PART TWENTY EIGHT (28)

984 41 5
                                    

                  ZURIA

        KANO NIGERIA

             ********
Bayyi ko minti talatin ba (30) mukaji ana sallama.

Fidat tatashi tabud'e kofar, Iman ce tafara shigowa da gudu tafad'a  a ciny'ata tanacewa "Aunty Ameera, missing u,
 
"Missing u too habibty",
shine amsar dana bata,

     Muna cikin maganar kawai mukaji ana knocking again, Fidat ta tashi tabud'e kofar tacire key batareda kullewa ba.
  Ilham tayi sallama tashigo palour, tazauna suna tad'i da Fidat.
       Bayyi ko minti d'aya ba, kuma naga Farees yashigo palour. Sanyeda black suit, (red sleeve and necktie😍).
Wallahi nakasa kau da idanuna a kanshi, tunda yashigo kallonsa kawai nakeyi babu kiftawa.
Narasa me ne matsayin Farees a zuciyata, domin tun ranar da nafara had'uwa da Farees rayuwata duk ta chanza, bani da wani aiki se tunanin sa kai ko barci nakeyi mafarkinsa nake, gaskiya bangane matsayin farees awajena ba, a bayansa ji nake tamkar babu wanda na tsana a duniya irinsa ba, amma dazarar naganshi se inji duk jikina tayi sanyi.

 Nayi zurfi cikin tunani. Yayinda mommy ta katseni  "Ameera"
A firgice na amsa "Na'am mommy".
     Kije d'aki kid'aukomin jakata.

Natashi cikin sanyin jiki na haura upstairs naje d'akin na d'auko jakar, nadawo zanbud'e kofar palour kenan naji kamar ana hayaniya "toh me kuma yafaru"?

Na tseya shiru a coridor ina sauraron su,  Ashe magana ta sukeyi.
Farees yanata masifa "haba, haba mommy, yazaki sani tafiya da wannan abun supermarket, kuma har tashigo cikin mota na, I can't take this, Impossible.

(Gasskiya Farees na cin mutunci na. abun yayi yawa wallahi, kuma insha Allahu zan rama duk abinda yakemin, kuma da yardan Allah shima watarana seya zubar da hawaye adalili na, kamar yedda ko yaushe nake zubar da hawaye a dalikin sa.)

Sanda nashare hawaye na, sannan nabud'e kofar nashigo palour.

Har yanxu dai suna kan yin maganarsu basu fasa ba.     

Momy ta mika hannu, ta kar6i jakar ta, cikin 6acin rai tad'au  karamin waya  ta wurgomin
"ga wannan wayar, ki rike,  kai kuma (farees) idon baka son ganin 6acin raina kutafi yanzun nan, idon kuma kanason 6acin rai na  seka seya inta magana kana mayarmin, tunda yenxu naga ka girma kafini tsayi.

A HAUSA STORY (ZURI'A)Onde histórias criam vida. Descubra agora