UWAR MIJINA..

2.1K 79 3
                                    

*🌺UWAR MIJINA..!*🌺
   _(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)_

          *Alkalamin:JANAF*
          *wattpad:Janafnancy*

*Dedicated to my blood Sisters JANAF*

*Intelligent writer's Asso*✏

*NOT EDITED*⚒

           *NO 11*

     """Har suka iso Abuja Airport, Zahirah na makale jikin yakura tana kuka itako,kamar ranta zai fita,tun yakura na lallashinta har takoma ta kyaleta domin bazata hanata takoka ba,kodon dacin dake ranta yafita.

     Jirgin na saukesu Mu"azzam yayi ma Ushe waya kan yazo yadaukesu,Bayan kuma yakira hajiya yafadamata isowarsu,Dr Abduljabar da shima yayi ma direban sa waya kan yazo ya daukesa,cikin lokaci kadan suka kariso,motar mu"azzam ita Aka saka zahirah da yan"uwanta sukuma suka shiga ta Dr.Abduljabar.

        Lokacin da Ushe ya dannah hon abakin wani babban get mai kyau da tsari baki da hanci su yakura suka saki suna kallon tsaruwa kai tun ma da suka doso anguwan,suka saki baki suna bin ko"ina da kallo lalle Duk wanda baizo Abuja ba yabar kallo,haka yakura da mahgana keta fada aransu.

      Sani maigadi jikinsa na rawa ya wangale get motocin guda biyu masu kyau suka sulala cikin gidan,motocin na tsaya a parking space sai ga Su zulaika dasu karime sun fito suna rangwada guda suna ma amarya lale da zuwa hajiya baraka ce agaba taci adonta cikin wani dakakken leshi,mai kyau da tsari,Ita da kanta ta bude ma Su Zahirah mota tana fadin"Brka da zuwa Amarya ta ango"Tafada farinciki ya nuna har bisa Fuskanta.

   mahgana tafara fitowa kana yakura tafito rumgume da zahirah wacce ta sunne kanta tana digan hawaye Rikota hajiya tayi tana fadin"Allah sarki Zahirah Allah yasa a kulla alheri"Tafada tana rumgumeta,Dariya yakura tayi tana fadin"hajiya baraka ashe rai kan ga rai"Hajiya baraka tariko hannun yakura tana fadin"Uhum kedai bari yakura ya bayan Rabuwa kuma"yakura ta amsa da "Sai alheri hajiya ina Suhaima.

  "Hajiya tace"Tana daga ciki mu karisa "Tafada tana musu jagora ammh zahira na rumgome ajikinta su zulaika na gaba suna jera guda ta ko"ina,suko su Mu'azzam daganan, sukayi sallama da Dr.Abduljabar da Brr.Barrau suka tafi amotar Dr din Shi da Shureim da Dr.Haruna ne suka take ma su hajiya baya.

   Ummi dake kwance, kan gado kowani dakika na zuciyarta bugawa takeyi,tana ji sanda hajiya kefadama zulaika cewa amarya ta iso..Gabanta ya amsa lokaci daya jikinta ya dauki rawa hawayen takaichi da bakin ciki suka zubomata ta sanya hannu ta share mata,bata gama tunanin mafita ba ,taji bude get da karan diran motoci,bata kara tsinkewa da al"amarin ba sai da taji gida ya kaure da ihu,da gudan zuwan amarya Ummi dake zaune tayi saurin mikewa Jiri na neman kadata ammh ina zuciyarta suya take tana fadin"Yanzu ke suhaima Diyar fadi zaki bari tashigo miki gida.ehe..Kinmanta yadda suka taru suka ruguza miki burinki da rayuwarki gabadaya"Jin abunda zuciyarta ke sakamata ne yasa ta nufo kofa da niyyar fita jirin daya debeta ne yasa tayi saurin dafe bango lokaci daya dadafe kanta nan ta sulale tana kuka mai cin rai tana fadin"Allah ya isa tsakanina dakai Shettima kadade kana cutar da zuciyata *WLH NI SUHAIMA NAYI ALQAWARIN DAUKAN FANSA AKAN KA,TAKUMA HANYAR DAKA,BIYOMIN,ZAN RAMA"Tana fadi tana dukan kanta da hannuwanta tana kuka kamar wata zararra.

     Suna zuwa kofar shiga babban falon hajiya tayi ma zahirah rada akunni tana fadin"Ki shiga da kafar dama,zahirah bayan kinyi addu'an fatan zaman lafiya agareki"Jin haka yasa tafara karanto addu"a tana kuka kafin su shiga falon wanda daman babban falo ne mai girma da tsari wanda yake dauke da kujerun royal chair har seti biyu,golden colour wanda sukayi ma falon kwanya bayanshi sai wani kafet mai kama da auduga wanda da kasanya kafa zakaji kafarka Ta, lume aciki,sai wani tafkeken Tibin bango daya kusa cinye rabin falon daga yamma kuma wani babban dining area ne wanda yaji wani ubansu Dining table wanda akallah mutane fin goma zasu kammallu agun.

UWAR MIJINAHWhere stories live. Discover now