® *HASKE WRITERS ASSO💡*
(Home of experts and perfect writers)*SA'IDAH*
Nah
Khadeeja Ahmad (Kdeey)
*wattpad* @Deejaht Ahmad*5*
Tun bayan tafiyar Abdulhadi na dawo wata sukuku ban fiya walwala ba, ko yaushe cikin tunanin sa nake gaba d'aya jikina yayi sanyi sai kace wacce aka aikowa da sa'kon mutuwa.Kullum muna waya da Abdulhadi amma fa tun kafin mu gama gaisawa nake fara kuka, mami tayi ta min fad'a tana cewa na dena yiwa 'kananan abubuwa kuka
Nakan bita da to mami na share hawaye na mu cigaba da hira.
Karatun mu ya d'au zafi muna secound semester aka kawo mana wani sabon lecturer wanda ze d'auke mu 2204 wani course ne me mutu'kar wuya ainihin malamin dake d'aukar mu ya rasu a satin da zamu dawo makarantar, kana ganin lecturer d'in kasan ba wasa a al'amuransa sam.
Fari ne dogo me d'an jiki saje kwance a fuskar sa ba lefi mutumin yana da kyau gun dressing kuwa no.1 ne hatta takalmi kalar kayansa yake sawa hannunsa zagaye da wani tsadadden agogo
Tunda ya fara lecture har ya gama ko alamar murmushi babu a fuskar sa amma Alhamdulillah muna fahimtar karatun, yana gama bayanan sa ya bamu assignment ya tattare ipad da wayarsa ya fita.
Fitarsa ke da wuya 'yammata har da samari suka fara magana kansa wai ya burgesu matan na cewa ya tafi da imaninsu, surutu dai iri-iri.
'Kawata kuwa binta abidin tsaki tayi tace ita har akwai namijin da ze burgeta ne, murmushi nayi kawai dan bansan amsar da zan bata ba.
♧
Kamar ko yau yaushe yau ma muna fitowa daga lecture Abidin wato binta tace min nazo na rakata ice cream take son sha, nace to dan tasan shan sanyi yanzu be dameni ba tunda Abdulhadi ya tafi,Kaina a 'kasa muke tafiya naji Abidin taja wani dogon tsaki nayi saurin d'ago kaina
"Lafiya?"
Da baki ta nuna min abinda take wa tsakin, malam yusuf ne (sabon lecturer d'inmu), wasu d'alibai sunyi gungu yammata guda a gabansa suna masa magana shi kuma yana ta basarwa, ni kaina sai da takaicin yan matan ya kamani dan ganin yadda yake musu
Duk da ba sana'a ta bace tsaki amma wannan karon sai da nima nayi, ice cream d'in da Abidin bata sha kenan ba muka juya.
Bayan wata uku
Muna d'aki na ni da Abidin muna hira kan malam yusuf wai ita a dole taga take takensa na rashin mutunci to ita mafa zata nuna masa ita first class ce gun rashin M.
Kamar daga sama naji an kira sunana
"Sa'ida" na kuma jin wani kiran, ko ba a fad'a ba nasan mamallakin muryar, ai a guje na fita falo na 'kan'kameshi ina ihu had'e da dariya shima murmushi yake na 'kasaita, ihu nane ya tada yaya karima daga bacci, itama baki ya'ki rufuwa.
Ranar dai kusan kwanan zaune mukayi, washegari kuwa duk wani abu da nasan Abdulhadi naso yaci sai da nayi masa da ya gani baki ya ri'ke
"Anty Sa'ida ina zan kai wannan abincin"
Nayi murmushi tare da jan hannunsa zuwa kan dining table nace "na fa sanka Abdulhadi kai rumbu ne"
Murmusawa yayi yace "fad'i su ramadan suji suyi mana dariya"
Na d'ora hannu a baki, "au na manta"
Ai kuwa dariyar su ramadan d'in mukaji, hamisu har da d'an fiton sa, da cewa "ai de munji kan ku"
Nace "ba wani nan"
Ummuhani ta she'ke da dariya tace "wallahi munji anty sa'ida"
Na kalli Abdulhadi cikin sigar shagwa'ba nace "wai sunji Abdulhadi"
"Rabu dasu anty sa'ida na, my big sis, oya zo ki ciyar da 'kanin ki, zo maza mu basu kunya"
Cikin jin dad'i na hau zuzzuba masa na kuma bashi da hannun na.
Duk wani abu da ya faru bayan tafiyar Abdulhadi se da na bashi labari kai hatta da cokula da ake wawwanke wa ko sababbin abubuwa da aka sake sai da na fad'a masa, ina ta zuba labari sai ji nayi muhammad na fad'in
"Taskar labarai"
Aikuwa da gudu na bishi har wurin mami ya 'buya a bayanta yana min gwalo, ni kuma nace sai na doke shi
Mami tace "lafiya anty sa'ida"
"Mami ce min yayi ma'karyaciya"
Muhammad yace "laahh anty sa'ida ba nufi na kenan ba kawai fa saboda kin ta magana shi yasa nace miki taskar labarai"
Na banka masa harara, hannu yasa ya ri'ke kunnuwan sa "am sorry big sis, kefa yayar mu ce our secound mami"
Bansan lokacin dana saki wani murmushi ba na nuna shi da hannu "kar ka kuma kaji 'kanina"
Ya girgiza kai "insha'Allahu"
Hannu nasa na share hawayen da suka fara zubo min, Abdulhadi yace "yanzu sa'ida har yanzu wannan saurin kukan naki na nan?"
Na kuma fashewa da kuka nace "tunda ka tafi Abdulhadi 'yan gidan nan suka had'e min kai, baba sule da Abba kawai nake jin dad'in su, su hamisu da su ummuhani dan sunga sun kamo ni a tsayi yasa duk suka rainani"
Lalla'bani yayi har nayi shiru, mami tace "uhm bari na tashi bazan iya kallon kayan haushi ba"
Na d'ago kaina daga 'kirjinsa nace "kagani ko kagani ko"
Yace "shh...yi hakuri, maza je ki canja kaya kizo muje yawo"
Da murna ta na amsa da "to"
#vote
#comment©Kdeey😊

YOU ARE READING
SA'IDAH
RomanceThe story of a young adult...ku biyoni ciki dan jin abinda ke kunshe da rayuwar SA'IDA, anty SA'IDA, BIG SIS inji ABDULHADI *SOYAYYA *SADAUKARWA *TAUSAYI *KADDARA *JURIYA *ILIMANTARWA *NISHADANTARWA Wannan labari nawa ya bambamta da sauran... Abinda...