UWAR MIJINA

1.8K 74 1
                                    

_*INTELLIGENT WRITERS ASSO*🖊_

🌺 *UWAR MIJINAH..!*🌺
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)_

*ALKALAMIN:JANAF*💕
*WATTPAD:JANAFNANCY*

*DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF*

*NOT EDITED*⚒

*NO.8*

'''''''''''Lami da Uwani Dake kichen suna kokarin hada breakfast sukaji wannan ihun tare da kiran Sunan Ummi,cikin Dimautuwa suka fito falo nan sukaci karo da karime itama ta rumtumo zata shigo kichin din hannunta dafe da kirji take fadin"Lami kunji abunda naji kuwa?'Tafada tana haki.

Lami bata samu zarafin mgana ba ,sai ga Sani maigadi da Falalu mai bawa fulawa ruwa da ushe suma sun Rumtomo zuwa falon Suna tambayan lafiya ihun me sukaji haka"Karime ta nuna Saman Hajiya tana fadin"Wlh bamu Sani ba ammh kamar daga bangaren Hajiya ne fa"Basu samu zarafin mgana ba suka ga Yallabai ya fito cikin tashin Hankalin hannunsa dauke da Ummi wacce ke halinn rai da Mutuwa.

Cikin sarsarfa yake saukowa yana Fadin"Bring d car plz"Yafada cikin tashin Hankali ganin haka yasa ushe rumtumawa waje ya bude motar yallabai wanda ya fito da ita 607 kirar Piogion ,su karime ko hannu suka daura akai suna fadin"Mun bani hajiya innalillahi wa"inna Alaihirraju"un"Haka suketa maimatawa har mu"azzam ya fice da sauri.

Kokafin sufito tuni har yasakata a mota ushe yaja sani ya budemusu get sun fice cikin hanzari..Lami da karime jikinsa babu inda baya Rawa Uwani tace'Mun bani meyafaru da hajiya ne'tafada kamar zatayi kuka babu wanda ya iya cewa komai sai ma karisa da sukayi gun sani maigadi wanda ke zaune da falalu suma suna janjanta Abun haka sukayi tsaye tsuru tsuru babu mai iya cewa komai kuma sun kasa komawa sucigaba da aikin gabansu.

Cikin Abunda baifi minti sha biyar ba suka bayyana acikin babban asibintin nan *SPECIALIST HOSPITAL ABUJA* Ushe ne yayi saurin fita ya rumtuma cikin asibitin yana kiran Nurses suma cikin rudewa suka dauko abun daukan mara lafiya suka biyoshi ammh kafin kace me har sunci karo da Mu"azzam ya dauko Ummi ahannunsa,cikin Tashin hankali yake kwalama Doctor kira..Dr Abduljabar ne ke kan Duty ranar kuma daman Asibitin nan asibitinsu nan suke da fayel tun bayan dawowarsu Abujan da azama.

Ko takan Nurses din dake kokarin amsan Ummi su sanya bisa gadon jinya dake hannunsu baiyi ba,kai tsaye office din DR.Abduljabbar ya shiga yana Fadin"Dr. Save my life Ummi na "Yafada kamar zai fitar da kwallah.DR.Abduljabar dake zaune yana duba patient yayi Saurin mikewa yana Fadin" Brr.Mu"Azzam meyasamu Ummi kuma"Shima yafada cikin Tashin hankali kafin yayi mishi nunu da dan gadon dake office din yana Fadin"Drop her here"Yafada yana kokarin taimaka ma Mu"azzam din.

Patient din Dr.Abduljabar yabawa hakuri ta jirashi awaje cikin gaggawa yafara gwaje gwaje dakuma kokarin farfado da Numfashin Ummi wanda yadauke gabadaya shiko Mu"azzam yakasa zama fadi yake"plz Ummina don"t do dis To me,inkika mutu rayuwata tashiga lahaula plz wake up nayi miki alqawarin bin dukka umarninki"Yafada cikin wata irin karyayyan murya lura Da Dr.Yayi baya cikin hayyacinsa sai ya kallesa yana fadin"Brr.Cool down Karka damu Ummi zata tashi bawani abu bane seriuos kawai taji Abunda yadan Firgitatane.So Abunda nakeso dakai kabani wuri in gudanar da aiki na plz" yafada kamar yana lallashinshi kuramasa ido yayi kafin yakada kai ya juya ya fice.

Sai da DR.Abduljabar ya kwashe fin awa kana ya fito wanda Mu"azzam ke kofar office din yana safa da marwa cikin tashin hankali ya rike Dr.Yana Fadin"Dr karka cemin Ummi bata tashi ba don Allah"Mirmishi yayi kafin yadafa kafadarsa yana fadin"is ok Brr.Mu"azzam Ummi tafarfado Cikin Nasara alluran barci nayi mata..Karka damu kamar yadda nafadamaka wani abu ne taji kota gani, wanda ya matukar razanata har yayi sanadiyar sumarta ammh yanzu ta farfado komai Normal insha Allah"ajiyar zuciya ya sauke yana fadin"Alhamdulillah..."Dr.Yayi mirmishi yana fadin"Ummi baxata mutu tabar mu"azzam ba saboda dayansu bazai iya rayuwa babu daya ba..Bantaba cin karo da soyayyar uwa da 'da irinku ba anyway kuna burgeni sosai"yafada yana bubbuga kafadansa

UWAR MIJINAHWhere stories live. Discover now