UWAR MIJINA

1.9K 72 0
                                    

_*INTELLIGENT WRITERS ASSO*_✏

    🌺 *UWAR MIJINAH..*🌺
          _(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri tareda biyayyah mai tsanani)_

      *ALKALAMIN:JANAF*💖
      *WATTPAD:JANAFNANCY*

*Dedicated to my BLOOD Sisters JANAF*

*NO.4*

_*Kasani cewa himma da hakuri da dogaro ga Allah,Sune ginshikin samun Nasara A rayuwa..Assalamu Alaikum janaf*_✌

*NOT EDITED*⚒

""""""Moodu bai damu da yarda suke cemai yafice yabasu guri ba..,Illa fara labarta musu lbrin Abunda yafaru Tunbayan Barinsa gida da Aurensa da Suhaima har zuwa yau dinan yakareshe da cewa"Ku yarda dani Wlh ko da kwana daya bantaba mancewa daku ba kuna raina..Aurena da Suhaima kuma haka Allah ya kaddaramin bani da yarda zanyi,kuyiwa girman Allah kuyafeman dan"uwanku"Yafada lokaci daya shima ya kice da kuka.

Ammh ina Shettima da Fadi basu tsaya sauraransa ba illa ma suna kara Umartansa daya bar musu gida basu bukatarsa ahalin yanzu.

    ""moodu kukan yake kuka maicin rai da shesshekan zuciya Shettima kuwa Da fadi mganganu suketa jefan dan"uwansu dashi kamar basusan daga inda yafito suna kuma cewa yafita yabarmusu gida..

  Tuni Suhaima ta rude duk da batajin yaren dasuke fadi ammh ganin yadda moodu ke kuka kuma shikanshi khamis din talura da yadda hankalinsa ke tashe cikin harshen larabci take tambayanshi meke faruwa? kan yasamu zarafin bata amsa Fadi ta bankamata harara lokaci daya dacewa"Shegiya mara Asali"Wanda sai da moodu ya tsaigata da kukan dayake yadago yana kallonta..Khamis kuwa yaji kalman ammah bai fahimci ma"anarta ba tukun tunda hausan daya iya gurin moodu bata da wani yawa.

  Suhaima bata saba ganin tashin hankali ba balle dataga yadda fadi ke hararanta sai ta rude tanufi moodu cikin tashin hankali tana jansa tana mgana cikin harshen larabci wai yatashi yatafi..Shi yakara bakantama Shettima da fadi rai suka umarci moodu yayi gaggawan barin musu gida basu bukatarsa..Khamis yana ta kokarin basu hakuri ammh sunki sauraransa..Yakura kuwa na kofar dakin tana sharan hawaye domin suhaima ce da moodu ke bata tsausayi.

  Zannah moodu ne ya tsawatar yana daga kwance cikin wani hali da karfi hali yace"Haba shettima Dan"uwanku ne fa moodu wanda kuka fito ciki daya...Nasani moodu bazai barmu haka kurum ba ku yarda da dalilinsa kubarsa yazauna cikin yan"uwansa na rokeku"Yafada tari ya sarkeshi moodu ne yayi saurin isa kusa dashi ya tarairayosa ya aza kansa bisa cinyarsa shettima ya dauko ruwa yana basa.

  Mganar da zannah yayi shiya dakatar da Shettima da Fadi basu da yarda zasuyi ammh fadi ita tunda tadora ido kan Suhaima taji ta tsaneta saboda itafa harga Allah kanwar mijinta tayima alqawarin yayan nata( Kiji karfin hali)da sun hada ido sai ta bankamata harara.

   Tuni labarin dawowar Moodu tacika gari yan"uwa da abbakan arziki sai tururuwan zuwa ganinsa ake..Anata lbrin yazo da mata balarabiya kowa sai zuwa ganinsa ake shida suhaima masu zuwa don Allah da masu zuwa don gulma..Tuni labari ya yahadu agari ashe moodu ba bacewa yayi ba yana chan yana hutawanshi harda ma balarabiya yazo..Chaichai..Abu yacika gari..kowa da Abunda yake fadi.

   Wuni sukayi da baki shiyasa basu kara wani tattaunawa ba,dare nayi kunyar shettima yasa yabar Suhaima gun yakura shikuma yatafi yakama ma khamis otel yakwana yaso yadawo ammh damuwar dayake ciki tahanasq dawowa kuka reras yayita ma khamis yana bashi hakuri..Koda gari ya waye suka dawo ko mgana shettima baimai ba saboda yatafi ya kwana da khamis..Itakuwa suhaima taga rayuwa domin bayan Tafiyan moodu haka Fadi ta sakata gaba da zagi da cin mutumci duk da batajin metake cewa ammh tasan cewa komeye bamai Dadi bane.

   Sai da yakura tamata mgana itama din bata ragama mata sai da dai tabar gidan aka samu sa"ida..Duk da yakura batajin larabci da hannu taita bawa suhaima hakuri wacce ta kwana kuka sai yanzu taji nadamar yarda da Auren moodu har ta yarda ta biyoshi nigeria ammh ta yanke shawarar khamis zata bi takoma kasarta ta haihu..Yakura ita taita dawainiya Da suhaima taneman mata makwanci takawomata abinci duk da bata mgana sai dai ta kalleta kawai tamata murmishi alamun tagode sosai.

UWAR MIJINAHWhere stories live. Discover now