MATA

750 50 16
                                    

*HASKE WRITERS ASSO💡*
(Home of expert and perfect writers)

            *SA'IDAH*

Nah
   Khadeeja Ahmad (Kdeey)
*wattpad* @Deejaht Ahmad

Am so sorry for making you wait so long..pls ga wannan kuyi manage i promise u next chapter to be in #next level✌🏻

*8*

   *SAFE*
Da wuri na tashi dan zuwa gyaran jiki dan matar tace dani tana da inda zata da yamma, sosai ta kw gyarani dan kwararriya ce ta wannan fannin 'yar meduguri ce ko ban fad'a ba kunsan ya gyara yake a gunsu

Tana min gyaran muna ta'ba hira, cikin hirar nake tambayarta sa cewa"kin iya mustan?", "meye kuma mustan?" Nace "wani gyaran jiki ne nagani cikin wani littafin Kdeey"

Tace "topah ya akeyi 'yar uwa" murmushi nayi na d'auko wayata ba shiga karanto mata aikuwa take tayi jotting cikin wata takarda da cewar insha'Allahu idan ta fita zata samo kayan had'in zuwa dare za tazo har gida tayi min.

Lokacin dana koma gida a kan d'akina na tarr da abidin 'karamin teburin gabanta plate ne ba wata kaza da kofin magani a gefe tuni na had'e fuska na fad'a band'aki

Ina jiyo dariyar ta 'kasa-'kasa, da na fito na shafe jikina da mayuka masu kamshi da sa laushin fata wanda mami halima ta kawo min na zira doguwar rigar shan iska irin ta sudanese na d'aura mayafin a kaina ta wutsiyar ido na

Kalli Abidin dake watso min kallon kiyi ki gama ki zo ki same ni, ganin batace dani uffan ba na hau gyara pillow da niyyar na kishingid'a najiyo tana cewa

"Malama amma kinsan ni ba bodyguard bace ko? "

Kaikaito da kai nayi nace "you are acting like one dearest" wata ashariya ta 'kundumo har bansan lokacin dana tuntsire da dariya ba

Nace "subhanallahi maida wu'kar, wasa nake bnda abinki aminiyar kwarai kike a gurina idan ma na kira ki da haka ai banyi laifi bà kema kina da lasisin kirana da hakan dan kuwa we r all one

Me sonka shi ya damu da yazo inda kake ya kuma kare ka daga dukkan mugayen abubuwa, amma fa..."

"Amma me?" Tace

Da ido na nuna mata kwanon gabanta, dariya da take guntsewa ta saki ni kuma na kya'be baki da fuska

Tace "haba mana amaryar malam karki bani kunya mana wannan da kike gani mahaifan mu gata suke miki.."

"Nifa ba wannan ba am..basu da side effect?"

Hararar wasa ta min "haba mana karki maida kanki wata dull mana wayannan fa da kike gani 'ya'yan itatu ne da 'yar sokoto ke kawowa mami halima, ke dai kisha ki bamu labari"

Ba dan ina so ba Abidin ta rin'ka hillata ta har na cinye kazar tsaf na kuma shanye tsumin raken duk inayi ne fuska ta  kyakkya'be

Dariya Abidin tayi tace "mutuniyata kina shiryawa malam bomb" murmusawa kawai nayi tare da kai mata duka nace "ko kuma kina shirin a kakkaryani ba"

Da daddare kitchen na shiga na shiryawa Abdulhadi salad d'in kaza da lemon za'kin zamani bayan na gama na shiga na watsa ruwa,

Yau ma kusan raba dare mukayi da Abdulhadi muna hira duk da cewar hirar tamu ta yau a takure nayi ta saboda yawan kallona da Abdulhadi keyi

Shiru nayi muka zuba wa juna ido a marairaice nace
Abdulhadi har yanzu fushi kake dani ko?"

Ajiyar zuciya ya sauke kan a hankali yace "anty sa'ida kin kusa tafiya ki barmu ko?"

'Kasa nayi da idona jin yacce suka cicciko da hawaye tunani ya mamaye zuciyata dagaske yanzu saura kwana kad'an nabar mami, 'yan uwana gidan mu in general anya zan iya kuwa? Anya?"


'Daurin aure na ya tara mutane da dama daga gari-gari haka abokan aikin mami  na minna suma sun samu halarta haka abokanan hurd'ar Abba suma sun sami halarta, kai Alhamdulillahi se fatan zaman lafiya.

Ranar da aka d'aura aure da daddare Abba ya shirya min gagarumar dinner lokacin da na shiga harabar wurin se da na zubda hawaye wai yau nice ake aurar wa, ranar anci an sha an kuma gintse har da masu guziri duk da wannan hayaniyar ban gaza gano rashin halartar mutumin da idanuna ke craving ba ako yaushe wato jinina!

Abdulhadi? Yana ina? Waige waige na shiga yi sam babu ko inuwarsa nan da nan mood d'ina ya canza har aka tashi kwai ya'ke nake, tun a mota na sha kunu har se da malam ya kula

"Wani abu na damunki ne mata?"

Sam banji abinda yake fad'a ba se jin saukar sassanyan hannunshi naji cikin nawa, d'an kallonsa nayi 'kasa 'kasa kan nace wani abu naji mota ta tsaya waje na kalla ganin 'kofar gidan mu yasa na mishi d'an murmushi kan na d'ora hannuna bisa handle na bud'e kan na fice ina jiyo muryar malama na fad'in se da safe mata ki shirya sha biyu zan zo d'aukar ki

Saurin waiwayo wa nayi inda nabi 'kurar motar da ido, idan akwai abinda ke fad'ar min da gaba be wuce naji an min zancen barin gida ba bugun zuciyata ya dad'a speed lokacin da na sauke idona kan 'kofar d'akin Abdulhadi dake wangale da sauri na nufi d'akin

Can na hango shi bisa reading table d'insa yana binciken takardu, a hankali na shiga taka wa de de bayanasa na tsaya tare dayin gyaran murya imda ya waiwayo a hankali

Baki na saki ina bin fuskr hamisu da kallo yatsa na nuna masa na kuma nuna 'kofar shigowa rewinding d'in time d'in da na shigo nayi, kansa a du'ke hasken fatar hamisu na tuno wacce tash bambam data Abdulhadi dan kuwa bashi da haske sosai

Ajiyar zuciya na sauke tare da rangwad'ar da kai gefe, nace "Abdulhadi fa?"

Kallo na yayi with full concentration yace "ah ah be fad'a miki ba?"

"Ya fad'a min me?"

"Ah to ai d'azu ya wuce cuba dan damun had'in gwiwar wannan shahararren kamfanin had'a motocin, kuma a 'kalla ze d'au tsayin wasu watanni kan ya dawo dan daga can ze wuce makaranta"

Idanuna suka fara rurrufewa, na shiga fizgo numfashi da'kyar ga wani irin nauyi da naji 'kirjina ya min irin kalar sallamar da zamuyi da kai kenan Abdulhadi?

©Kdeey😊

SA'IDAHWhere stories live. Discover now