ABDULHADI

662 53 4
                                    

® *HASKE WRITERS ASSO💡*

            *SA'IDA*

Nah
   Khadeeja Ahmad (Kdeey)
*wattpad* @Deejaht Ahmad

*4*
Abdulhadi ne 'kawata, komai nawa shine dan bazan manta lokacin dana cika shekara 16 a duniya na fara jinin al'ada,

Abdulhadi na fad'awa cewa jini na fita daga jikina inajin mutuwa zanyi, wuni mukayi a d'aki muna kuka har mami ta dawo daga office

Da ta tambayemu dalilin kukan Abdulhadi yace
"Mami big sis ta kusa mutuwa jini take zubar wa, ganowa da tayi period ne yasa ta kirani d'aki bayan ta lallashi Abdulhadi ta kuma tabbatar masa da lafiya ce ke causing haka.

Ni kuma tayi min fad'a kan cewa to yanzu na girma  tare da yimin bayanai ta yacce zan kiyaye da kuma gyare kaina.

Tun daga wannan rana mami ta dage da 'kara mana karatuttukan mu wanda tuni ta ajiye ganin yanayin lafiyar.

(Kar kuyi mamakin d'abiun 'ya'yan mami suna rayuwane wacce bature kema la'kani da isolated life, makarantar boko ce kurum suke zuwa daga ita komai cikin gida ake musu , haka zalika wasu zasu ce shi Abdulhadi ai yakai girman da zesan abubuwa taya ze kasa sanin jinin al'ada dan Allah ku bini a sannu duk zan warware muku zare da abawa)

A makaranta muna amfani da sunan da mami ke amfani dashi wato maimuna muhammad jauro, haka kowa son mu yake na rasa dalili duk inda 'yan gidan mu suke zakaga mun fita daban ayi ta sha'awarmu, ra'ayinmu d'aya ne sai bambancin wasu abubuwa da halaye .

Abdulhadi nada shekara 23 ya gama jami'ar maiduguri wato unimaid dan haka mami ke ahirye shiryen turashi wata 'kasar karatun masters amma shi baya so ni kuma a lokacin na zana waec.

Kamar kullum yauma dana dawo daga exam Abdulhadi ne  tsaye a kitchen daga shi dai three quarter bansan meyasa ba dana kalleshi sai na tsinci kaina da fad'uwar gaba

Had'avido mukayi yayi saurin d'auke kansa nayi gyaran murya ina hango yacce chicks d'insa sukayi tudu alamar yana murmushi

Nace "dole ka'ki waiwayo wa mana  tunda kayi laifi, nace ka rin'ka jirana ina dawowa ina mana girki ka'ki"

Ba tare da ya waiwayo d'in ba yace"kiyi ha'kuri big sis naga ayyuka suna miki iawa sosai daalama ma rayuwarki kif kina neman sadaukar da ita wurin kulawa da mu ba ruwanki da damuwarki, ke damuwar ki itace kawai taki"

Murmushi nayi "'kanina kenan"

"Yayan ki dai"

"Oh yau kuma?..to idan ka manta ne let me remind u ni sa'ida yayarka ce dan mami kullum zancenta baya wuce ki kular min dasu Abdulhadi kaga kuwa ai girman yana hannuna"

Ya tuntsure da dariya tare da fad'in "san girma irin na sa'id.."

Hararar wasa na watsa masa ya d'aga hannuwa sama "au na manta big sis, ko dayake inaga zan koma kiran ki da mama sa'ida"

Nace "aa sai dai anty sa'ida"

Abdulhadi ya d'auka kitchen napkin ya kama tukunya yana juye fried sphaghetti cikin flask bayan ya gama ya wanke hannu a sink ya juyo da murmushi saman fuskarshi

yace "good idea, anty sa'ida will be perfect"

Murmushi nayi muka nufi dining room.

Mafarin kirana abty sa'ida kenan.

Bayan wasu kwanaki aka maida mami zuwa garin Kano da aiki nan muka tarkata ya namu ya namu muka nufi garin kano.

A dai garin na kano ne mafari ko ince asalin kome ya faru dani a rayuwa, kirarin da mukaji ana yiwa kano

SA'IDAHWhere stories live. Discover now