UWAR MIJINAH

5.4K 304 6
                                    

_*INTELLIGENT WRITERS ASSO*_✏

    🌺 *UWAR MIJINAH..*🌺
          _(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri tareda biyayyah mai tsanani)_

      *ALKALAMIN:JANAF*💖
      *WATTPAD:JANAFNANCY*

*Dedicated to my BLOOD Sisters JANAF*

    _Alhamdulillahi Rabbil Alamin....Godiya ta tabbata ga ALLAH Subuhanahu wata"ala wanda da ikonshi ne komai ke faruwa,...Aminci tare da Rahama da gafara su tabbata ga shugaban fiyayyen Halitta Annabinmu MUHAMMED (SAW),tsira da Aminci sukara tabbata garesa shida Alayansa da sahabbansa gabadaya_

_*GARGADI:LABARINA (FICTION STORY) NE NAYISHINE DOMIN FADAKARWA,DA NISHADANTARWA DUK WANDA YAGA WANI ABU WANDA YAYI DAIDAI DANA SUNA,KO HALLAYA,KO NA GARI,TO DUK ANSANE DOMIN KAWATA LBRI..AGUJI JUYAMIN LBRI KO SATAR FASAHA,KUMA ALLAH YA ISA GA DUK WANDA YAKARA SIYARMIN DAWANI BANGARE NA LBRINA,..KAMAR YADDA YA FARU A NAZIR..*_✌


*Hohoho chai chai Janaf freeking fans...Nasan zakuyi suprise saboda gobene..promise dina daku..,But my Sahiba HAFSART HAFNAN..Itace tace Nabaku update yau sunday 7/7/2019..Saboda yadda take kaunarku so duk wanda yaci karo da wannan page din juz yayi mirmishi bayan ya shekamata albarka lols*


   _*KARAMCINKI NE SILA...FEEDHOM❤Hakika karamcinki ne sila,Mutumcinki ne sila,Martabanku ne sila,Karramawanku ne sila..Dattakon ki ne sila tare Karamcinki gareni yake ma"abociya Fara"a da Annushuwa..,INA ROKON ALLAH DUK INDA KIKA SANYA KAFA ALLAH YA CIGABA DA DAFA MIKI...YAYIMA RAYUWARKI ALBARKA DAKE DA ZURU"ARKI....Janaf tana Matukar girmamanki..Zuciyata haryau takasa mantawa da alherinki gareni Allah yabiyaki da aljannah mafi soyuwa FIRDAUSI*_🙏

*SUNDAY 7/7/2019*
*3:00Pm*


      *AM BACK*🤝

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

  *NO:1*

*ABUJA*

  
*MAITAMA  DISTITRITE*

         """"Saukowa take daga step cikin Takun isa,sanye Take da riga da zani na Atamfa super wax..,Tasanya wani katon lifaya tayane dukkan jikinta dashi harzuwa kanta hannunta da wuyanta sanye da zinare suna kyalli kallo daya zakamata ka fahimci balarabiyace ta usili,doguwar mace ce wanda kudi da hutawa suka maida ita
yar Dumaduma,fuskarta mai dauke da doguwar fuskar da dogon hancinta har baka..,Gashin idanunta zarazarane kamar tayi kari dan bakinta karami dashi..Gashin kanta kuwa har gadon bayanta yake... *HAJIYA SUHAIMA KENAN*..Hakimar mace ce Kyakyawa kin kowa kin wanda yarasa akallah zata bama shekaru 50 baya ammh bazaka taba cewa tayi wannan shekarun ba domin kana kallonta zaka hango zallah kurciyanta saboda yadda yanayin jikinta yake da kuma Shikanshi Gishirin kyan bai Tafi ba

  Cigaba da saukowa tayi kafarta cikin wani flat din,shoe mai kyau da tsari saukowa tayi ta bayyana cikin wani katon falo wanda yake zagaye da Royal chairs hadaddu masu garari dakyawu,golden colour sai wani katon Plasma wanda yacinye Rabin falon in kana kallo kamar agun ake gudanar da komai falon gabadaya agyare yake komai tsaf sai tashin kamshin Turaren wuta yake.

   Kan Daya Daga cikin kujerun Falon ta yada zango bayan ta kinshigida da kujera tana duban agogo wanda yake wani makeke daga yammah acikin bango wanda shima yamamaye Rabin bangon daidai daya buga karfe 9:00pm nadare..,Tsaki taja bayan tadan mike cikin kasala ta Furta.."Karime..Da dan karfi dagachan bangaren naji an amsa da Na"am hajiya..Kafin wacce aka kira da karime ta bayyana Afalon.

  Cikin Rawan jiki wata yar dattijuwa ta durkushe gaban matan tana Fadin"Barka da Fitowa hajiya.."Yamutsa fuska tayi kan tace cikin Hausan ta data chakule da Larabci"Ki shiga bedroom dina ki daukomin Phone dina"Tafada tana yarfa hannu"Cikin Rawan jiki Karime ta mike tana Fadin"Angama hajiya"Tafada tana Hawa step din.

UWAR MIJINAHWhere stories live. Discover now