*AMRAH'S KITCHEN🍷*
_By Princess Amrah_
*FATEN WAKE MAI DANKALI*
Ingredients
1- Wake gwangwani daya
2- irish guda bakwai
3- tarugu guda biyar
4- tumatur guda biyu
5- albasa guda biyu
6- curry 1 tea spoon
7- maggi and salt to taste
8- hanta 200g
9- citta da tafarnuwa
10- veg. Oil 1/2 gwangwani.
11- alayyau dauri gudaInstruction
1- ki nemi wake ki gyara shi sosai sannan ki wanke.
2- ki zuba a tukunya da ruwa ki tafasa shi.
3- ki sauke sannan ki zuba hanta da kayan kamshi da kuma maggi, ki dora a wuta.
4- idan ta dahu, sai ki tsame daga ruwan zafkar, ki zuba mai ki soya ta sama sama.
5- ki juye cefanen da kika jajjaga a ciki, ki ta motsawa har sai sun soyu.
6- ki juye ruwan da kika tafasa hantar da shi, ki zuba maggi da curry ki rufe.
7- ki fereye dankalin turawa ki rarraba ko wane daya gida biyu saboda yayi saukin dahuwa. Ki zuba a cikin ruwan da kuma zafkakken waken a ciki.
8- ki tasting idan komai ya ji sai ki zuba alayyahu ki barshi ya dahu.
9- idan ya dahu sai ki sauke.
10- enjoy.
Princess Amrah✍🏼

YOU ARE READING
AMRAH'S KITCHEN
Short StoryNice and amazing dishes. follow me and have an idea on many recipes