*HASKE WRITERS ASSO💡*
*SA'IDAH*
Nah
Khadeeja Ahmad (Kdeey)
*wattpad* @Deejaht Ahmad*7*
Restaurant d'in da malamai ke zuwa nan malam yusuf ya shigar damu yasa a kawo mana irin abincin da muke so, ni dai kunya bata bari naci ba sa'banin abidin daCin abincin ta kawai take yi, yayinda ni kuma nake ta faman juya cokali, zuwa can malam yace min kunyarsa ce ta hanani ci ko?, sunkuyar da kai nayi had'e da girgiza kai
Tsam ya tashi yabar table d'in zuwa wani ya zama na ya juya mana baya, kallon Abidin nayi had'e da sauke ajiyar zuciya kallona itama tayi "ya dai budurwar malam?"
Hararar wasa na mata "bansan rashin M"
"Yau naji mace, to 'karya nayi na zata yanzu tsabar kunyar sa da kike ne yasa kika kasa cin abincin gabanki"
"Hmm..Abidin baza ki gane bane"
Ta d'aga kafad'a tare da fad'in "kinga malama saki ciki muci banza yau kud'in mu ya huta"
Murmushi nayi na maida kaina kan plate d'in gabana, ba laifi naci sosai se bayan mun gama malam ya dawo kwanon gabana ya kalla
"Ah ah lallai 'yar gidana har an kammala"
Lumshe ido nayi had'e da sunkuyar da kai, ya ajiye key d'in motar sa a gabana yace
"Maza kuje mota gani nan fitowa nayi dropping d'inku"
Abidin ce ta fara mi'kewa ta d'auka key d'in ni kuma na mara mata baya, malam kuma ya nufi ciko dan biyan kudi.
A d'an tsukin nan ne malam yusuf ya furta min abinda ke zuciyar shi, duk da bansan meye so ba amma gaskiya ya kwanta min a rai haka zalika inaji a jikina zan iya rayuwa dashi,
Dan yan kwanakin da mukayi dashi yasa na karanci wasu daga cikin halayensa haka zalika duk abinda zai yi se ya fad'a min haia nima ko me zanyi se na tuntu'be shi.
Malam yusuf d'an masu dashi ne domin kuwa kallonsa idan kayi kad'ai zaka san wani hamsha'kin ne ko kuma d'an wani hamsha'kin
Dan irin suturar da yake sawa da irin motocin da yake hawa iri-iri ne. Duk gidan mu sun san malam saboda irin zancen sa da Abidin ke yi
Tun ina kunyar mami har na daina, malam na yawan had'ani da 'yanuwansa a waya mu gaisa kuma da alama na kwanta musu
Se dai na rasa dalili hamisu da muhammad da kuma ramadan 'kiri-'kiri suke nuna min basa san malam haka nan taufiqa wato anti usaina
Da na fara zancen sa zasu had'u suyi ta kishe shi sai kace wanda yayi musu wani gawurtaccen laifi, ni kuma nayi tajin haushi
Har saida mami ta gaji tayi musu ta-tas tace " sa'idan dai da kuke tsokana itace uwarku dan ko bayan rai na ita zata kula daku. Shikenan na samu lafiya
Duk wannan budurin da ake Abdulhadi be san zancen malam ba tunda in muna waya mantawa nake da kowa mu zauna muyi ta bayyana wa junanmu yanda mukayi rashin juna
Hakanan halayyata na fad'a ma Abdulhadi cikina tana nan wannan maganar d'aya rak! Ita na gaza fad'a mishi wato zancena da malam
A 'yan kwanakin nan malam ya matsa min kan son ya turo manyan sa gidan mu. Ni kuma na rasa dalilin da yasa sam bana son yayi min maganar, saboda bansan ta yadda zan fad'a ma mami ba
Dan haka yan lokutan nan cikin damuwa nake, da nayi wa Abidin magana sai tace kar na damu zatayi wa mami halima magana
Haka kuwa akayi a washegari ranar mami halima ta tari mami da maganar.

YOU ARE READING
SA'IDAH
RomanceThe story of a young adult...ku biyoni ciki dan jin abinda ke kunshe da rayuwar SA'IDA, anty SA'IDA, BIG SIS inji ABDULHADI *SOYAYYA *SADAUKARWA *TAUSAYI *KADDARA *JURIYA *ILIMANTARWA *NISHADANTARWA Wannan labari nawa ya bambamta da sauran... Abinda...