® *HASKE WRITERS ASSO*💡
(home of experts and perfect writers)*SA'IDAH*
Nah Khadeeja Ahmad
Wattpad @Deejaht AhmadAssalamu Alaikum lovelice I'm back dafatan zakumin hakuri najina shiru da kukayi hakan ya faru ne bisa wasu dalilai hope za amini afuwa and albishirinku tuni littafin sa'ida ya kammala so ba jira insha'Allah mun fara kenan har se mun kai Aya update akai akai so follow me sweathearts muci gaba da gashi #love
*9*
Washegarin ranar lahadi da yamma aka kaini d'akina wanda yake 'bangarene guda aka gina cikin gidan su malam, wuri yayi kyau sosai dan a ranar na kuma tabbatarwa ni d'in ta gaban goshin mami ce jama'a se zuba gud'a suke wasu ko kira suke masha'AllahDaga 'kasar dubai mami tayo order kayan d'akina kai hatta da curtains a can ta siyo haka zalika kayan kitchen, bayan duk an watse ya rage daga ni se adda usaina wacce mami tace ta jira isowar ango, hannuna ta kama muka shiga le'ka d'akunan gidan ganin irin dukiyar da mami ta narka se na tsinci kaina da zubda 'kwalla tare da yiwa Allah godiya da ya bani ita matsayin mahaifiya
'Karar bugun 'kofa ce ta fargar da ni da sauri adda ussaina ta kufa shafe min fuska da powder tare da shafa min lipglow nan da nan na kuma haskakawa ta gyaran veil sannan ta nufi falo ri'ke dani ta zaunar dani saman kujera
Koda ban d'aga kaina ba jikina na babi idanunsa na kaina dakyar na iya seta kaina ina lazimi a zuci dede lokacin da naji muryar ramadan na fad'in malam ka taimaka ka bawa tawa amanar hanya ta wuce mu baku fili
Gyaran murya yayi tare da d'ora hannuwa a kai yana sosa cikin kanshi da key yace " afuwan 'kanina yayar taku ce duk ta...."
Saurin katse shi adda tayi da cewa"se da safe malam, anty sa'ida ki saurari kirana Allah huta gajiya"
Gyad'a kai nayi tare da sadda kaina hawaye masu d'umi suka ziraro min yanzu shikenan na shiga wata sabuwar rayuwa wacce ba mami nor 'yan uwana baki d'aya" jin hannuwa bisa nawa ana goge min hawaye yasa nayi saurin d'ago kai de-de lokacin da malam ya d'aga mayafin daya rufen fuska
"Masha'Allah, tsarki ya tabbata ga wanda ya tsara wannan kyakkyawar halitta", sunkuyawa ya kuma yi tare da kaiwa tafin hannuna sumba kan ya tashi ya zauna gefena ya shiga rage min gwala-gwalan dake sanye a wuyana da kuma hannuwa na daga 'karshe ya jani zuwa toilet a cewar sa dan mu d'auro alwala dan nuna wa ubangiji farincikin nuna mana wannan rana wanda daga 'karshe daren ya zame min me tsayi, tsayin da har gobe bazan ta'ba mantawa da shi
Dare ne wanda ya kunshi abu biyu a gareni na farko ina farin cikin nakai babban abunda duk wata cikakkiyar yarinya budurwa 'yar mutunci take mafarkin gani, wato mijina ne ya fara sani na, na biyu kuma ina me ba'kin cikin ina tarayya da miji na amma mind d'ina na can wata duniya wurin tunanin abinda tasan ya mata nisa nisa na sosai.
Washegari na tashi sukuku kwakkwaran motsi wannan dakyar nake yi Allah ya taimake ni mami ta turo mana da kulolin abinci masar bauchi da miya se kunun gyad'a irin na 'yan adamawa.
"'Yar so" shine sunan da 'yan gidansu malam ke kirana da shi acewar su wai kowa ya ganni farat d'aya nake shiga ran shi, na kanyi murmushi kawai dan nasan wurin mami na gaji haka dan itama haka mutane ke fad'i a kanta.
Muna zaune lafiya da malam da kuma iyayensa, kullum sona da 'kaunata na dad'a ruruwa a zuciyar malam, zuwa yanzu da na d'auki kusan sati biyu a gidan malam muna waya da Abdulhadi kusan sau hud'u ko biyar a rana, har malam ya fara 'korafin anya soyayyar da nake wa Abdulhadi bata kere tashi ba kuwa, na kanyi murmushi kawai nace kowa san da nake masa dabam.
Rannan dai malam ya rutsa ni kan lallai na fad'a mishi tsakanin shi da Abdulhadi wa nafi so, neman duburburcewa nayi na fara kame-kame , zuwa can dabara ta fad'omin na kallesa tare da kashe masa ido bayan na yi masaki kan cinyarsa na sar'kafo wuyansa tare da matso da fuskata daf da tashi

YOU ARE READING
SA'IDAH
RomanceThe story of a young adult...ku biyoni ciki dan jin abinda ke kunshe da rayuwar SA'IDA, anty SA'IDA, BIG SIS inji ABDULHADI *SOYAYYA *SADAUKARWA *TAUSAYI *KADDARA *JURIYA *ILIMANTARWA *NISHADANTARWA Wannan labari nawa ya bambamta da sauran... Abinda...