38

683 24 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
SAI KA AURENI DOLE
      💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

             ~NA~

*AYSHA  A BAGUDO*

~DEDICATED TO~
HAUWA A USMAN
      JIDDARH

*qala rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam :la yadkulul jannata bakhil*

*Allah 's messenger saw said : the miser will not admit paradise*

page 38

su ore tagani tsaye cirkocirko su uku  dukkaninsu  basa cikin natsuwarsu suna sanye cikin wando da riga.
tana ganin yanayinsu take taji wata irin mummunar faduwar gaba from know where .
suna ganinta suka soma sara mata tare da rige rigen mgn  .
tayi saurin dakatar dasu da hannunta tana kallonsu a dan tsorace sannan tace uhm mutun daya ta min bayani meke faruwa?
ore ce tasoma mgn a natse ol,ori yanxu baba alaye ya kirani yace nagaya miki yakira  number dinki sau ba adadi baki dauka ba .
yace nagaya miki ga  abdulkabir dinki ce tare da wata a sabon gidansa .
amman yace min ba wannan karuwar tasa bace wannan wata ce daban.
tsalle tayi ta dire agurin tana haki da numfarfashi tare da jijjiga jiki ......oh my God meyasa meyasa... yanzu irin rayuwar da abdulkabir ya zabawa kanshi kenan ta neman mata.. kmr bunsuru.....
tayi mgnr a kasan ranta .

a bayyane kuwa cewa tayi yanxu amanar soyayyar tawa zai ci wallahi bai isa ba sau duba zai canza wata yariyar sai dubu zan rabashi daita .
shi din kadarata ce ni ..ni kadai .
ta juya fuuuuu ta koma cikin dakin batare da tace dasu komai , inda tabar ummanta tsaye jingine da bango har yanxu tana nan agurin. jikinta yayi wani irin bala'i sanyi ganin yadda take kuka ..ahankali takarasa gareta ta Kamo hannuta  xuwa kan dan karamin madaidacin gadon uwar ta zaunar daita kiyi hkr umman su'ad kimin adduar bisa hatsari nayi ayyukan alkhari da abubuwa masu mahimmanci dayawa. tare da risking din rayuwata yauma zanyi  wani aikin alkhairi bisa hatsari ki taimaka kimin adduar samun narasara.. hawayen  umma take zubawar har lokacin takasa tsaidasu ta daura hannuta dake rawa bisa kan su'ad ta kasa furta mata komai adduar take son mata amman me zatace mata akan kudinrinta tunda tasan karshe daukar mgn zata fita yi .. ...
umma kimin adduar samun nasara naje na dawo batare da ansamu wata matsala ba.
ko me umma ta tuno yasa a fusace   tasoma mgn cikin kuka da bacin rai kowani irin aikin alkhari ne su'ad karkije.....
   bana son fitarki yau zuciyata bata amince da fitar koina yau ba ki taimakeni ki zauna tare dani ki canza wannan rayuwar da kikeyi kwata kwata bata dace dake ba .. ..
matsalata dake kenan umma rashin fahimta da ganiya da saurin daukar zafi akan abu, yanzu wannan ihun da fadan dakike  ne zai sa naki fita.
  kawai kimin addua kmr yadda nace ni na wuce ta mike ta fito daga cikin dakin uwar zuwa parlour umma  tabiyota da sauri tana ihun kiran sunanta. dan girman Allah umma karki biyoni ki taramin jama'ar unguwa wai meyye hk ne nace zanje na dawo agida ma zan kwana yau, tasanya kai tayi ficewar  gbdy wanda zuwa lokacin su ore sun fito waje zaman jiranta. ta bar ummanta agurin tana kuka wiwi.
   tana karasa fitowa daga part dinsu ta riske neighbor's  dinsu  masu hayar a gidansu su uku tsaye abakin pompo suna mgn  kasa kasa kinga alhalin yan'iska nan sunzo sun janwota .
tun safe fa uwar tasata adaki ta kasa ta tsare amman sai  da sukayi sanadin fitowa daita.. dayar tace uhm ina ai uwar bazata iya daita ba wannan su'da din fa da kuke gani ta gawurta ta zarta da tunaninku ace mace daita ta daukarwa kanta rayuwar yan iska ki kalleta fa ita da nmj basu da wani banbanci .
ni waye ma zai auri wannan fitinanniyar yarinyar ?
dayar matar tayi murmushi me rabon wahala shi zai kwasa suka kwashe da wata uwar dariya gbdynsu  ai ni ashanu talla ma nakejin ance wai dan gidan tsohon ambassador take maseefar so....
saurin kama baki dayar tayi tana zaro ido waje a shekuwa zata mutu babu auri ..
irin wayan magangun suketa tautauwa atsakaninsu har sanda su'ad takaraso.
har   gabansu ta dinga auna musu kallon banza dan duk tagama sauran abinda suke cewa akanta.
zabura sukayi da ganinta tare da dafe kirji suna dubanta atsorace hankalinsu yayi bala'i tashi domin su tunaninsu tabi su ore ne sun fita. gbdy suka yi wiki wiki da idanu suka shiga kallon kallo tare da shan jini jikinsu har ta juya zata wuce su taga ai bai kamata ta barsu hk ba gara ta dan soma gyara musu zama kafin ta dawo taci kutumar ubansu daya byn daya dan hk ta dawo da baya da baya tana juyowa ta sa hannuwanta duka ta hade  kansu ta gwara waje daya sannan ta dauke dayar da wani gigitaccen mari tace kujira dawowota yau duk uban da yayi muku tsaye sai kun bar gida tunda bana ubanku bane..
    "amman kafin ku fita sai cacci uban kowace daga cikinku tana gama fadar hk .
juya tayi cikin sauri tayi waje ,su kuwa aguje suka kwasa da gudu suna rawar jiki kowace tashige part dinta ta kulle.

SAI KA AURENI DOLEWhere stories live. Discover now