PART FIFTY (50)

792 36 31
                                    

                      ZURI'A

                  🌹🌹🌹🌹🌹

Ameera ta kwana cikin damuwa da tunani. Dare guda bata samu tayi barci ba se nafiloli dakuma kuka data kwana tanayi, kwakwalwarta ta shiga rud'ani da damuwa Allah Allah take kar wannan maganar Nasir ta zamto gaskiya domin ko da gaskiya ce ba'zata ta6a rayuwa da wani mahalukiba fa ce  Farees.

               ********
Ta 6angaren Nasir kuwa dare guda yashafa a tseye, se safa da marwa yake tayi cikin d'akin yanata jujjuyi tamkar mara hankali.

Bai tsanardasu hajiya a daren ba, sanda yajira safiya karfe bakwai ya bugowa Hajiya ya tsanar mata abinda ke faruwa amma ya shedamata cewa kada susa damuwa zayyi handling na komai, kuma da yardan Allah zai dawo Nigeria tare da Fatima amasayin Matarsa.
    
Umma ta'yi mamakin jin hakan sosai, amma tace masa kada ya kuskura ya barwa Farees Fatima dalilin dukiyarsa ko wani abunasa na duniya, yayi komai tsakani da Allah domin yasake mallakar matarsa.

Da wannan shawarar hajiya ya kashe wayar sannan ya sake danna layin Azna, hannayensa na karkawa yayinda ya kira layin.

A bugu na uku ta d'aga wayan cikin muryar shegantaka tace; Mijina ka samo mana kud'ad'en ne? Ka dawo musha shagalin bikin mu......

Bata karasa furucintaba yayinda Nasir yayi saurin katseta dacewa; Azna ba don wannan na bugo miki ba, Inaso kishiga jirgi yanzun nan ki taho America, akwai masala.

Masala kuma?:Azna ta fad'a cikin sananin damuwa; Kodei asirinka ta fara tonuwa ne?

A'a ba hakaba, Fatima nagani a gidan Dr Farees wai itace matar da zai aura, kuma wallahi kwata kwata Fatima ta nuna cewa batasanni ba.

Inna lillahi wa inna ileihi rajiun, Nasir any'a lafiyanka kuwa, Fatima ta rasu tun ba yau ba mey..........

Bata karasa maganartaba Nasir ya daka mata tsawa; Azna me yasa kikemin haka ne, taya zan miki karya, Wallahi Fatima tana gidansu Dr Farees kuma wai itace matar da zai aura.

Cikin sananin mamaki Azna tace: lallaikace Farees ya d'auko ruwan dafa kansa, da dukkan alamu bai San ko kai waye ne ba shiyasa yake kokarin wasa da hankalin ka.....

Azna ke dei ki taho, nayi magana da oga kado zaku taho tare. Yanzu haka shiryawa nake zan tafi ofishin y'an sanda.

OK toh, bara na shirya, se mun taho...

Da wannan maganar ya kashe wayar.......

                 ******
Daga nan babban police headquarter'n America ya nufa, a chan yakai karan Farees ga hukuman y'an sanda.

Bayan nan ya wuce gida.. Karfe goma da minti arba'in da shida dedei ya shirya, ya je airport inda ya d'auko su Azna suka koma gida tare.

          ***********
Ta 6angaren Farees kuwa, zaune yake yana shan sha'i yayinda Sa'ad yashigo a guje yake tsanar masa cewa Y'an Sanda sun taho kuma sun ka'ma Hajiya Turai tareda dukkan y'ayanta, Allah ya baka hawan rai,  harda Ameera dasu Abi duk sun tafi tare, yenzu hakama sauran y'an sandan suna waje.....

A HAUSA STORY (ZURI'A)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant