UWAR MIJINAH

1.7K 77 2
                                    

_*INTELLIGENT WRITERS ASSO*🖊_

🌺 *UWAR MIJINAH..!*🌺
        _(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)_

       *ALKALAMIN:JANAF*💕
        *WATTPAD:JANAFNANCY*

*DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF*

_I DEDICATED dis page to u ANTY FATIMA(In low)...Hakika kirkin gareni sai dai nace ALHAMDULILLAH..Kulawanki akaina sai dai nace MASHA ALLAH,..Alherinki gareni kuma Sai dai nace ALLAH YAYI MIKI SAKAYYAH..,Bayan ya iya miki Abunda kika gaza..Tanque So much Janaf Relli Appriciate_🌹

*NO 7*

   
........Saurin kakaro mirmishi yayi yana kara riko hannun Ummi yake Fadin"Normal Ummi kaina ne yadameni da ciwo dat why nadawo gida"Yana Fadin Haka Ummi ta rude tafara taba wuyansa tana fadin"Ayyah shiyasa naga kayi wani iri oya muje kaci abinci na baka magani banison zama da ciwo kasani son"Tafada tana jawosa suka Nufi hanyar Falon ushe na binsu abaya dauke da yar jakarsa.

  Suna shiga falon tashiga kwalama lami kira wacce ke kichen tafito Arude tana Fadin"Hajiya lafiya kuwa naji kiran ne daga Sama" Ummi takalleta daidai lokacin da Mu"azzam ke zama kan kujera hannuwansa duka biyu dafe dakai tace"Ina lafiya son ne yadawo gida ba lafiya"Dafe kirji lami tayi tana Fadin"Munshiga uku hajiya yallaban? Tafada duka idanunta waje.
 

   Ni tara na shiga bama uku ba, lami,abinci zaki Taimakon dashi yaci na bashi mgani"Tafada kamar zatayi kuka da sauri lami takoma da baya tana Fadin"Yanzu kuwa hajiya..Yallabai sannu,Allah kenan yanzu yanzu da lafiyanka anjuma kuma ta kubcemaka"Tana wannan mganar tafada kichen din karime da Uwani na tambayanta lafiya takwashe komai tafada musu suma din dafe kirji sukayi idanuwa waje kafin su cikin rawan jiki su fice zuwa falon.

  Koda sukaje sun iske Sani maigadi da Falalu durkushe sunatama yallabai sannu wanda ke kwance kan cinyar Ummi tana shafa kansa tana jeramai addu"o"i tana tofamai bisa kai,kamar zatai kuka kokuma ciwon yadawo jikinta nan su karime ma sukabi ayari suka zube suna jeramai sannu wanda ke amsamusu dakai kawai ammh a zahirin gaskiya jiyake dama shine su domin su basu da wata damuwar kamar yadda yake ciki,lafiyansa kalau kawai yarasa mezaicema Ummi ne, wanda hankalinta zai kwanta,to gashi bai tsiraba shiya manta yadda in yana ciwo Ummi haka zata sakashi gaba tana kuka bata sukuni sai ya samu lafiya..To yaudin ma hakane yafaru ita tadinga bashi abinci abaki Wanda yakeji kamar yana cin madaci ammh hakanan yaita Turawa yana gama ci dama tama Family doctor dinsu waya Dr Abduljabbar wanda yace yana hanya.

Koda Dr Abduljabar yazo yaduba mu'azzam kawai yace Rashin Samun hutu ne alluran barci yamai yace ya kwanta yasamu barci na good 5 hours yana tashi komai zai koma Normal,ai Ummi ta dakanta ta rikeshi har dakinta ta ciremai,takalmi da Socks taciremai caot din,ta kwantar dashi bisa gadonta tana Fadin"Oya sleep kaji dai Abunda Dr yace ko'"Yagyada mata kai yayi, sai tacigaba da cewa'Bani son katashi sai na tasheka da kaina so Rest kaji son"Tafada tana shafa kanshi.

 

Kallonta yakeyi kafin yariko hannunta yace"Nagode Ummi na Nagode"Yafada idanunsa sun kawo kwallah kafin yayima hannun kiss mirmishi tayi tamaidamai kiss din bisa goshi tana Fadin"Iz my duty son..Love u so much"Tafada tana kara kissing dinsa bisa goshinsa shikuma lokacin alluran tafara aiki idanunsa na lumshewa blanket tarufamai zuwa kwankwasonsa kafin ta fice bayan Ta rufomai kofa..Ajiyar zuciya ya sauke yanajin kamar ya fashe da kuka..Yazaiyi Baffa shettima zai watsama kasa a ido ko Ummi wacce ta sadaukar da fatincikinta akansh,ta sadaukar da dukkan jin dadin Rayuwarta zuwa gareshi,yasan cewa Ummi bazatataba fahimtarsa ba kilama tayi Fushi dashi Fushi na har abada..Da wannan Tunanin barci yayi awon gaba dashi.

   """"Saida yashafe wajen awa shidda yana barci kafin yatashi shima din kiran sallar mangarib ne yataadashi wanda daman haka yake komai Nauyin barci wlh ana fara kiran sallah Allah ke tayar dashi..daidai lokacin daya mike Ummi ta shigo dakin Ganinsa zaune yasa Takarisa tana Fadin" Nasan daman yanzu zaka tashi shiyasa na shigo"Tafada tana zama kusa dashi wuyansa tataba zuwa kansa tana Fadin"Ya jikin hop u feel better Now, son?"Tafada murya cikin Damuwa lumshe ido yayi kafin ya bude cikin sansanyar murya yace"Naji Sauki Ummi daman Ciwon kai ne,fa kawai"Yafada yana kallonta.

UWAR MIJINAHWhere stories live. Discover now