® *HASKE WRITERS ASSO💡*
*SA'IDAH*
Nah
Khadeeja Ahmad (Kdeey)
*wattpad* @Deejaht Ahmad*6*
Misalin 'karfe biyar na yamma agogon motar abdulhadi ya nuna wanda yayi dai-dai da tsayawar mu 'kofar wani madaidaicin gida me yalwar shuke shuke,Juyowa yayi yana 'kare min kallo har se da naji kallon ya isheni sannan ya tambayeni
"Anty sa'ida kinsan inda muka zo?""A a abdulhadi" with a questionable look a fuska na.
Yace "Amma kinsan mami ta takura min kan batun aure"
Nace "of course" ina murmushi
Yace "to dalili kenan da yasa nazo ki tayani za'be, nan da kika gani gidansu samina ne yarinyar da nake ganin idan na aura bazata kawo mana matsala a family ba"
Cikin murna na matsa na rungume shi ina me cewa "kai amma Abdulhadi ka burgeni, kuma ka huta da gorin Abba na kayi kwantai"
Yayi murmushi more like ya'ke kan yace "shiga ki mana sallama da ita"
Girgiza kai nayi na fice cikin takuna na tausayin 'kasa kamar yacce mutane ke fad'amin, shiga nayi tare da sallama ta wayam tsakar gidan ba kowa, kusan sau bakwai ina kwad'a sallama kan wata yarinya da bata wuce 13yrs ba ta le'ko daga wata 'kofa
Tace "wai ance ki shigo"
Da d'ari d'ari na bi hanyar da zata sada ni da 'kofar data le'ko. Na shiga falon inda na tarar da wata dattijuwar mata zaune kan kujera bisa dukkan alamu zata girmi mami nesa ba kusa ba
Gefenta na tsugunna na gaisheta cikin girmamawa, fuskarta d'auke da fara'a ta amsa tare da cewa "daga ina 'yammata?"
Bayani na shiga yi mata kan na gama, fara'arta ta dad'u, waya ta d'auka bayan wasu sakanni naji ta fara magana "samina maza ki shirya Abdulhadi ya zo har da ba'kuwa"
Cikin hikima tarin'ka jana da hira har da tambayata ala'ka ta da Abdulhadi nace mata yaya nane. Wucewar minti sha biyar na fara jin takun takalmi alamun sakkowa daga stairs
A hankali na d'ago da kwayar idona kan samina dake nufo mu, ba laifi samina na da kyau dai-dai ita, murmushi na shiga sakar mata duk da fuskar tata ba yabo ba fallasa kusa da ni ta tsaya
Tare da cewa "muje ko"
Girgiza kai nayi batare dana damu ba nayiwa mahaifiyarta sallama muka yi waje, muna cikin tafiya na gaisheta d'an kallo na tayi kad'an ta amsa tun daga nan naja bakina na tsuke yl har muka fara hango Abdulhadi
Murmushi ta shiga aika masa yayin da gogan naku ya tsare gida nikam cikin zuciyana cewa nake "dama haka masoya suke?"
Sama sama suke hirar da d'an armashi sai de tunda yace "samina ga anty sa'ida da nake ta baki labari"
Bud'ar bakin samina se cewa tayi "naga fa sa'ida" daga haka taci gaba da masa hira, haushin hakan yasa shi binta da um ko um um.
Jikina yayi sanyi da samina dan da alama batayi na'am fa ni ba har addu'a na rin'ka yi dan su gama hirar mu tafi.
A zuwan mu na uku wurin samina kuwa kaca-kaca tayi min a falon gidan su lokacin da naje kiranta har da cemin karuwa, kwartuwa, na rasa miji shine zan li'kewa saurayinta, maganganu dai na 'batanci iri-iri, kalma d'aya dai na iya furta mata a wurin
"Shin samina kinsan cikin mu d'aya da Abdulhadi?"
'Daga murya tayi da cewa "ke malama me kika maida ni, to tsaya kiji ko makaho ya shafa yasan son juna kuke"
Fuska sha'be-sha'be na komawa Abdulhadi, aikuwa ranar samina har dur'kusawa tayi tana bashi ha'kuri yayi biris da ita a 'karshe ya kira sunanta cikin kakkausar murya
"Samina"
Tace "na'am"
Yace "kaf duniya ba me muzanta ko wula'kanta sa'ida na kyale shi ko da kuwa mahaifiyar mu ce"
Yana kaiwa nan yaja hannuna ya zaunar cikin mota kan shima ya shiga ya ja muka taci.
A ta'kaice dai a hutun nan bayan samina mami tayiwa Abdulhadi 'yanmata 6 amma duk dalilina suke rabuwa har gajiya nayi ina kuka
nace "Abdulhadi ka dena zuwa dani tunda ba a 'karewa da dad'i"
Yayi murmushi "anty sa'ida duk wanda ze soni se dai ya so ni tare ni da ke" daga haka ya lumshe ido ba tare da ya kuma furta wani abu ba wanda yake al'adarsa da zarar ya lumshe ido tofa zance ya 'kare bayan haka da kwana uku ya koma canada wanda shima da kuka muka rabu.
♧
Yau da gobe malam yusuf na koyar damu har ya ganeni dan akwai ni da amsa tambaya a aji, Abidin kuwa takaicinsa ke hanata amsa tambayar da yake,Har ta kai idan aikin aji ya bada zakaji yace a bawa jauro ta kawo min, ni dai bansan dalili ba duk da cewa malam yusuf baya yiwa ko wani d'alibi dariya amma ni yana min har jana yake da wasa ni kuma na kasa sakin jiki.
Yau da gobe se Allah dalilina Abidin ta rage jin haushin malam yusuf itama har d'an wasa suke , kuma ko yaushe takan tsokaneni wai malam sona yake sam na'ki yarda da maganarta amma yaushe malami kamar malam yusuf me mugun ji da kansa ze so d'alibar sa wai kuma ni SA'IDA.
Yauma zaune muke ni da Abidin a office d'in malam yusuf kusan minti sha biyar muna jiranshi ya gama da wasu d'alibai ya dawo kanmu.
Sai da ya gama tsaf ya juyo cikin mirmishi yace "kuyi ha'kuri fa yau da aiki muka tashi, sunkuyar da kai nayi Abidin kuma tace "ba komai malam"
Ya kalleni cikin wani kallo me 'kayatarwa yace "to ai 'yar gidana batace komai ba"
Murmushi kawai nayi, tare da kuma yin 'kasa da kaina , haka kullum yake min kuma ko ina naje yana biye dani, ko a makaranta haka ya hanani yiwa ko wani namiji magana ko meye dalili oho?
#vote
&
#comment©Kdeey😊

YOU ARE READING
SA'IDAH
RomanceThe story of a young adult...ku biyoni ciki dan jin abinda ke kunshe da rayuwar SA'IDA, anty SA'IDA, BIG SIS inji ABDULHADI *SOYAYYA *SADAUKARWA *TAUSAYI *KADDARA *JURIYA *ILIMANTARWA *NISHADANTARWA Wannan labari nawa ya bambamta da sauran... Abinda...