UWAR MIJINA..!

2K 70 3
                                    

_*INTELLIGENT WRITERS ASSO*🖊_

🌺 *UWAR MIJINAH..!*🌺
        _(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)_

       *ALKALAMIN:JANAF*💕
        *WATTPAD:JANAFNANCY*

*DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF*

*NOT EDITED*⚒

                       *NO9*

    """"Basu isa ba sai gabda la"asar Shureim, Mu"azzam kawai yakira yafada musu lambar dakin da Sunan Asibitin,kai tsaye chan Suka Nufa,Sai da Ummi tagansu kwatsam lokacin tana zaune bisa gadon ancireta mata karin Ruwa tayi nisa cikin Tunani sai jin Muryan Hajiya taji tana fadin.

   "Suhaima wannan wani irin sakarci ne naji kin aikata"Cikin Firgita Ummi tadawo daga tunanin Tilon danta ganin Hajiya tsaye bisa kanta Shureim na gefe yasa tace cikin mamaki"Yaya.." yaushe agari kuma"tafada tana kakaro mirmishi Balla mata harara Hajiya tayi kafin tace"Kul karki kara cemin yaya Tunda baki daukeni da daraja ba,sau nawa zan Fadamiki Suhaima kidinga barin yaron nan, ya shiga cikin Danginshi,ke baki mantuwa kuma baki yafiya wani irin zuciyane dake da bazaki gane yanzu kinfi karfinsu ba ehe'"Tafada ranta bace Ummi ta kalli Hajiya kafin tayi mirmishin Takaichi tace"To yaya ki zauna kiji mana,kinsan mezasu min kuwa Mu"azzam fa suke neman Rabani dashi"tafada cikin zubar hawaye.

    Dagamata hannu hajiya tayi kan tace"Bazan zauna ba,domin bashi nazo yi ba,nazo ne namiki fada ki chanza Tunani saboda Abunda kika aikata ko a addininki bashi da kyau,Wayace zai Rabaki da Mu"azzam danki ne fa,wanda kika dauki cikinsa wata tara kikazo kika sha wahalan Nakuda,bayan kin Haifesa kika sha wahalan Renonsa har ya kawo iyanzu,kina tsammanin ko butulu ne shi zai manta dake? balle Yaron iya biyayyah yana miki sujuda ne kawai baya miki shin bazaki godema Allah ba..,Karki manta akwai iyayan da ko mutuwa zasu yi wlh basu isa su hana ya"yan su abunda sukayi niyyah ba,shinke baki bambamta dasu ba,saboda sonki da yake yasa baya son bacin ranki, yakasa fadamiki sai dai shi yayi ta zama da damuwa bisa ransa,so kike watara zuciyarshi ta buga saboda zafafan kalamanki akanshi.."Hajiya tafada tana dakatawa saboda tagaji da tsayuwa( da dai kicii gaba da tsayuwan waya gayamaki borno gabas take😂)

  Wuri ta nema ta zauna tana kallon Ummi dake kuka Shureim kuwa hajiya nafara fadanta yafice..Riko hannunta hajiya tayi tana fadin"Don Allah don Annabi Suhaima kibar Mu"azzam yayi Auren karfa ki manta ba mugun abu bane,Sunnar ma"aiki ne fa zasu dambaka,kuma in baki manta ba yanzu shettima yaga ishara da halin Rayuwa ke din dai da suka tsana, kece sanyin idanuwansu saboda keki ka haifanmusu dan" daya zama garkuwa garesu'"takareshe fada tana kallonta.

  Ummi dai kuka take bilqqi da gaskiya Kafin tadago tana kallon hajiya ta furta cikin kuka"yaya diyar FADI ce fa,Kin manta yadda Fadi tayi sanadiyar wargaza farincikina  duk da burina na zama da moodu har karshen Rayuwata"Takareshe fada cike da gunjin kuka,Mirmishi hajiya tayi kafin takara rike hannunta Tace"To Saime,Ita Fadin tana raye ne? ehe..Ai Allah kenan wanda ka raina shi zai maka rana wata rana"Tafada tana kallonta shuru Ummi Tayi tana kukan ta Hajiya sai bata kara mata mgana ta kyaleta tayi kukan nata.

     Mikewa tayi tana gyara mayafinta kan tace"Kinga in har baki ji mganata ba wlh tallahi Shi kanshi dan "Dakike Tutiya dashi watarana ke da hannunki zaki kasheshi"Da sauri Ummi Tadago tana kallon, hajiya idanunta jajur ta furta murya adashe"Ni Hajiya..Zan..Zan kashe mu"azzam"Gyada mata kai tayi kan tace'Kwarai indai baki janye kalamanki na bakison ganinsa ba,kuma baki sama auren albarka ba, Shi zai jawo ki Sakamai damuwa aranshi har yayi sanadiyar mutuwarsa kamar yadda Fadi da shettima suka kashe moodu da Zaluncinsu"Kallonta Ummi keyi cikin nazari kafin tayi mgana Hajiya ta rigata da cewa"Karki ce komai kawai kiyi Fatan alheri..Kifara shiri Sati mai zuwa za"a daura aure kuma yataho da matarsa,ki Natsu kuma kiyi aiki da hankalinki kuma ko bakomai yar"uwansa ne"Hajiya tafada tana tafiya kafin takara cewa"Indai na isa dake..Kada naji wata mgana kuma,ki fadama Mu"azzam amincewarki ko hankalinsa ya kwanta,Ni na wuce daman Abunda ya kawoni kenan"Hajiya tafada tana kokarin Ficewa.

UWAR MIJINAHOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz