DAMBUN SHINKAFA

1K 50 5
                                    

*KITCHEN PRIDE🍽*

*DAMBUN SHINKAFA*

By Princess Amrah✍🏻💞

Ingredients

Barzajjiyar shinkafa
Zogale
Tarugu
Albasa
Veg. Oil
Maggi and salt to taste
Soyayyar gyada (gyadar amaro)

Method

Ki wanke barzajjiyar shinkafarki sannan ki saka a gwagwar karfe ki bari a ciki.

Ki nemi tukunya wacce kika san gwagwar za ta iya hawa daram, sai ki zuba ruwa a ciki makimanci sannan ki dora gwagwar a kai ki dora a wuta.

Idan ya turaru sai ki sauke.  Ki jajjaga tarugu hade da gyadar amaro da maggi ki juye a kan turaren. Ki zuba zogale dafaffiya, idan kuma danya gare ki to tun a wurin turaren shinkafar na farko za ki saka.

Ki zuba vegetable oil ba mai yawa ba. Ki motsa sosai sannan ki yi dandano. Idan kin tabbatar komai ya yi sannan ki sake juyewa a cikin gwagwar ki miyar a wuta.

Idan ya dahu za ki ga albasar ta yi taushi alamun ta dahu. To sai ki sauke daga nan.

Serve and enjoy!

Serve and enjoy!

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

©Princess Amrah

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 07, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AMRAH'S KITCHENWhere stories live. Discover now