*HASKE WRITERS ASSO*💡
(home of experts and perfect writers)*SA'IDAH*
Nah Khadeeja Ahmad
Wattpad @Deejaht Ahmad*11*
Ji nayi duniyar ta tsaya min cak yayinda na fara ganin dishi dishi baki na rawa nece "ciw..on zuciya mami??" Tuni hawaye ya fara 'bal'balomin janyo ni tayi ta rungume "kiyi shiru sa'idah Kinga shiyasa tuntuni na 'ki fad'a muku"Cikin sheshshe'kar kuka nace "shin mami laifi ne idan kin fad'a mana, mami addu'a..mami ko dan muyi miki addu'a"
"Yi ha'kuri sa'idah 'kauna da son da nake muku yasa banson ganin ku cikin damuwa" wani sabon kukan na saki can ta nisa ta d'ago kaina tare da sharen hawayen "ya isa haka sa'idah inada abubuwan da nake son sanar da ke"
Gyad'a kai nayi tare da silalewa na kwantar da kaina kan cinyarta tasa hannu tana shafar kaina tacigaba da cewa "sa'idah Allah be kad'ai yasan irin so da 'kaunar da nake miki, bayan yayana Abdulhadi kece abu mafi soyuwa a raina, Ina 'kaunar ki sa'idah kullum na ganki farinciki na 'karuwa yake Allah ya raya min ke naga jikokina daga gareki"
Na rufe fuska da tafukan hannuna nace "Amin mami"
Tayi murmushi "sa'idah na uwa ta takaina"Har kusan 'karfe uku na dare muna hira da mami tana fad'a min sirrikanta wayanda a da ban sani ba har seda nace "mami meyasa kike fad'a min"
Tace "sa'idah kece mace kuma kece babba ki ri'ke 'yanuwanki kinji sa'idah ki kuma kula da yayanki Abdulhadi, baba sule da karima ku ri'ke su da kyau masu 'kaunar ku me"
"insha'Allah mami"
"Mami Halima aminiyar kwarai ce Kuma uwar arzi'ki"
"To mami mu kwanta dare na ja"
Ta murmusa "to sa'idah"
Kashe fitila nayi nabi bayanta na lafe zuciyata na rawa bansan dalili ba na tsinci kaina cikin fargaba.
***
Daga China sa'udia muka wuce satin mu guda muka dawo kano aka fara shirye shiryen bikinmu dan harda Muhammad da taufiqa (aunty usaina) za'a had'a da Kuma Ramadan da ummuhani duk za'a d'aura aure dana d'aya.Hidima aka fara sosai ko ina kaga mami cikin walwala take da farinciki, ko wace shawara za'ayi kaji tace a nemi sa'idah haka nima duk inda tasa 'kafa nan nake zansa tawa ana gobe d'aurin aure Abdulhadi ya dawo
Kusan raba dare nayi a wurinsa muna hirar yaushe gamo zuwa can bayan asuba mami ta kirashi nan yabarni bacci ya d'aukeni, wuraren balwai na farka toilet na shiga na wanke bakina nayi wanka na fito de-de lokacin ya fito daga d'akin mami.
"Morning" nace a hankali, yayi winking idonsa yayi ya wuce hanyar d'akinsa seda na tabbatar yaci abinci sannan na nufi d'akin mami dan ganin ya ta kwana bacci na tarar tanayi naja mata bargo na fito a hankali dan kar na tasheta.
Ranar ni da mami anko mukayi dan harta da sar'ka iri d'aya muka sa, wuraren 9:30am su Abdulhadi suka shigo yi wa mami sallamar tafiya d'aurin aure sanye yake da d'anyar shaddar filtex samanta wata babbar riga ce worth dubu d'ari biyu kalar sky blue hannunsa sa'kale yake da agogo me bala'in tsada haka zalika hula da takalminsa tass ya fito dashi tamkar shine angon
Abinda ban ta'ba ji ba game da Abdulhadi yau naji shi wani irin kishin matar da ze aura saurin korar shed'an nayi na bangarar da tunanin, mami ta shafa kansa
"Allah ya kiyaye min ku ya tsare Allah ya albarkaci rayuwa" da Amin mutan gurin suka amsa, har bakin 'kofa na rakashi Ina faman turo baki "ya akayi anty sa'idah na"
"Ni bansani ba jiki nane yau banjin dad'insa sosai"
Cheeks d'ina ya ja "khairan insha'Allah" bari naje na dawo amaryar mu Abba na jirana, kai na gyad'a na d'aga mishi hannu10:30am
'Dakin mami na shiga inda na tarar da mami Halima da mami wacce kallo d'aya zakayi mata kasan tana cikin tashin hankali nace "mami lafiya?"
"Sa'idah tun d'azu nake Kiran wayoyin mazan gidannan duka a kashe har ta baba Sule"
Dafa ta nayi "mami kwantar da hankalin ki insha'Allah babu komai"
"Um um sa'idah jikina na bani wani abu na shirin faruwa"
"insha'Allah ba abinda ze faru mami dan banjima da magana da nura ba ya kuma tabbatar min su Abba sun Isa wurin"
"Kin tabbatar"
Na gyad'a kai, ta sauke ajiyar zuciya.12:30 dai-dai aka bud'ewa Abba da su Abdulhadi gate dake muna farfajiyar gida wanda yayi dai-dai da lokacin da wayar mami tayi 'kara kallon Juna mukayi ta sakar min murmushi tare da kara wayar a kunne
Banga lokacin da mami ta sulale ba se 'karar fad'uwar waya Naji saurin tsugunnawa nayi ina jijjigata a rud'e, ihu da kururuwar da nake ya janyo hankalin jama'ar gidan yayinda Abba da Abdulhadi suka iso a guje suna sakin salati
Salatin da suke shi ya rud'ar dani zuwa can naji wata murya da bazan iya tantance ta ba na fad'in "bata numfashi mami babu" tuni na yanke jiki na fad'in.
***
A hankali na shiga bud'e ido na inda nabi d'akin da nake da kallo gefe na Abidin ke zaune d'aya gefen Kuma Abdulhadi ne 'ko'karin tashin da nayi ya sa suka gane na farkaSaurin maidani yayi ya zaunar na ri'ke hannunsa cikin murmushin 'karfin hali nace "Abdulhadi kaga shirmen mafarkin da nayi"
Yayi saurin kallona yace "sa'idah wani irin mafarki?"
Nace "wai mafarki nayi mami ta rasu", shiru yayi yace Abidin ta mi'ko masa abinci ya shiga bani da'kyar na iya cin loma hud'u nace ya bani ruwa nasha,Likita ya shigo ya dubani yace ba matsala ma iya tafiya gida, Allah Allah nake mu 'karasa na bawa mami labarin mafarkina Sede muna shiga layin gabana ya tsananta bugu da muka iso gidan kuwa cike ne ga 'kofar gidan da jama'ar da ba iyaka wanda nasan duk 'yan biki be
Cikin gidanma ma'kil yake da jama'a mami halima na fara hangowa na nufeta da sauri dan ji nake duk na muzanta saboda kallon da jama'a ke bina dashi
Idonta na Kalla naga jajir cikin rawar murya nace "mami halima lafiya Ina mami?" sunkuyar da kai tayi nan na ji an fad'o jikina da sauri na d'agota "autan mami, auta lafiya?" Ta kasa bani amsa se kuka nan kowa ya d'auka
Kaf falon aka rasa me amsani can sega Ramadan ya shigo falon cikin alamun tashin hankali yace "Sai ha'kuri sa'idah mun Rasa mami yau kwanaki hud'u kenan"
Ban 'karasa jin maganar tasa ba jikina ya saki gaba d'aya na tafi zan fad'i akayi saurin ri'koni..
©️Kdeey😊

YOU ARE READING
SA'IDAH
RomanceThe story of a young adult...ku biyoni ciki dan jin abinda ke kunshe da rayuwar SA'IDA, anty SA'IDA, BIG SIS inji ABDULHADI *SOYAYYA *SADAUKARWA *TAUSAYI *KADDARA *JURIYA *ILIMANTARWA *NISHADANTARWA Wannan labari nawa ya bambamta da sauran... Abinda...