® *HASKE WRITERS ASSO💡*
*SA'IDAH*
Nah
khadeeja Ahmad (Kdeey)
*wattpad* @Deejaht Ahmad*3*
Mahaifiyata Maimuna mutuniyar adamawa ce wato bafulatana ce usul mun taso naga gidanmu mu uku ne kacal yara wato Abdulhadi, ni sai ramadan a lokacin duka duka ba zanfi shekara 7 ba a duniya, Abdulhadi 17 sai ramadan dan shekara 2, mami wato mahaifiyar mu ba 'kara min gatatamu take yi ba a rayuwaKomai na namu abin sha'awa ne kuma kowa son mu yake yi duk inda muka shiga zaki ji ana cewa ai 'ya'yan mami ne a lokacin
Zan iya tuna sunan garin da muke, minna cikin jihar naija, bab sule shine drivern mami a lokacin yayinda karimatu ke kula da gida,
Mami bata ta'ba bambanta mu da su baba sule da karinatu ko nace yaya karima dan haka muke kiranta, akwai sha'kuwa matu'ka da 'kaunar juna a gidanmu sosai.
Har Allah Allah nake gari ya waye dan nayi wasa da mami, yaya karima, baba sule da 'yan 'kannena ramadan da Abdulhadi
Abdulhadi ya girmeni nesa ba kusa ba amma ina kiransa da 'kanina saboda ko da yaushe mami ke cemin su duka 'kannena ne tunda ni kad'aice mace hakan yasa nake kiransu da 'kannena, gani dama da san girma dan wani lokacin idan nayi abu se dai kaji ana cewa san girma irin na sa'ida .
Wata rana da yaya karima naji ta kira da alhamis ne mami ta dawo gida hannunta ri'ke da wani yaro da baze fi shekaru 3 ba
Tace min "sa'ida ga wani 'kanin naki, ki kula dashi kamar yadda kike kula da sauran 'kannenki, nayi murmushi
Nace "to mami Allah ya taya mu ri'ko", yaya karima tayi dariya tace "Amin sa'ida"
Kullum da asuba muke tashi in munyi sallah mu zauna yin azkar tare da mami tana fad'a muna fad'a kuma baba sule shi ke mana limanci
Muna karanta "la'ila hai'llallahu wahdahu la sharikalahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai'in 'kadir×100, subhanallahi wa bihamdhihi 100, suratul ikhlas 3, falaq 3, nas 3, ayatul kursiyyu d'aya tare da sauran addu'oin da ake"
Idan mun gama mami zata mana 'karin karatu har zuwa 'karfe 6:30, sa'annan ayi mana wanka muci abinci mu shirya baba sule ya d'aukemu tare da mami
Idan an saukemu a makaranta ya 'karasa da mami office d'inta wanda lokacin tana shugabar gidan marayu ne na minna
In mun dawo zamu ci abinci muyi wanka sannan mu kwanta bacci zuwa 3:30, mu tashi muyi alwala tare da wanke baki (brush), muyi sallah sannan mu kuma zama azkar d'in yamma
Idan mun gama mami zata koya mana karatu , idan mun gama kowa ya d'auko aikin makarantar shi yayi, se a zauna hira kuma, wacce duk yawancin hirar tarihin annabawa ne da sahabbai mami ke bamu
Sai ko tarihin raywarta da wanta abdulhadi lokacin suna yara, nakan tambayi mami wato Abdulhadi sunan yayanta yaci sai tace min eh.
Kuma takan 'kara da cewa kaf duniya ba abinda tafi kusa dashi tare da so kamar wannan yayan nata Abdulhadi.
Ko a gida mami bata san matsantawa Abdulhadi hakan yasa muke kiranshi da d'angatan mami, haka kuma gareni kaf 'yan uwana bani da sama da shi bani da wanda nake so nake kuma 'kauna sama da Abdulhadi
Komai namu tare muke, shi ke koya min duk wani abu da ya shigemin a duhu a makaranta, abincine mami ke had'a mana duka a babban faranti har da yaya karima baba sule ne kawai nasa daban.
Wata rana babar yay karima tazo tafiya da ita gida sakamakon aurenta daya tashi , nasan karima ita ke kula da gida amma har ga Allah na d'auka 'kanwar mami ce .
Haka da naji ance ga babarta zata tafi da ita hankalina ya tashi mutu'ka , mami kuwa kana kallonta duk ta fimu taahin hankali muna ji muna gani aka tafi da yaya karima har mami sai da tayi kuka, yaya karima kiwa dakyar aka fita da ita daka gidan mu.
A lokacin ne duk aiki kamar wanke-wanke, shara, wankin under wears d'inmu da yiwa 'kannena wanka ya dawo hannuna dan lokacin mami bata da lafiya sosai
Idan nace mami meke damunki sai dai kawai ta kalleni tace sa'ida ki zama jaruma kinji ki kula da su Abdulhadi nakan amsa da to mami
A lokacin se naji sabon 'karfi ya zo min, shekarata 10 daidai aikin mami ya maida ita maiduguri, wato gidan marayu na maiduguri
A lokacin ba 'karamar kewar minna nayi ba ko dan ganin su yaya karima ne ko ko dai? Dana ganina na fara sanin kaina.
Watan mu biyu a maiduguri mami tazo mana da yara uku
Muhammad, Kamal da hamisu nan ma haka tace min"Sa'ida ga wasu 'kannen na kawo miki" nace "to mami Allah ya taya ni ri'ko", har zuwa wannan lokacin mami bata samo wata me aikin ba.
Daga mu sai baba sule, muhammad sa'an ramadan ne yayin da Kamal da hamisu sa'annin juna ne aun bawa su ramadan shekara d'aya d'aya kamar yadda naji daga bakin mami.
Bayan shekara biyar
Kullum da safe zan tashi na share gida na tashi 'kannena mu gyara ko ina kafin mami ta tashi dan har zuwa lokacin tana da 'karancin lafiya
Nakanso na hana ta fita aiki sai tayi murmushin 'karfin hali tace to mamana in banje aiki ba da me zan nemo muku abinci tausayin mama ne ya kamani har ni da Abdulhadi idan muna hira nace masa
"Idan na girma zan d'aukewa mami duk wata wahala tamu"
Yakan ce "Allah ya yarda big sis"
#vote
#comment©Kdeey😊

YOU ARE READING
SA'IDAH
RomanceThe story of a young adult...ku biyoni ciki dan jin abinda ke kunshe da rayuwar SA'IDA, anty SA'IDA, BIG SIS inji ABDULHADI *SOYAYYA *SADAUKARWA *TAUSAYI *KADDARA *JURIYA *ILIMANTARWA *NISHADANTARWA Wannan labari nawa ya bambamta da sauran... Abinda...