37

779 22 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
      JIDDARH

*qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam la yadkulul jannata qathi'u*

*Allah messenger saw said :the person who off one's friendship will not admint janna*

page 37

shimfidadden titi ne kwance har zuwa bakin tafkeken get din makarantar ,wanda ke dauke da suna Hill City University tare da tambarin  makarantan daga sama.
  cikin harabar  makarantar shima titi ne kwance tare da wasu titi nan dake da hayan  kashi kashi wanda zai ka mutun kai tsaye duk inda yayi niyyar zuwa ,tare da entrances car park. gabadaya ilahirin harabar makarantar zagaye yake da  shuke shuke na korayen flowers ,wanda a kullun suke sake kawata yanayin  tsari makarantar   ta haka ne  kullun makaranta ke kara fitowa da kyau a idanun duniya. daga can bangaren yamma hostel din talibai ne jere .
  sorroding makarantar kuwa human beings ne kawai  ke kai kawo wasu akafa wasu a bike rides.
duk wani abin na cigaban rayuwa  akwai shi aciki wannan jami'a kama daga network shopping mall Bank's ,street  lights flag garden da sauransu jami'ar hill city, jami'a ce data tattara manyan malamai daga kasashe duniya har zuwa na nan cikin kasar Cotonou sannan jami'a ce data tattara ya'ya manyan attajirai zuwa kososhin gwamnati.
, zaune nake cikin  haddadiyar motata bak'a kirar camry alokacin  ina direving ina kan hanyata ta zuwa makarata. ahankali cikin dan hanzari nacigaba da diriving dina duk da kasancewa ba hk tsarin yanayin tukin kasarmu yake ba domin ba'agaraje ko sharara mugun gudu akan titi.
  nima ranar nayi hkn ne sakamakon kiran dana samu daga gurin aminiyata Ramlat akan na hanzarta shigowa da wuri an kawo mana sabon malamin turanci tun last week ,km yau shine zai soma bamu darasi.
abinda yasa bani da masaniya hk nayi kwana biyu banshigo makarantar ba ina can tare dasu yaya yusif a gida .
cikin hanzari na isa harabar makarantar kai tsaye inda dalibai suke ajiye motocinsu  na nufa na parka motata na fito a tsanake dalibai ne bila'addadi a harabar makarantar wasu zaune akan motocinsu yayinda wasu ke kokarin fitowa daga mota tmkr yadda nake kokarin fitowa daga cikin tawa motar zuwa cikin department dinmu  . fitowata ke da wuya idanun dalibai bila'addadi sukayi caaa akaina suna kallona wanda idan da sabo narigada na saba da wannan kallon .
sanye nake cikin daya daga cikin  bak'ar duguwar rigar da yayyuna suka yo min tsarabarta daga America doguwar riga ce har kasa me dagon hannu wace akayiwa ado da korayen duwatsu tundaga samanta har kasa hk bakin hannun rigar shi zagaye yake da duwatsu. nayi rolling kaina da mayafinta wanda ya fidda ainihin sahihin kyawun fuskata, flat bby shoe  sanye akafafuna suma bak'i sai yar madaidaiciyar jakata dana sakale a kwarin hannuna. yayinda tsintsiyar hannuna daure yake da agogon gold hk yatsan hanuna daya na hagu zoben zinari ne kwaya daya tal na manne idanuna da farin glass kasancewar ni dalibar likitanci ce.
wani irin sihirtaccen kamshi ne ke tashi a gbdy sansar jikina  alokacin babu wanda zai shaki kamshi turaren danake amfani dashi bai so ya sake shakarsa ba. hk zalika duk wanda ya sanya idanunasa akaina ba zai so dauke idanunsa ba ya dinga kallona kenan har sai na bacewa ganinsa .
ni kaina nasan ina da matsanancin kyau kyau km na kare magana. shiyasa wani lokacin bana bleming mutane akan yadda suke kallona duk da hkn baya daga cikin tsarina.
ahankali nasoma daga kafufuna ina tafiya a tsanake mutane gurin na sake cigaba da kallona har na isa department dinmu abin mamaki
duk wannan uwar saurin dana kwaso sai dana iske malamin turancin nan yarigani .
dan  har ya soma gabatar da darasi.
banyi hanzari shiga cikin ba naja na tsaya kasancewar nasan kowani sabon malami yana da salo tare da kaidarsa .
ina tsaye dalibai sukayita xuwa amman duk wanda yazo ya gani tsaye sai yaja ya tsaya . wasu na tmbyr tare da neman ba'asi ,yayinda wasu sukayi shr.
ni dai babu wanda na takawa acikin masu yin tmbyr nacigaba da tsayuwata rungume da hannuwana duka akirji.

SAI KA AURENI DOLEWhere stories live. Discover now