*AMRAH'S IFTAR KITCHEN🍷*
*RAMADAN DAY 9⃣ DISHES*
1- Fruit salad
2- Bate pastry
3- Sweet beef baking
4- Tea
5- kwadon lettuce*1- FRUIT SALAD*
Ingredients
1- Any fruits of your choice
2- vanilla extractInstruction
1- ki yanka fruits dinki duka ki hade wuri daya.
2- ki zuba vanilla extract a kai.
3- ki motse sannan ki dora kankara.
*2- BATE PASTRY*
Ingredients
1- flour gwangwani 1
2- dabino 10
3- sugar 3 tablespoons
4- evaporated milk half cup
5- melted butter 2 tablespoons
6- pinch of salt.
7- baking powderInstruction
1- Ki hada flour, baking powder da salt ki motse su.
2- Ki miyar da dabino kanana sosai ki zuba a flour din.
3- ki zuba kwai, madara da butter ki yi mixing sosai.
4- Idan da bukatar karin ruwa sai ki kara kadan. Da tauri dai ake sonsa.
5- ki dama wata flour din daban amma ita da ruwa ruwa zaki dama ta. Ki ajiye a side.
6- Ki zuba sugar a container kadan da ruwa ki dafa.
7- Ki fidda shape dinsa kaman yanda zan gwada maku a hoto.
8- ki nema wani siririn abu ko ki yi kwarkwaro ki zuba wancan kwabin mai ruwa ruwa. Ki ringa zubawa kaman yanda zai zo maku a hoto.
9- ki nemi brush ki ringa dangwalar sugarn kina shafewa da shi.
10- ki dora baking tray ki gasa.
*3- SWEET BEEF BAKING*
Ingredients
1- Beef 200g
2- Soy sauce
3- maggi to taste
4- Zuma/sugar cyrup 2 tablespoons
5- vineger 1 tablespoon
6- ginger and garlic
7- pepper 2 tablespoons
8- ketchupInstruction
1- ki wanke nama ki tsane shi daga ruwa sannan ki juye a baking tray. Ki zuba maggi da kayan kamshi sannan ki saka a oven.
2- Ki zuba soy sauce a sauce pan, ki zuba pepper, maggi da gishiri, vineger, ketchup da mai kadan. Ki dora a wuta ki soya sama sama sannan ki sauke.
3- Idan naman ya kusa gasuwa sai ki sauke. Ki zuba sauce din a kai sannan ki juye a tukunya ta yi kaman minti goma sannan ki sauke.
*4- TEA*
A hada tea da madara in da hali ki zuba ovaltine, ki ci da bate pastry din kamshin ovaltine na dukan bakinki.
*5- KWADON LETTUCE*
Ingredients
1- lettuce
2- tumatur da albasa
3- green pepper
4- maggi
5- kuli kuli
6- vinegerInstruction
1- Ki yanka lettuce kanana ki wanke sosai.
2- ki yanka tumatur da albasa da green pepper ki zuba a kan letuce din.
3- Ki zuba kuli kuli a container daban ki zuba ruwa da vineger da maggi ki dama.
4- idan kuli kulin ya damu sosai sai ki juye lettuce din a kai ki motse sosai.
*A SHA RUWA LAFIYA*
Princess Amrah✍🏼

YOU ARE READING
AMRAH'S KITCHEN
Short StoryNice and amazing dishes. follow me and have an idea on many recipes