UWAR MIJINA...!

5.7K 281 174
                                    

*🌺UWAR MIJINA..!*🌺
   _(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)_

          *Alkalamin:JANAF*
          *wattpad:Janafnancy*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*Intelligent writer's Asso*✏

*NOT EDITED*⚒

                *NO 12*

        Cikin faduwan gaba da Firgici ya waigo yana fadin"Na"am Ummi na.."Yafada cikin nuna kulawa,kallonsa tayi fuskarta babu Annuri tace"Kazo ina son mgana dakai ne"jin haka  yasa,yafara takowa ya iso gareta Harda zai zauna bisa gefenta kan kujera sai wata zuciyar ta haneshi,kawai sai yanemi waje gefen zahirah dake sharban kuka ya zauna.

  Ummi tayi kasake tana kallonsu cikin takaichi tace"Kai miye haka? tafada tana hararansa dagowa Yayi yana fadin"Na"am me kika ce"Yafada kamar baiji metace ba

  Kallonsa tayi tana fadin"Taso daganan kafin na saba maka,yaushe ka chanza da har kafara zama kusa da wata bayan ni"Tafada da kakkausan murya Cikin mamaki Mu'azzam yakalli zahirah dake gefensa wacce Kanta ke sunkuye tana sharan hawaye duk da haka akwai tazara tsakaninsu.

Rausayar dakai yayi ya mike yana fadin"Am srry Ummi..."Yafada yana zama kusa da ita,kauda kai tayi tana wani cin mgani kafin tadago tana kallon Zahirah cikin wani dan lokaci tana nazarinta Aranta take fadin"Shegiya komai irin na uwarta ne,haka uwarta take Macijin sari ka noke"Tafada cikin ranta lokaci daya tana jan tsaki afili,mtsewww..wanda sai da Mu'azzam ya kalleta.

   Gyara zama tayi tace cikin kakkausan murya"Ke..."Tafada cikin tsawa Zahirah dake durkushe tadago da hanzari tana kallon Ummi lokaci daya kuma tayi hanzarin janye idonta saboda ganin yadda Ummi ke binta da kallon Tsana hawayen dake kokarin zubomata suka kwaranyo Ummi tace"Ke...Don Ubanki kinaji ina kiranki Shine don kin rainani kikayi banza dani"Tafada cikin bacin rai.

    Zahirah tadago cikin rawan murya tace"Na.."am.."Ckin tsoro da kuka harara Ummi ta sakarmata kan tace"So nake ki bude kunni dakyau kiji,nan gidan ba gidan Shettima bane balle na uwarki Fadi,nan gidan Suhaima ne wanda gudan jininta ya gina mata"Tafada cikin gadara,Mu'azz am dake gefe yana latsa wayar hannunsa saida zuciyarsa ta tsinke ta wutsiyar ido yake kallon yarinyar yarda take toshe bakinta ammh duk da hakan hawayenta sun kasa tsaya,lokaci daya yaji wani abu aransa koba komai bai dace ace jiya daga kawo yar mutane ba,Ummi ta tasata agaba.,bai gama tunani ba yaji Ummi na cewa.

"Abu nagaba kingan ni nan"Tafada tana nuna kanta gyada kai Zahirah tayi kafin Ummi tacigaba da cewa"Duk duniya banda makiyiya kamarki bar ganin kina mtsayin matar dana,don ni ban daukeshi aure ba"Tafada cikin halin ko inkula kafin tacigaba da cewa"Nasan an baki lbrina kuma kinsan Abunda Uwarki da Shettima suka hadu suka min,so no need na sake miki tuni,domin kinfi kowa sanin cewa sai kin girbi abunda suka Shuka,kafin nan dole namiki gargadi mai tsauri game da dana,ba ganin yana mijinki wlh billahil azim ko kallon arziki ban amince kimai ba,ke ko gaisuwa bance dole ba,bani bukatar ki rabi dana,bani bukatar kisan kammaninsa koda wasa na kamaki kina kallonsa ko kina mai mgana wlh sai na yanka ki"Tafada cikin tsawa lokaci daya tana zaro ido

  Ba Zahirah kadai ta tsorata ba, harda Mu'azzam wanda yadago da sauri yana kallon Ummi kan yace"Haba Ummi wann...!Kai.."Ummi ta katsesa da tsawa kan tace"Zan saba maka nayi magana dakai? tafada cikin Fushi rusunar dakai yayi yana fadin"Allah ya huci zuciyarki kiyi hakuri bazan kara ba"Wani kallo ta jefeshi dashi kafin ta juya takalli Zahirah wacce ke kuka harda shessheka tace.

  "Kinji ko baki ji ba"Tafada cikin mata tsawa da sauri Zahirah tagada kai wani tsawan Ummi ta dakamata kan tace"Don Uwarki baki da baki ne"Saurin bude baki Zahira tayi tana fadin"Na..J.....i..Cikin rawan murya da kuka Gyada kai Ummi tayi kafin tace"Na biyu ban lamunce kidinga giftamin afalo na ba,don na tsani naci karo da Fuskar munafukar uwarki ataki Fuskan,saboda haka kiyi nesa dani tunkafin wata zuciya ta debe ni na illataki"Tafada cikin nuna zata aikata,Abunda tace din.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 26, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

UWAR MIJINAHWhere stories live. Discover now