UWAR MIJINAH..

2K 86 1
                                    

_*INTELLIGENT WRITERS ASSO*🖊_

🌺 *UWAR MIJINAH..!*🌺
        _(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri, Tareda biyayyah mai Tsanani)_

       *ALKALAMIN:JANAF*💕
        *WATTPAD:JANAFNANCY*

*DEDICATED To my BLOOD Sisters JANAF*

   
_*Assalamu Alaikum janaf fans,ya kuke, hop kuna cikin koshin lafiya,kamar yadda nake..Afuwan plz game da yadda na dinga comfused dinku,Akan Sunan ZAHIIRA..Wani Wajen sai na dinga saka ZANIIRA,Afuwan don Allah, wlh dauka nake sunan duk dayane😂, but by Now zamu cigaba da amfani da ZAHIIRA..Tanque so much masoyana, da gyaran ku gareni,hakan ya nunamin kuna biye dani..One luv*_💖

   *NO.6*

    """Kamar amafarki yake jiyo kiran sallah a masallacin dake kusa dasu, cikin mutuwar jiki,da gajiya ya farka,mika yafarayi kan ya sauke kafafunsa akasa wa"inda sukayi masa Nauyi sakamakon kwana atakure,Baiyi mamakin ganinsa kwance kan kujeran falon ba ma"ana anan yakwana bargon Ummi ne dake gefensa ne yabashi mamaki,gefe daya kuma sai ya murmusa daya tuna tabbas Ummi ce ta sauko tazo tayafamai,dan cije lips dinshi yayi kafin ya mike,ya tattara wayoyinsa ya wuce zuwa shashensa wanda ke kasab daNa Ummi domin dauro alwala.






  Agurguje yayi alwala yafice zuwa massallaci domin har an tada sallar..Bayan an sallame sallan saboda barcin dake cin idonsa ko Wa"azin da"ake bai tsaya Sauraraba,Wanda baya wucesa dawowa yayi gida, ya shige dakinsa mai kama da aljannah Duniya babu tarkace adakin daga wardrope dinsa,wanda takusa cinye rabin dakin sai madubi da gado sai kafet...gabadaya dakin blue ne komai da komai,komai dai cikin Tsari.





  Cikin mutuwar jiki yafada gadon dayaji lafiyayyan zanin gado ya baje,ya cigaba da barcinsa wanda ya daukesa mai Nauyi kuwa.


   Ummi kuwa tana Shiga daki kan gado tafada tacigaba da kukanta kamar karamar yarinya,tanaji komai har sanda mu"azzam,Ya shigo yazo yana mata magiya..Sai datagama mai isanta kana ta shiga bayi ta wanke fuskarta tayi alwala tazo tayi shafa"i da wuturi kana ta sauko tana zuwa taci karo Da mu"azzam kwance barcin gajiya ya kwashesa tadade tsaye tana kallon fuskar tilon dan nata,ganin tayi ya takure gu daya alamar Sanyi yakeji sai ta kashemai Ac din kafin takoma bedroom tadauko mai blanket tazo ta rufamai bayan ta shafa mai addu"a tasani saboda ita yazonan ya kwanta shafa kanshi tayi kafin tabashi Sumba,komawa sama tayi Ranta namata kuna na yarda tayi sake Shettima na neman Rabata da tilon danta.





***  ****  *****

   Cikin barci yaji sautin kiran wayansa cike Da haushi mu"azzam ya lalubo wayar akasan filon dayake kwance kasheta yake da niyar yi ammh sunan daya gani ne yasakashi Saurin picking" *DAN UWA* ya furta cikin muryan barci Daga chan bangaren Dr Shureim yace"How far Dan"uwa"Cikin kasala Mu"azzam yace"Am not Fine wlh"Yafada cikin damuwa.




Saurin Ture Zulaika Shureim yayi wacce ke kokarin dauramai Nektie yana Fadin"Wht wrong dan"uwa..? yafada cikin tashin hankali "Tsaki mu"azzam yaja mtseewww..."Kafin ya mirgina bisa gadon yana fadin"bana Fadamaka zani maid jiya ba",Shureim ya amsa da "yes.Wht hppend" mu"azzam yace" wlh baffa ya ballomin ruwa dan"uwa..Wai Diyar inna Fadi data mutu ta bari yabani na Aura'"




   "Kutumar ubanchan.."Shureim yace lokaci daya da dafe baki wanda sai Da Zulaika wacce ke kokarin gogemai takalmin dazai sa ta waigo cikin mamaki don bata saba jin irin wannan ashar din daga bakin mijin nata ba,cikin Rawan baki shureim yace'"Ka amsa Mu"azzam..?"Yafada cikin rawan murya.





  Ajiyar zuciya Mu"azzam ya saki kan yace"I hv no option dan"uwa.."Yafada cikin muryan karaya,jinjina kai Shureim yayi kan yace"Ummi fa.."Shuru mu"azzam yayi kan yace"Ummi batasan ma da zence ba, kawai na tafiyata maid ne daban gayamata ba,tahau koke koke, to inaga taji babban Abun..Kila tsinemin zatayi wlh"Yafada kamar zaiyi kuka.


UWAR MIJINAHWhere stories live. Discover now