® *HASKE WRITERS ASSO*💡
(home of experts and perfect writers)*SA'IDAH*
Nah Khadeeja Ahmad
Wattpad @Deejaht Ahmad*10*
Cikin zubar hawaye nace
"Malam sharrin kuma da zaka yi mana kenan, 'kiyayyar da kake wa Abdulhadi har ta kai haka!"Yayi murmushi zance ko dariya kan yayi min wani 'kas'kantaccen kallo yace "sa'ida da ne kuka rufeni bai-bai amma yanzu an wayar min da kai"
"Me kake nufi malam..."
"Nufina shine na gaji da zama da bara gurbi bazan yadda mara asali da tushe ta zama uwar 'ya'yana ba" kuka wiwi nake
Ya cigaba "kinga dama shiru ki kayi sa'ida ni dai ba abinda zance sai Allah ya isa tsakanina da ku da aka munafurce ni"Cikin tsawa nace "malam ya isheka ya za'ayi ka auro ni gaban iyayena sannan kazo kana ce min mara asali!!"
Murmusawa yayi "ke bari na gaya miki sa'idah karatun da mami kuke cewa kome tayi muku kenan amma ni ko da nazo aurenki ba'a nuna min ubanki ba.."
Sauri nayi cikin kakkausar murya na later shi "ya isheka ya isheka malam.."
"Hmm sa'idah me kyawun d'an miciji be isheni ba kuma daga yau kin bar zaman gidan nan kenan tunda duk rufin asirin da nayi miki baki gani ba, ki je na sake ki 'saki uku'.
Yuuu wata jiwa ta d'ebeni da kyar na dafa kujera ina binshi da wani kallon mamaki zuciyata ta d'au zafi rintse ido nayi kan na kalleshi nace "malam nagode amma insha'Allah se Allah ya saka min"
A daddafe na juya na d'auki wayata na kira hamisu nace yayi maza yazo gidana cikin mintuna da basu wuce shabiyar ba kuwa ya iso mayafi kawai na yafa na sameshi a mota "muje" kawai nace
"Mama sa'ida lafiya kuwa"
"Lafiya hamisu kaini naga mami"A rud'e yaja motar, da muka je gida tun kan mota ta tsaya na dira a guje na shiga falon Mani inda na tarar da ita da Abdulhadi, kan cinyarta na fad'a dake bata ga shigowata ba se jina da tayi a firgice ta d'agoni tana kallon 'kofa a tunaninta low wanine ya biyo ni
Hawayen data gani a fuskata Shi ya tabbatar musu ba lafiya Abdulhadi yayo kaina a rikice
"Aunty sa'ida meya faru ko wani abune ya samu maigidanki?"Na girgiza kai, "to menene?"
Hanci naja cikin sheshshe'kar kuka nace "mami ina abba??"
Tace "gaya min meya faru dake sa'idah, me akayi miki""Mami abba kawai nakeson gani" nace bayan na share hawayen, tace "Abba yaje gida zuwa magriba ze shigo, amma menene ya faru kinsani a duhu"
Har zanyi magana Abdulhadi yayi gyaran murya had'e da girgiza min kai se na 'ka'kalo murmushi "bakomai" na mi'ke da sauri jin wani hawayen ya ciko idanuna"
"Sa'idah yaushe kika fara 'boyemin damuwarki?"
Daidai lokacin wayata tashiga 'kara alamun kira nayi saurin cewa "laaa mami ina zuwa kinga hajiyar su malam na kira na" saurin fita nayi daga falon har ina neman fad'uwa, nayi saurin fad'awa d'akin Abdulhadi
Shigowa yayi tare da sakawa 'kofar key a rud'e ya nufoni
"Aunty sa'idah kinsa zuciyata a rud'ani dan Allah meke faruwa?"Cikin hikima na fad'a masa komai Ina kuka har Ina neman shid'ewa, karkarwa Abdulhadi ya fara sai hawaye suka biyo baya be cemin komai ba ya juya ya fita nan na kwanta ina risgar kuka.
Bud'e idona nayi a hankali ganin duhu yasa na tashi na fito bansan na jima ina bacci haka ba dan har magriba ta wuce band'aki na koma nayi alwala na fito bayan na idar na fice zuwa falon mami
Dai-dai lokacin abba ya shigo gidan cikin tashin hankali gefensa Abdulhadi ne fad'a ya shiga yiwa mami kan me zata bar Abdulhadi ya doki mijin sa'ida
Tsayawa tayi tana kallonmu kamar hoto ta gaza furta ko kalma d'aya fad'awa nayi jikinta Ina kuka, Abdulhadi ne yayi 'karfin gwiwar fad'a musu
Abba ya daddafa ya zauna haka ma mami seda Muhammad ya ri'keta falon ya d'au shiru na kusan minti talatin sannan muka Ga Abba ya kama hannun mami sunyi cikin d'aki.
Washegari da la'asar aka kwaso kayana daga mami har Abba banji sun kuma ce min komai ba, Abba ne ma ya sameni har d'aki ya bani baki kan nayi ha'kuri abinda ya faru tsakanina da malam dama Allah ya 'kaddara hakan kar na sake na sa damuwa a Raina.
Kwanaki sunja a makaranta ko lecture din malam muka shiga bana ko d'ago kai balle na nuna na sanshi da yawa mutane basu san mun rabu ba Abidin kuwa kullum cikin tsine mishi take.
Tuni Abdulhadi ya koma wanda kafin ya tafi seda akayi d'an 'karamin fad'a dashi dan cewa yayi lallai sede na datse karatuna na bishi ya samar min makaranta a can mami da Abba sukace sam basu san zance ba da kyar na lalla'bashi ya tafi bayan ya siya min sabuwar mota wai nake amfani da ita dan bayason yawo na cikin napep duniya na kallona.
*Bayan wasu watanni*
Yanzu hankali na ya kwanta se dai akwai wasu tambayoyi da nake bu'katar amsar su sede nasan bazan ta'ba samun amsar ba dan ni kaina bazan iya tambayar ba.
Kullum Abdulhadi ze kirani a waya mu jima muna hira min kuma sha'kuwa da juna hakanan mami na mutu'kar kula dani.
Kwanakin nan na kula da wani Abu tsakanin taufiqa da Muhammad wato akwai alamun soyayya tsakanin su dan yacce take zagewa tayi masa girkinsa daban ta kuma hana kowa sannan ita ke masa hidima dan ko cup yakeso se ya kirata ta kai masa ga wani kallo da suke ma juna da wani iyayin mayana da take mishi ni dariya ma suke Bani dan rannan data ganshi ta rin'ka wani kashe kashen ido ashe hamisu ma ya kula nan mukayi tax tsokanarsu dan taufiqa A ce gurin tsokana har mami da baba Sule da suka shigo suka taya mu.
A satin nan zamu shiga za'a fara bikin Abidin dan haka kullum a tafe muke bama zama.
Satin bikin kuwa komai ya kacame komai nice a kai gashi ango ya had'ani da aboki da Nura senior komai muke bu'kata shi muke contacting aikuwa ranar kai amarya yake fad'amin shifa sona yake
Shareshi nayi a zatona ze hakura, aikuwa kwana uku da kai Abidin gidanta Sai ga wayarta wai jura ya hanata sakat haka suka kafamin naci har seda na amince na fara kula nura.
Wannan karan da wuri na fad'awa Abdulhadi yayi d'if kamar an d'auke mishi wuta se daga can yayi min fatan alkhairi.
Tsaftatacciyar soyayya muke da nura dan ma na kasa sakin jiki amma be ta'ba nuna damuwa da hakan ba mami kuwa se murna take yi kome ta gani tace bari ta d'aukar min nakance mata ina da komai fa mami se tace bakya ganin wancen ya tsufa nafison ma kaiki da komai sabo
Ana haka muka tafi China da mami da kuma mami Halima satinmu you muka juyo da kaya Niki Niki dan komai suka gani se sun kwasomin kai hatta da furnitures seda suka siyo min naji dad'in tafiyar sosai
Lokacin nan mami ta kuma shagwa'bani dan kwana ma d'akinta na koma, kamar ko yaushe kwance nake a bayanta muna hira inda take bani labarin yarintar ta da yayanta Abdulhadi na tashi zaune
"Mami Ina to shi yayan na'ki yake yanzu?"
"Yana nan sa'ida"
"To ya baki ta'ba kaimu wurinsa ba"
Ta juyo ta kalleni "Abubuwa da yawa sa'idah,..inajinki ciwo sa'idah 'ko'kari kawai nake"
A rud'e na kalleta cikin rawar mirya nace "mami wani irin ciwo?"
Tashi tayi zaune tare da kamo hannuwa na bayan ta kalleni tayi wani guntun murmushi
tace "Ciwon zuciyata"©️Kdeey😊

YOU ARE READING
SA'IDAH
RomanceThe story of a young adult...ku biyoni ciki dan jin abinda ke kunshe da rayuwar SA'IDA, anty SA'IDA, BIG SIS inji ABDULHADI *SOYAYYA *SADAUKARWA *TAUSAYI *KADDARA *JURIYA *ILIMANTARWA *NISHADANTARWA Wannan labari nawa ya bambamta da sauran... Abinda...