SUYAR KAJI MAI KYAU

555 30 1
                                    

*AMRAH'S KITCHEN🍷*
         *1, 2, & 3*

    *SALLAH DISHES*
🍕🍔🍟🌮🌯🍝🍖

_Pls a koya mana yanda zaka soya kaji suzamana so attractive ga koma waye. Irin wanda zakigansu sunyi fluppy haka me kyau kaman bada mangyada aka soyasu ba_

To masha Allah!

Ita dai suyar kaza kala daya ce tal! Saidai a samu banbanci ta wurin kayan hadi ko kuma kalar suyar.

Indai kina son suyar kajinki ta yi kyau sosai yanda ya kamata, a ido tayi kyau kuma a baki tayi dandano mai dadi (Nasan wasu zasu ce dama akwai suyar kaji marar dadi? Mu dai bamu taba ji ba sai a wurin Amrah...lol.  Tabbas kuwa akwai marar dadi, wadda zaki ga gata a ido a kawace, amma a baki babu dandano mai dadi. Wata kila ma kina sakawa a baki ki fitar saboda karni, bata ji kayan kamshi ba.)

Kina da bukatar ki nemi:

1- kaza
2- tarugu
3- citta
4- tafarnuwa
5- maggi
6- salt
7- albasa
8- vegetable oil.

_Yanda zaki tafasa ta komai ya kamata tun wurin zafka kafin suya:_

Zaki wanke kazar kamar sau uku ko hudu, ki tabbatar ta fita sosai.

Ki zuba a tukunya ki zuba ruwa madaidaici, wanda kika san zai dafa miki kazar kuma ruwan ya tsane tsaf a jikinta.

Ki zuba farin maggi da gishiri ki tabbatar ya shiga ta ko ina, kar kawai ki zuba a wuri daya yanda zai yi wuyar hadewa.

Ki jajjaga tarugu makimanci ki zuba a ciki.

Ki yanka albasa mai dan yawa itama ki zuba a ciki, ki zuba citta da tafarnuwa ta ko ina.

Ki dora a wuta, kar ki sakar mata wuta sosai, kadan kadan zata ringa dahuwa yanda komai zai ringa shigarta a hankali har ta dahu.

_Yadda zaki soya kazar ta yi jar suya mai kyau._

Bayan kin tabbatar ruwan kazar ya tsane a jikinta, idan ma an samu akasin ruwan ya dan yi yawa, zaki iya juye ta a kwando ki bata kaman minti talatin yanda ruwan zai tsane tsaf daga jikinta. Amma so samu dai ruwan ya tsane tun wurin dahuwarta.

Ki zuba mai a babban pan, wanda kika san kazar zata wala ba wai karami ba.

Idan kin tabbatar yayi zafi sai ki rage karfin wutar, ki zuba kazar ki motsa gudun kar ta dunkule.

Ki zauna a wurinta kar kiyi nisa, zaki ga tana tsanewa a hankali sannan ta fara soyuwa, idan kin tabbatar ta soyu, ba wai ta soye sosai ba, ja ake da bukatar tayi sai ki kwashe.

Haka zaki yi har ki gama.

Ki nemi foil paper ko kuma cling film ki nade kazar a ciki dan kar ta bushe.

Fakat. Sai enjoying🤗

Princess Amrah✍🏼

AMRAH'S KITCHENTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon