💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
JIDDARH*qala rasulillahi sallallahu alaihi wasallam:*
*al Muslimu a khul Muslim LA yazlimuhu wala yakzulu wala yakkiru**Allah's messenger (s. a. w) said a Muslim is a Muslim's brother he neither oppresses him does he humiliate him nor does he look down upon him*
Page 13
Jikinta Yayi mugu mugun tsanyi ,ganin yanayin da yayi .
Lokacin da kalmar sonshi ta fito daga bakinta.. Take kirjinta yasoma bugawa da sauri da sauri ta tsura masa idanunta Tana kallonsa kmr zata cinyeshi gabadaya ji tayi Duk wata saliva dake cikin bakinta ya dauke... Da kyar ta sake janyo wata Jarumta da karfin Hali Ta sanyawa jikinta sannan kirjinta na bugawa da muryarta gurin sake cewa baka sona ko abdulkabir... ...ya sake girgiza still yana mamakinta.
Amman fa ransa amatukar bace yake bai taba tunanin zata iya kallon tsabar idanunshi tace wai tana sonshi ba dan hk kanshi ranshi a jagule ,muryarsa adake yace bance bana sonki ba sai dai da akwai wace nike so acikin zuciyarta yakarasa fadar hk yana tsare gira sosai Dan kar ma takawo masa raini. yayinda shi kawai ya fada mata hk ne Dan haushin databashi ba dan yana da Wace yake so ba.
Still mamakinta yacigaba dayi ta za'ace Mace daita tasoma furtawa nmj Tana sonshi Mace da akasani da daraja da kamun kai....Nashiga uku ni Zainab ta dafe daidai saitin zuciyarta tana tsareshi da idanunwanta cike da tashin hknl Ta sake bude bakinta baka sona kenan abdulkabir?
Ya yatsina fuska yana sake tsare gira bance bana sonki ba sai dai akwai wace take cikin zuciyata yana gama fadar hk ya mike tsaye ya bar parlour Zeey ta koma Kasa ta zauna dirshsn tana kuka.wayyohhly Allah meke shirin faruwa dani?
Wacece wannan Data min shigar sauri?
Abdulkabir karkamin hk wallahi ina matsanancin sonka,rasaka daidai yake da rasa rayuwata. Wayyohhly Allah sai da
tayi kuka me isarta ganin babu Mai rarrashinta yasa Ta tashi daga cikin parlour 'n Ta nufi dakin baccinsu ta fada kan gado tare da Janyo pillow ta daura kanta babu abinda yake fita cikin idanunta sai hawaye.
Tayi matukar bakinciki faruwar hk domin bata taba tunanin AK zai Ki amincewa da soyauyarta ba.
ganin yadda yake kuladaita da Duk wani lamarinta uwa uba shakuwar dake tsakanInsu GA kulawa ta musamman da sukewa juna.Da dadaddare misalin karfe takwas AK yayi shirinsa cikkn wasu hadaddun kananan kaya masu matukar Kyau da daukar hankali sai kamshi ne ke tashi akowani shashi na jikinsa gashin kan nan nashi baki yasha gyara sai sheki yake .
ya nufi hotel dinsu onye ahankali yake takunsa har ya Iso bakin kofarta batare da neman izini ba yashiga dakin, byn ya daga labule onye tayi saurin tasowa cikin tafiya sauri sauri gudu gudu tashige jikinsa ta kamkameshi tana shakar daddaden kamshi turaren jikinsa, shima rungumeta yayi tsam ajikinsa yana shafa bayanta daga bisani ta dan jaye daga jikinsa tare da sanya hannuwanta tana gyara masa kwalar rigarsa hade da Yi masa wasu tsadaddun kalaman soyayya... AK yasanya hannuwansa duka ya sake matso daita jikinsa yana gyara mata gashin kanta baya... Cak ya dauketa yana jujjuyawa daita a tsakar dakin yana fadin Irin kyawun datayi sannan daga karshe ya direta akan katifa Suka shiga holewarsu..Ak ya dinga yiwa onye mgn cikin yanayin na rada acikin kunneta wai yaji dadin yadda ya same Ta jikinta yayi sauki nan fa onye ta narke tashiga zubawa AK shagwaba iri iri, shi km Duk ya rude hannushi na kan manya bombom dinta yana shafawa tare da lumshe idanun.
alakar dake tsakanin AK da Zeey yanzu ta wargaje domin kuwa Zeey ta daina kulashi Duk yadda yaso alakarsu taci gaba kmr da Amman taki Duk da ciwon sonshi dake cin zuciyarta.
ammi ta lura da Zeey kwana biyu bata cikin walwalarta Dan hk Ta rutsata a dakinta byn tagama gyara mata dakin Ta zauna daf da Zeey dake shirin ficewa daga dakin, takira sunanta ,Zeey ta amsa tare da dawowa kusa da ammi ta tsaya da na'am ammi.
zauna Ta nuna mata kusa da ita Zeey ta zauna Kirjinta na tsananta bugawa.. Sautin muryar ammi Ta doki dodon kunneta wai me ke damunki cikin yan kwanankin nan na lura kina cikin damuwa? Zeey tayi murmushin karfin hali wanda yafi kuka ciwo da radadi sannan tace babu abinda ke damuna kwana biyu din nan dai ina jin jikina bana jin dadinsa.. Shine kika ja bakinki kika Shiru.. Yanzu idan ban tmyeki ba hk zakiyi ta zama da ciwo ajikinki ammi kiyi hkr In ji cewar Zeey shikenan sai Ki shirya anjima kije kiga doctor Zeey tace to ammi..

YOU ARE READING
SAI KA AURENI DOLE
Romancesai ka aureni dole all talk about betrayal of consent, love involves sacrifice, disagree with destiny, following witcraft.