Ramadan day 19 dishes

524 11 0
                                    

*AMRAH'S IFTAR KITCHEN🍷*

*RAMADAN DAY 1⃣9⃣ DISHES*

1- Bread and potato rolls
2- Coconut drink
3- Alalen plantain
4- farfesun kayan ciki

*1- BREAD AND POTATO ROLLS*

Ingredients

1- Sliced bread
2- potato
3- vegetable oil
4- maggi and salt
5- kayan kamshi
6- ganyen parsley
7- pepper

Instruction

1- Ki dafa dankalin turawa ki murzashi ya daddame.

2- ki nemi vegetable oil ba mai yawa sosai ba, ki zuba pepper a cikinsa ki motse.

3- ki tsoma sliced bread a ciki ya jike shakaf da mai yanda zaiyi saukin tankwasuwa.

4- ki zuba kayan kamshi a cikin mai ki soya da ganyen parsley sannan ki zuba dankalin da kika guggurza a ciki ki motsa har sai komai ya shiga cikinsa har da maggi sannan ki sauke.

5- ki juye a cikin bread din da ya jike da mai sannan ki nade shi kaman yanda nayi a hoto, zaki ga ya zauna daram kamar kin saka masa glue.

6- ki soya a cikin mai.

*2- COCONUT DRINK*

Ingredients

1- kwakwa
2- madara
3- sugar
4- ice cubes
5- vanilla extract

Instruction

1- ki fereye bayan kwakwa sannan ki guggurzata.

2- ki saka a cikin blender sannan ki zuba madara, sugar da kuma ice cubes kin markada a tare.

3- ki cire sannan ki tace.

4- a yi serving a glass cup.

*3- ALALEN PLANTAIN*

Ingredients

1- plantain
2- pepper
3- vegetable oil
4- onion
5- maggi and salt
6- tarugu

Instruction

1- ki nemi plantain ki yayyanka kanana.

2- ki zuba a blender ki saka pepper da albasa sannan ki zuba tarugu idan kina so.

3- ki markada amma kar ki zuba ruwa da yawa. Idan yayi sosai sai ki fitar ki juye a container.

4- ki zuba maggi da kayan kamshi.

5- ki nemi irin kananan gwangwanin yin cake ki shafa mai kadan kadan sannan ki zuba kullun a ciki.

6- ki nemi foil paper ko cling film ki nade sosai dan kar ya zube.

7- kiyi steaming dinta.

8- idan kin tabbatar tayi sai ki sauke, ki ringa fiffiddawa a hankali daga gwangwanin dan kar shape din ya baci.

*4- PEPPER SOUP NA KAYAN CIKI*

Ingredients

1- kayan ciki
2- maggi and salt
3- spices
4- pepper
5- onion
6- ganyen parsley

Inatruction

1- ki wanke kayan ciki sosai sannanna ki saka a tukunya.

2- ki zuba kayan kamshi da albasa da su maggi a ciki.

3- ki barshi ya dahu sosai.

4- idan ya kusa dahuwa sai ki saka pepper.

5- ki sauke bayan yayi laushi, parsley din ma ki tabbatar ya dahu sosai.

*A SHA RUWA LAFIYA*

Princess Amrah✍🏼

AMRAH'S KITCHENWhere stories live. Discover now