cake's measurements

733 12 1
                                    

*AMRAH'S KITCHEN🍷*
            *1, 2 & 3*

    *SALLAH DISHES*
🍕🍔🍟🌮🌯🍝🍖

_Amrah tawa tambayar ita ce; dan Allah idan ina son yin cake na mudu daya, dame dame ya Kamata na saka? Kuma ya kwatankwacin awonsu zai kama? Nagode._

To madallah, shi dai cake din nan yana daya daga cikin pastries wanda suke da bukatar kayan hadi sosai. Dan haka ya zama dole in dai kina son cake dinki ya bi jerin cakes fitattu, kuma masu dadi, to dole ki daure ki saki hannu, ki zuba wadatattun ingredients. Shine zaisa ki ga naki ya sha banban da na wasu matan.

Abubuwan da zaki bukata sun hada da:

1- Flour
2- corn flour
3- egg
4- butter
5- sugar
6- flavor
7- baking powder.

Idan zan yi flour gwangwani biyu, abin da nake nema sune;

1- kwai, guda takwas
2- margarin leda daya da rabi
3- sugar kwatan gwangwani
4- baking powder 1 t spn
5- flavor 1 t spn.
6- corn flour 3 tablespoons

Wannan kenan.

To kinga idan kin tashi sai ki kwatanta. Mudu yana cin gwangwani nawa ne? Ki auna ki ga ni, duk yanda ya baki to haka ingredients dinki zasu kasance.

Fatan kin samu gamsasshiyar amsa.👏🏻

Princess Amrah✍🏼

AMRAH'S KITCHENWhere stories live. Discover now