PART FOURTY ONE (41)

747 28 38
                                    

                  ZURIA

Momy dakanta tayi tuki har izuwa asibitin d'anta🏥.
   
Ta gangaro ciki tayi parking sannan tafito cikin hanzari tana kuka yayinda take tambayar Receptionist d'akin da Ameera take.
    
Ya'sheda mata cewa tana Emergency room3 *ilhams ward*
(Duk wards na asibitin da sunan y'ayanshi akayi👍)
       
Momy da Iman suka hanzarta zuwa Iham Ward 3*.
        
A hany'ar su tashigowar wards d'in Dr Farees ya hangosu daga nesa😦, hankalin sa yayi matukar tashi ganin irin guduwa da kukan da mahaifiyar tasa keyi, dashike tunda safe bai shigo asibitin ba, so baisan abinda ke faruwa ba. 
    
Pepopin dake hannun sa duk suka wase a kasa, tsanadiyar firgitan da yayi😱. 
    
Y'an sandan dake tare dashi duk suka ra'zana ganin yedda Ogan nasu yafara rugawa tamkar mai gasar gudu (race).
 
Hankalin su yayi matukar tashi yayinda dukkan su suka biyosa  a guje🏃🏃🏃🏃🏃.
         ❇❇❇❇❇❇❇❇

Momy da Iman suka karaso cikin wards d'in a fusace, Momy na'ta kuka yayinda taji an rungumota tabaya.   
A tsorace tawaiwayo, kwatsam taga Ashe Fidee ce.
     
Fidat nata kuka yayinda ta zayyano mata duk abubuwan da yafaru abayan ta. A lokacin Ilham takaraso wajen cikin kuka tarungumi kanwarta Iman tanacewa "Iman Aunty Ameera ce wai zata mutu"...
       
Ta'ke Iman tafashe da kuka tanacewa "Adda ilham kenan Aunty Ameera ma so take tabarmu kaman yedda momy tatafi tabarmu".
       
Ilham ta gyada kai cikeda tausayi tace: baby Iman kidena kuka in Allah ya yerda ba zaamu rasa taba😭...
              💜💜💜💜
Nan ta'ke Farees yakaraso wajen a guje tareda y'an_sandan sa biye dashi a baya.
         
Nunfashi yake sama sama a yayinda yake tambayar Momy "Lafiya?"
         
Ilham ce ta amsa mishi tambayar dacewa; Daddy Aunty Ameera ce bata da lafiya.          

Farees yaja doguwar nunfashi sannan ya girgiza kai yanacewa; Alhamdulillah ai ni azatona Abi ne ba lafiya.
          
A lokacin Momy tata6e baki tana mishi kallon mamaki "Farees yaushe kazama haka, ai wannan rashin Imani ne kana likitan ma ba'ka da Im.........
       
Bata karasa furucintaba yayinda Farees yayi murmushi yanacewa: Ana asif, sorry mama ya wuce baza'a sake ba...
         
Momy ta gyada kai "Bakomai D'ana ya wuce, yanzu dei yakamata ka karaso cikin d'akin kaduba ta ko'ta farfado.
       
Yayi murmushi karfin hali; alryt. Sannan yaja kofar yashigo d'akin🚪...........

        ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤
Farees ya karaso cikin d'akin har izuwa gadon Ameera.
     
Inda yatar da likitoci zasukai akalla su bakwai akanta sunata faman aikace aikace.
        
Ya tseya shiruuu har nawasu mintuna yana kallonta cikin sananin fuskar tausayi.    

Nan ta'ke likitoci suka cire mata oxygen dake makale a fuskarta sannan Dr Ahmad yasheda masa cewa "a yanzu nunfashin ta yakoma normal kuma muna saran zata iya farkawa nanda minti talatin" .
     
Farees yayi murmushin karfin hali sannan ya yaba da kokarin su. 
    
Dr Munir ya sany'a mata ruwa (drip) kamin dukkan su suka fice,

Dr Farees da patient Ameera kawai aka bari a d'akin. 

Farees ya matso yazauna kan godon a gefenta. Ya'kure mata ido har nawasu mintuna sannan yamike nan ta'ke domin yafara karya alkawarin dayama zuciyar sa akan babu wata alaka dazai sake had'ashi da Ameera.
              
Nan t'ake yayi ajiyar zuciya yafito waje, inda yashedawa su Momy cewa "zasu iya shigowa cike"..
Sannan yayi tafiyar sa.....
               ***
Momy, Fidat, ilham da Iman duk suka karaso ciki.  Kai tseye suka wuce har inda take. 
Momy tashafe kanta (ameera) "Allah yabaki lafiya Yata".  
Yayinda tazauna a gefen gadon tafara tunani..

A HAUSA STORY (ZURI'A)Where stories live. Discover now