DASHEN ZUCIYA

429 8 2
                                    

💔 *DASHEN* 💔
       *ZUCIYA*

   
   
_Written by_
_*HUMAIRAH Bashir Melody*_👄

*Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘

6⃣

Ummi kallonta kawai take tasan za'a Rina, hannun bisma ta kama tace "kema fa naki" lokaci guda Bisma taji wani mugun dadii tayi tsalle sukayima Ummi Sallama suka kama hanyan Zuwa GRA biki.
Direba ne ya daukesu dayake an hanasu tuki, saboda rough driving da Bisma takeyi saboda sabo da kasar Florida,
Bakin wani hall sukayi packing lokaci guda suka fito kowacce sanye da Google a idanunta, yadda kukasan makafi wakane kawai ke tashi abun sai Wanda yagani, cikin tafiyar ka saita suka isa cikin hall din daman ansan da zuwansu kowacce kodata akeyi.

Guri aka sama musu a high table, inda manyan baki suke Bisma kawai ake kodawa likita likita kenan likita bokan turai, bakije Us a banza ba wallahi baba ba'ayi asaran kudin Tara ba, tashi bisma tayi ta isa wajen Mc tafara yimai barin Naira yan dubu dubu kawai take watsamai, saboda dadin washin dayayi mata.
Ba'a jimaba Aka fara Event wani Abu Bisma tagani daidai da shigowan Amarya da Ango lokaci guda zuciyarta tafara bugawa, Hamdan Munnir Hameed Weds Laila Ibrahim Wambai.............

Lokaci guda ta mike tace "Daman hamdan yaudarata yakeyi basona yakeyiba? Oh noo nayi regretting saninka Hamdan a rayuwana, amma yau saina bata maka ranar farin cikinka saina gayawa duniya cewa kai macuci ne maciyi amana kuma azzalumi Wanda baidau soyayya da muhimmanci ba, Hamdan menene don kace mun zakayi aure? What is dere?"
Dayake bamai saurin kuka bace ta zauna ta hakimce akan kujera dayake Bisma itace babbar kawa.

Itama Rumaisa abunda yake bata mamaki shine "tabbas wannan shine saurayina Wanda muka Dade munason juna har Alkawarin aure mukayi dashi shine zaiyi playing dina haka? Toh koh yadebo ruwan dafa kansa don saina canzamai halitta yadda matarsa bazata sake ganin kyawunsa ba".
Bayan kowa ya zaunane aka bukaci babbar kawar Amarya Bisma Bassam Anka tafito lokacin Hamdan yaji wani tashin hankali lokaci guda ya mike zai fita Laila tace "babu inda zaka zauna tun dazu bakasan zaka fitaba saida Bisma zatayi magana kuma Sanin kankane babbar kawatace?"

Ai ba shiri yakoma ya zauna zufa kawai yake zuba ajikinshi lokaci guda yayi shar kab da zufa Kamar yayi wanka da ruwa.
Bisma ce tafito kan stage taga dubban mutane an taru saboda murnan bikin Hamdan da Laila, tace "ya dubban mutanen nan zasuji abunda hamdan ya tafka? Ya Laila zata daukeni? Ya makomar bikin Hamdan da Laila? I don't care wannan yarage nasu".
Farawa tayi da gaisheda kawarta Laila Ibrahim da Angonta Hamdan munnir, sannan ta juyo ta gaida dubban mutane sannan tafara gabatar da kanta a matsayin aminiyar Laila tabada tarihin Laila tun daga kuruciya harya zuwa yanzu, guri tuni yadau tafi sauka tayi daga kan stage din tareda loudspeaker din....

DASHEN ZUCIYAWhere stories live. Discover now