® *HASKE WRITERS ASSO💡*
*SA'IDAH*
Nah
khadeeja Ahmad (Kdeey)
*wattpad* @Deejaht Ahmad*2*
***
Sama da kusan minti goma kenan suna kallona, kallo irin na takaici da kuma mamaki, na san tsabar takaicin yanda suka ga na maida kaina ne ya hanasu maganaMuhammad, ramadan da hamisu ne 'kannena da muke mutu'kar 'kaunar juna, hasalima dukan mu gida d'aya muka taso,
Ramadan ne ya fara mi'kewa tsaye ya kalli muhammad da hamisu yace "in kun gama kallon nata ku sameni a mota" nayi sauri kallon sa
Lallai da alamun duniya ta dad'e da fara juya min baya tunda har ramadan da kansa ya cewa ragowar 'yan uwana haka, be damu da damuwa ta ba kenan?
Duk abinda zanyi ko nake ciki ko zai same ni naje yayi ta samuna kenan? Ba matsalarsa bace? Lallai *Abdulhadi* ya cuce ni
Duk shi ya jawo wannan matsalar a rayuwata, cikin shshshe'ka na kalli Ramadan nace "Ramadan haka zaka yi min?" Ko kallo na beyi ba
Sai wata amsa da naji daga muhammand wacce tayi mutu'kar girgiza ni yace "nima biyoka zanyi ramadan dan bazan iya zaman 'bata lokacina a nan ba, dan ban gaji zaman 'bacin rai ba bare nayi, kuma ba mutuwa aka yi mana ba bare nace zaman makoki muke yi to akan me? Gara in tafi koda cikin abokai nane kona rufawa kaina asiri"
Duk suka fice, har hamisu ma gani nayi ya kad'e rigar sa ya wuce ya barni anan, wani kukan na kuma fasawa tun 'karfi amma ko alamun dawowa basuyi ba.
***
Misalin 10:30 na safe agogon bangon dake falo ya nuna, dai-dai nan naga nafisa ta d'aga curtain d'in d'akin da take ta fito ko inda nake bata kalla ba ballantana nasa ran zata gaisheni,Lallai duniya rawar 'yan mata ce, na gaba ya koma baya wai yau nice yaran da naci kashinsu da fitsarinsu na rena a hannuna suke min haka.
"Nafisa" na kira sunanta, ta juyo ba tare da tace min komai ba se kallona da take yi, na cigaba
"Tarbiyyar da nayi muku kenan nafisa na 'kin girmama babba ko daraja d'an adam?"
Ta girgiza kai ba tare da tace komai ba, "na cancanci haka wurin ku kenan?" Na kuma tambayar ta
Nan ma gigiza kai tayi, nace "to akan me kuke son rusa mana rayuwa ku canja hali bayan ba haka muka taso ba"
Kuka tasa tana fad'in "anty kece kika canja gaba d'aya, ke kika koya mana rayuwa me dad'i amma yanzu akan abinda be kai ya kawo ba
Kika sa 'kafa kika shure tsabtatacciyar rayuwar da muka shimfid'a akan me anty? Akan me? Akan me?" Haka tayi ta maimaita wannan kalmar kusan sau goma kafin naga ta ta sulale ta fad'i 'kasa yaraf...
Daidai lokacin Abdulhadi ya shigo, yayi kanta cikin sauri yayin da na d'ora hannuna a ka na fasa ihun kukan da yasa duka gidan fitowa dan ganewa idansu abinda ke faruwa, aikuwa ba wanda hankalinsa be tashi ba ganinta kwance a 'kasa kamar gawa.
♡
Gaba d'ayan mu gidan ne zaune a reception na asibitin munyi jugum-jugum Abdulhadi ne kawai keta safa da marwa sai ni da Kamal da hawaye ke zubar mana sha'be-sha'be daga idanunmuKowa cikin mu da abinda ke sa'kawa a zuciyarsa ni tashin hankalina goma da ashirin dan kuwa nasan ko mene ya samu nafisa nice sila in nayi la'akari da bayanan da take zanzarowa kafin ta yanke jiki ta fad'i
Bansan maganar da nakeyi ta fito fili ba sai da naga su adda ussaina da ragowar 'kannena a kaina suna tofa min addu'a sa'annan na tambaye su "lafiya?"
Tambayar da nayi ne yasa adda ussaina rafsa kuka tana fad'in "innalillahi wa inna ilaihir rajiun mun shiga uku nafisa kwance rai a hannun Allah ga sa'ida kuma ta zare wayyo ni usaina"
Shiru nayi tare da zurfafa tunani dan gano maganar adda usaina, ina d'agowa mukayi ido biyu da Ramadan ya rafkan harara na maida idona kan Abdulhadi yayi shiru yana tsaye hannunsa d'aya cikin aljihun wandonsa
Ya kafa min ido yana kallona amma na kasa fassara yanayin da yake ciki, sunkuyar da kaina nayi sa'annan na 'kara fashewa sa wani kukan wanda yasa dole suka kira likita yayimin allurar bacci tun ina jin muryoyinsu suna magana har naji shiru.
Dishi dishi nake gani kan a hankali idona ya washe, ganina a kan gadon asibiti ya bani daman tafiya tunani dan gano sanadiyyar zuwana asibitin.
Kamar a majigi haka na rin'ka ganin abubuwan da suka faru dani suna dawo min a rayuwa har zuwan kan maganar da mukayi da Abdulhadi wanda itace silar
Jawo duk wannan tashin hankalin da gidanmu ya shiga da wanda ni kaina nake ciki take na fara addu'ar data zame min jiki ko yaushe wato
"Allahuma inni a'uzubiki min jahadil bala'i wa darkish sha'ka'i wa su'il 'kad'ai, wa shamatatul a'ada'i" na kuma 'kara da "Allahumma inni a'uzu bika minal ajzi wal kasali wa'auzu bika min galabatiddaini wa qahari rijal.." ina kaiwa nan na lumshe idona na fara tunano abubuwan da suka shud'e shekarun baya.
TUNA BAYA🔭
...♧tashin hankali goma da ishirin -tashin hankali me tsanani
♧sa'annan-sannan
#vote
&
#comment©Kdeey😊

YOU ARE READING
SA'IDAH
RomanceThe story of a young adult...ku biyoni ciki dan jin abinda ke kunshe da rayuwar SA'IDA, anty SA'IDA, BIG SIS inji ABDULHADI *SOYAYYA *SADAUKARWA *TAUSAYI *KADDARA *JURIYA *ILIMANTARWA *NISHADANTARWA Wannan labari nawa ya bambamta da sauran... Abinda...