UWAR MIJINA

1.8K 46 0
                                    

_*INTELLIGENT WRITERS ASSO*_📝

    *UWAR MIJINA...!*
    _(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tareda biyayyah mai Tsanani)_

     *HAKKIN MALLAKA:JANAF*💖

   *AM BACK AGAIN..😍WIT ANODA HRT TOURCHING STORY..✍JUZ GIVES U A FOLLOW*👉

   _*Ya it me JANAF😘....masoyana masu bibiyar lbarina gani nasake zuwa muku akaro na Hudu..Cikin wani salo na dabam mai Tafiya da salon zuciya❤Salon na dabam ne ba irin na MA"AIKACIN KAMFANI BANE🏢balle Na NA TAFKA KUSKURE🙆kuma ba irin na NAZIR👧bane...UWAR MIJINA..! Tafiya yake da salo mai Natsar da  zuciya,ku Natsu kuma ku lura wajen karban Sakon lbarin..Nikuma zan himmatun wajen kyautatamuku..Assalamu Alaikum..Janaf*_💖
  


*Kadan Daga cikin labarin UWAR MIJINA.!*

      *DURLING SON* Naga tayi dialing kafin takara wayar bisa kunnenta..Daga chan bangaren aka dauki wayar da cewa cikin tsantsan murna da Farinciki.. *UMMINA* Ajiyar zuciya tasaki mai karfi duk farinciki ya mamayeta najin muryan gudan jininta cikin koshin lafiya..Bai hanata dakewa tace"Where are u? kafita tun Safe baka dawo ba"Tafada da hausanta wacce take chakule da larabci ajiyar zuciya ya sauke kan yakara kwanciya bisa kujeran bayan motan hannunsa na bisa kansa yana shafawa yafurta"Am on my way Ummina yanzu zaki ganni"Tambayarka nake ina kaje? Tafada cikin kakkausan murya.

     Rausayar dakai yayi kafin yace *MAIDUGURI* naje Ummi Baffa keson ganina,naleka kafin intafi na tarar baki...kit yaji ta yanke wayan bayan tajamai wani dogon tsaki.sauke wayar yayi daga kunnansa yana sakin mirmishin dayafi kama da kuka ciwo,komawa yayi yasake jingina da kujeran motan hannunsa bisa kansa yana shafawa.."har yaushe ne Ummi zata daina Nunama Dangin mahaifinsa tsana? har yaushene Ummi zata bar Abunda ya wuce shekara da shekaru..yatsani halin Ummi indai na Riko ne...

  *****   *****   ******

Fuskarta kawai na kallah babu alamar fara"a atare da ita..huci kawai take saki kafin tafara mgana cikin Fushi da Hausanta wacce take chakule da larabci _*WLH SHETTIMA BAKA ISA BA,BAKA ISA KA RABANI DA DANA GUDAN JININA BA,WANDA NASHA WAHALAR RENONSA TUN YANA KARAMI HAR YAKAWO IYANZU...TUNDA KUKA NUNAMIN TSANA NIKUMA NAYI ALQAWARIN DUK WANI ABU DAYA DANGANCENI SAI NA RABAKU DASHI..CIKI KUWA HARDA DAN NAKU..MU"AZZAM NAWANE NIKADAI*_ Takareshe fada lokaci daya da fashewa da mtsananciyan kuka mai cin rai da bakinciki kafin tashuru takalmi tafara haura Step tana kuka kamar karamar yarinya...karime dake gefe fadi kawai take Allah huci ran hajiya,yan aikinta dake bangaren kichen Uwale da lami suma fitowa sukayi hannu dafe da kirji Suna sallallami..Domin inda sabo sun saba ganin hajiya Lokaci bayan lokaci tana shiga wannan halin wanda ko dan lelen nata bai isa ya sauko da ita,Ba sai don kashin kanta ta hakura ta Sauko..

jugum jugum Sukayi kowacce hannu dafe da kunci Suna zaune afalon Suna kallon agogo daidai lokacin da agogo yabuga karfe 10:00pm nadare daidai lokacin kuma sukaji hon lokaci daya da karar Sanda Sani maigadi yabude get din gidan sunajin haka Suka mimmike kansu akasa cikin lokaci kadan Sukaji yana gaisawa da Sauran ma"aikatan dake aiki a haraban gidan
kafin ya Nufo kofar dazata sadashi da babban falon gidan.

    yana gaba Ushe na binsa abaya dauke da yar jakar briefcase dinsa Da Siririyar muryansa yayi sallama bayan ya bayyana akaton falon dayaji kayan alatu na more rayuwa,Kamshin Turaransa Na MAN Yafara bayyana kurama kofar falon nayi daidai lokacin daya bayyana.. _Wow nafurta lokacin danayi arba dawani dogon mutum mai dogon zati irinsu ne ake kira giant ko'ina na jikinsa amurdene hatta da musles dinsa gasunan awaje..Kirjinsa nada fadi kamar ingarman zaki,choculate colour ne shiba baki ba kuma baza"a kirashi fari ba..Kallo farko zakamai kazata yahada iri da yan maroco, idanunsa daradarane masu dauke da zarazaran gashin ido..Yanada cikar gira kamar wani mace wanda tama kusa hadewa,hancinsa kuwa har baka yake tareda karamin bakinsa wanda ke zagaye da bakin sajensa wanda yahadu yayi masa kyau..Leben nasa yana fitar da maiko kamar wanda yashafa lipstick kallo daya zakamai kasan yahada Ruwa biyu wato kanuri da Larabawa .Yana sanyene dawasu ubansu American Suit black nd white wuyansa matse tektie wand ya matse wuyansa dashi hannunsa Sanye cikin wani agogon azurfa na maza,kafarsa sanye cikin Rufaffan takalmi na fatar Damisa..Sumar kansa tayi kwance kamar wanda keshafamata shampoo,kallo daya zaka masa kafahimci tsatsan jarumtarsa da kamewarsa ayadda yake Tafiya zaka fahimci tsantsan miskilancinsa wanda ko ayadda yameTafiyansa da yadda yake mganarsa zaka fahimci haka *BARRISTER IBRAHIM MUHAMMED MOODU KENEN WANDA MUTANE SUKA FI SANI DA BARRISTER MU"AZZAM MOODU* Babba ma"aikaci ne akotun Nageria Suprame Hight court Abuja,Akallah ashekarun haihuwa zai kai 30 Aduniya.._Ganinsu karime tsatstsaye yasan za"a Rina dama,sannu da zuwa suka hau jeramai atare,daga musu hannu kawai yayi yanufi upstair din cikin kuzari yake haura Step fuskarsa na bayyana tsantsan Damuwa.

  **** *****   *****  *****

Yakura takalli Shettima tana fadin"Haba Shettima ashe yanzu baka Tsausayin marainiyar Allah *ZANIIRAH* Tana da Rauni bazamu taimakamata mu tallafi Rauninta ba,kamanta Abunda ke Tsakaninmu Da *HAJIYA SUHAIMA* karka manta ko danta badon Sonranta yake rabarmu ba,kamanta *ZANIIRAH* Diyar * FADI* ne mekake shirin aikatawa"Tafada idanunta sunchanza launi cikin zubda kwallah tacigaba da cewa' *ZANIIRAH* Jininkace Shettima kuma Jinin *FADI* ne..Suhaima bazata taba kaunarku ba har Abada"Tafada tana ficewa daga dakin bayan kuka yaci karfinta.

   Baffa Shettima na zaune inda yakura tafice ta barsa kansa na duke ne,na tsawon lokaci yana dagowa Abun mamaki hawayene ke Zubowa bisa kuncinsa suna zuba har bisa farin gemunsa..Kofa yakurama ido wasu lokata acham baya suna zuwamai Daki daki kamar yanzu komai ke faruwa.

_*TOPHA..YAKUKAGA SALON..ZAI TAFI DA SALON TUNANINKU HARDANA ZUCIYARKU? KOKUWA ZAI TAFINE KAN YADDA KUKA HIMMATU DA ZUWAN LBRIN?...KU BIYO JANAF..CIKIN LBRIN..UWAR MIJINA...! UWAR MIJINA...! UWAR MIJINA...!*_

    *COMING SOON....!COMING SOON...!COMING SOON......!*

*NO DATE*
*NO TIME*
*NO PROMISE*

*KUYI MIRMISHI KAWAI DUK SANDA KUKA TSINCESA CIKIN WAYARKU*

_*Kifara Daga farko Sa"ace..🤘ki yankeshi daga tsakiya Haushi ne🤘Barinki abaya kuma Rashin Nasara ce🤘Samun sa Akan lokaci kuwa BAIWA CE*_🤘







*#One Love#*
*#Janaf fan"s#*
*#Intelligent writer"s#*
*#HAFMEELART#*
*#Mallakar janaf ce#*
*#UWAR MIJINA..!(A Very touch one)#*

UWAR MIJINAHWhere stories live. Discover now