UWAR MIJINA

1.8K 88 3
                                    

_*INTELLIGENT WRITERS ASSO*_✏

    🌺 *UWAR MIJINAH..*🌺
          _(Soyayyah,sadaukarwa,hakuri tareda biyayyah mai tsanani)_

      *ALKALAMIN:JANAF*💖
      *WATTPAD:JANAFNANCY*

*Dedicated to my BLOOD Sisters JANAF*

*NO.3*

   *WASU SHEKARU ACHAN BAYA*

   """ *MUHAMMED MOODU* Shine asalin sunan mahaifinsu,wanda Asalin iyayansu da kakaninsu yan Asalin haifaffun maidugurinne awani yanki da"ake cema *USIFARI* zama ne dakuma yaya da jikoki yasa suka koma cikin garin maiduguri da zama...cikakkun bare barine gaba da baya.

  
muhammed Moodu yakasance babban malami ne mai ilimi da addini wanda jama"a ke girmamawa,shiyasa kowa ke kiransa *ZANNAH MOODU* matar Aurensa Daya Ummu kursum wacce sukayi Auren Saurayi Da budurwa Ya"yansu uku aduniya kachal shettima ne babba sai Fadima( Fadi) kenan sai Auta Muhammed moodu wanda yaci sunan zannah.

     zannah moodu yakasance bayan malantansa yana kiwon Dabbobi kama daga shanu awakai farare da jajaye..,kaji zabbi kai komai fa yana kiwo,gidan Gona garesa na mussaman inda yake gudanar da kasuwancinsa,..Yakasance yanada almajirai daga garuruwa da dama yana karantarsu dasu..Cikin yayansa kaf babu wanda bai bawa ilimin addini ba daidai gwargwardo,Shettima baida Ra"ayin Karatun boko ko kadan shiyasa ya tsaya gana addinin Fadi kuma dama macece kuma zannah baida burin sanya diyansa mace makarantan boko..Moodu shine yafita zakka tun tasowarshi yaro ne mai kaifin basira komai aka koyamai yana daukeshi lokaci daya.,Yakasance mutum ne mai hakuri da kawaichi ko yana bukatar Abu bai iya fadi sai dai wanda ke tare dashi ya fahimta yayi sauka tun yana shekara bakwai Aduniya sauran littafai yake bita..Kullum safiya yana fitowa kofar gidansu inda wasu yara ke wucewa zuwa wata mkaranta boko ta gwannati.Abun na burgesa yana sha"awan Shima ya tsinci kansa cikin karatun na boko..Tun Zannah bai fahimta ba har ya Fahimta shikuma gashi Allah ya jarrbceshi da kaunar Dan nasa moodu shiyasa batare da shawara dakowa ba yasanya moodu mktantan prmary ta boko wanda hakan yakawo Rudani matuka ko Shettima bai so asanya shi ba ammh zannah moodu ya yi biris dasu yacikama Dansa burinsa..
   

  Cikin ikon Allah Moodu yakammallah Prmary sa cikin Nasara wanda kafin gamawarsa sai da yayi suna saboda kokarinsa da hazakarsa malamansu har gida suka zo gun zannah moodu suna fadamai irin baiwar Da Allah yayi ma yaronsa na kokari da hazaka hakan shiyakarama Zannah karfin gwiwan Sanya Moodu awata mkaranta maisuna *IMMA MALIK* mkarantace na ya"yan masu Dashi tana hade ne Arabi da boko..Cikin kudiran Allah Karatu yadinga Tafiya Da Nasara hazaka Moodu tawuce duk inda ake tunani, suma malaman makrantan da kansu sukazo gida suka ba Zannah Moodu shawaran kai moodu madina domin yahada degree sa na farko achan..Haka ko akayi da taimakon malaman mkarantan bayan kammallah jarabawan karshe dasu moodu Sukayi kuma Alhamdulillah yafito da sakamako maikyau..Zannah ya saida rabin Dabbobinsa yahada kudi akayi ma Moodu cuku cuku yasamu gurbin karatu ajami"ar Madina.

      Lokacin Da zai Tafi yayi kuka kamar me saboda baison Rabuwa da gida,alokacin yana Dan shekara ashirin da biyu aduniya..Shettima Dana da ashirin da bakwai fadi kuma tanada wajen ashirin da hudu don anyi mata Aure da almajirin Zannah moodu *ABUBAKAR BAHGANA* Wato Abubakar Babakarami kenan Shima dan asalin maidugurin ne yayi zama gidansu gun zannah Moodu to shi ya bawa Aurenta wajen shekaru biyar kenan ammh ko batan wata bata taba yi ba.

    

************

  shekara Biyar Moodu yayi Ya kammalah degree dinsa na farko,saboda hazakarsa dakuma basirarsa yasa jami"ar ta rikesu shida wani *KHAMIS* khamis yakasance haifafan sudan ne wanda shima karatu yakawoshi har suka hadu Da moodu to ganin yadda yakeda kokari ga fanni karatu shima khamis din badai kwanya ba yasa suka kulla abota tun Moodu bai saki jiki dashi ba hardai yasaki khamis dan manyan mutane don iyayansa suna da hali matuka...Sun amshi tayin mkarantan sunfara koyarwa da taimakon Khamis moodu ya amince saboda yaso komawa gida saboda ko wanda baffansa ke aikowa shekara biyu kenan babu lbarinsa..khamis ya matsamai ya amshi aikin,ganin sunfara koyarwa khamis yakara tursasama,moodu suka dora digirinsu na biyu,suna karatu suna koyarwa ammh duk da haka kewan gida da tunanin halin da ahalinsa ke ciki basu barsa ba,duk kuma albashinsa da Abunda ya samu ba ya iya ci..Yana tarawa ne domin iyayansa da yan"uwansa.

UWAR MIJINAHWhere stories live. Discover now