika fitomun da kanwata inada daman kamaka saboda inada ID card, yaciro IDCard dinsa na shedar zama Police mai Anini, kana iya bina police station Tunda naga abun naka da rainin hankali" tuni gida ya rude haka yaya salim yayi matching din Mahaifin Hamdan har police station dake hanyan unguwar gwaza da kauran namoda.

Ciki suka shiga da isarsu kawai suka fara sarama yaya salim, cikin kankanin lokaci yayi report din dinsa aka sakayashi, mahaifin Hamdan cewa yakeyi "Da girmana da muk'amina kusani a Bayan kanta ni Wallahi bansan inda Hamdan yakeba haka yarku,"
Yaya salim yace "Banyarda a bada belinsa ba harsai yafito mun da dansa tareda kanwata".
Suko su hamdan tuni suka fara plan tuni suka samo wata yar kwalbar magani sukayi da sunan poison ne aciki, Cikin rudu Aunty takira wayar mahaifin hamdan tace "Yaya ba ga hamdan da Rumaisa suna shirin shan poison su kashe Kansu Dan Allah kuyi gaggawan zuwa" cikin rudu Alhaji yace "wat????? Dan Allah kutaimakeni ga Dana chan zai kashe kanshi zaisha poison shida yarinyar da ake nema banaso inrasa Dana Ku taimakeni infita daganan," cikin gaggawa wani corporal ya ruga yakira yaya Salim yasanar dashi komai, batareda bata wani lokaci ba suka isa gidan kafin suzo ai tuni Rumaisa da Hamdan sun kwankwade sai gasu a kasa suna fitarda wani kumfa a bakinsu ai Aunty ta kara rudewa tana cewa "Hamdan inace ba poison din gaskiya bane pls kar kayimun haka Alhakin duk a kaina zai kare, da jiniya suka isa gidan suka tadda hamdan da rumaisa kwance basuko motsi.

DASHEN ZUCIYAWhere stories live. Discover now