Uwar mijinah

1.8K 61 1
                                    

_*INTELLIGENT WRITERS ASSO*🖊_

🌺 *UWAR MIJINAH..!*🌺
        _(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)_

       *ALKALAMIN:JANAF*💕
        *WATTPAD:JANAFNANCY*

*DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF*

                  *NO 10*

     """Awa uku suka shafe a sama,kafin jirgin ya saukesu a babban Filin jirgin dake birnin na maiduguri,Mu"azzam da kansa yakira Bukar yafada masa isowarsu wanda dama tun suna gida yafada masa zasu biyo jirgi In sun kariso azo a daukesu.

  Bukar da kansa yazo filin jirgin ya daukesu zuwa chan gidan nasu daya kachame da al"umma mata da maza wa"inda suka zo daurin aure,baban Falon Na gidan Bukar nan aka saukesu wanda sukansu yan"uwan Bukar din da sukayi tozali Da mu"azzam din sai da suka raina kansu domin sunga tsantsan  kyau,ilimi da kamala tareda tsantsan kwarjini da dattako.,Ba shakka zahirah ta dace da samun gwarzon Namiji haka suke fadi duk wanda ya fito daga falon bayan sun gaisa,Bukar daganshi ya shiga cikin gida inda mata ke gudanar da sha"aninsu yayi ma mahgana mgana kan akawo masu Mu"azzam abinci kafin su wuce daurin auren,Jin isowar ango yasa gidan yadau guda lokaci daya.

    Kafin kace kwabo an cika gaban su mu"azzam da abinci Nau"i na dabam dabam sai wanda suka zaba,Shureim ya kalli Mu"azzam yace"Ango fa kasha kamshi,to ya ne zaka taba ne kafin mu wuce"yafada yana dagamai gira.

  Tsaki Mu"azzam yayi kafin yace"Sai dai kai,domin naga kamar kafini bukata"Yafada yana Cigaba da dannan wayansa,Dariya su brr barau suka sheke dashi suna Fadin"Shima yana kukan aure so ba cin abinci"Kara darawa sukayi kafin Shureim yacire babban Rigansa yana fadin"To Ango ayi kuka lafiya,yan"uwa ku sauko muyi mu harraka kafin kuma na anjuma"Yafada yana zama lokaci daya da bubbude kulolin gabansa,Sinasir ce sai na biyu Tuwon shinkafa sai Farar shinkafa.

  Sinasir suka zuzzuba da miyar Alaiyyahu wacce taji nama da manshanu suna ci suna zolayansa suna dariya,Shiko yama gefe ko kallonsu bayayi yana ta latsa waya abinsa Shureim ya kallesa yana tura sinasir abaki"Wai nace ba"Yafada yana kallon Mu"azzam wanda ya dago yana kallonsu.

  Ganin haka yasa Shureim yace"Amaryan ba nan ne gidansu ba"eh sai akayi ya"mu"azzam yafada cikin dage kai,Dariya shureim yayi kafin yace"yo ko gilmawarta banji ba,balle kamshinta kasan ance yan maiduguri badai kamshi ba"Yafada yana tauna kashi Dariya Dr Abduljabar yace"Kwarai su dabam da kamshi aka sansu"Kauda kai Mu"azzam yayi kafin yace"Sai ku shiga ciki duk wacce kuka gani tana kamshi itace amaryar"Yafada yana wani hararansu dariyan shakiyanci suka shekemai dashi sunayi suna dibam garan abinci shiko yayi musu banza.

  Ahaka suka kammallah kafin duk su share hannayensu da bakinsu da Tissue,babu dadewa sai ga bukar yazo yace su fito su shiga ciki su gaisa da googonin Zahirah kafin su rankaya ,zuwa gun daura auren lokaci ya kusa,Cikin jin dadi suka mike mu"azzam na baya baya,suka iza keyarsa gaba koda suka shiga nan suka ga dangi kowacce taci adonta ammh fa sun dane jikinsu ciki lifaya wanda ya burgesu shureim sun gaisa da kowa da kowa don kowani daki sai da suka shiga,kanwar bukar itace autansu Aisha sunanta suna cema Ashe ta fito da gudu ta wani kasko ahannunta wanda yake cike da Rushin wuta ga turare yana fitar da hayakin kamshi tafara zagaye Mu"azzam dashi tana sakin guda,nan da nan guri ya kaure da guda da wake wakensu na chan sai abun yakoma burgesu shureim tuni suka fitar da wayoyinsu suna daukan bidiyon yadda mata suka zagaye mu"azzam kowanne rike da kaskon Turare suna mai Feshi da hayaki,tare da guda,dakyar dai suka barsa ya isa gaban mahgana wacce keta faman saka mishi albarka bayan tasaka hannunta bisa kanshi"Allah ya albarkaci Aurenku moodu da zahirah,Allah yayi ma rayuwarku albarka,Allah ya baku zuru"a tagari,Allah ya zaunar daku lafiya,ya kauda dukkan Fitina akanku..Yaasaka ace gwara da akayi"Tagama fada hawaye suna zubomata gabadayan jama"an gun amsata mata da Amin.

UWAR MIJINAHWhere stories live. Discover now