1

325 10 2
                                    

★★★★★

*_SIRRIN..._*
                      *_B'OYE_*
  
                                ★★★★★★

     *_STORY &WRITING BY_*

*_UMMA MUHAMMAD NAJAMAGA_*


           *_follow me on wattpad👇_*

*_kulsuum_muhd_sadeeq🤙_*

          *_ummanajamaga@gmail.com_*



*_I  THANKS ALMIGHTY ALLAH TO GIVE ME OPPORTUNITY POWER TO STARTED THIS BOOK AND I PRAY FOR THAT TO FINISHED IN PEACEFUL MANNER!!!!_*


★★★★
          ★★★★
                   *_01_*   ★★★★★★★★★★★★★★★


"Yanzu doctor kana nufin Ina da kansar mahaifa bazan tab'a haihuwa ba ,? Yanzu kana nufin saidai Inga wasu da yaro mu sai kallo? Kenan kana nufin AL'MUSTAPHA zai iya yin aure ya haihu tunda matsalar a jikina take ba ajikin shiba ? "

Wani ihu tasaka tana kuka tana cewa "wallahi ba'a Isa ba Ni kad'aice matar almustapha babu macen data Isa ta rabeshi," ta Kara'sa maganar cikin matsanan cin kuka gwanin tausayi, doctor ne yace mata " haba maryam meye Na damuwa alhalin shi mijin naki Bai damuwa ita haihuwa ta Allah ce sai kiga da wannan cutar kin haihuwa , Amman Dole cikin biyu ayi d'aya , duk abinda zaki Haifa Dole ya kasance mai k'arancin lafiya . Dole yazo a makaho ko gurgu kee zai ya zuwa ta marar hankal..."

"Shut up doctor Saleem ..." Yaji an buga mai wata muguwar tsaya , gaba d'aya jijiyoyin jikinshi sun Tashi sai fitar da huci yake tamkar Na mijin zaki , Saida yagama yimai kallon wulak'annci da kaskanci sannan yafara magana cikin tsanin b'acin rai, "mai kake nufi doctor ..? kana nufin yanzu inhar maryam tasamu ciki danmu zai kasance cikin wannan yanayin da ka lissafo ..?"

Doctor Saleem zare glass din idonshi yayi sannan yafara bayani kamar haka "eh kwarai kuwa Dole danku ya kasance cikin wannan yanayin domin tunda ga lokacin da kuka samu cikin zaike zaune cikin mahaifar kuma duk wani cuta zasu rayu tare dashi cikin mahaifar, wannan abunda Na lissafo maka kad'an kenan daga ciki..." Wata iska mai k'arfi almustapha yaja sannan yafara magana yace "to doctor zamu tafi gida idan mukayi tunani zamu nemeka zuwa waye wan gari," hannu ya baiwa doctor sukayi musabaha sannan suka fito suka nufi motan su.sai yanzu Na samu daman k'are masu kallo

Sanye yake cikin wata suite mai kyau Wanda kallon ta kadai shi zai bayyana maka ba k'aramin kud'i aka fidda ba kafin a mallaketa , black and ash color ne suite d'in , dogo ne sosai ma'abocin tsawo yana da d'an kauri Wanda ya dace   da tsawon jikin shi ,fuskan sa Na zagaye da saje mai kyau Wanda shine abunda yafi komai k'awata mai fuska , yana dauk'e da Dara daran Ido Masha Allah domin manya ne sosai ,yana dauk'e da hanci Wanda shiba dogo ba sannan shi ba gajere ba madaidai ci ,da bakinsa d'an k'arami Wanda sajen shi yakara fiddo da Jan leban shi Masha domin gaskiya guy d'in ya had'u k'arshe domin irin su ne aki Kira 3in1,

Fara ce ita kamar mijin ta kana ganin ta kasan Hutu da jin dad'i ya ratsata bata da wani sirrin kyau Amman yanayin jin dad'in da take ciki zaka iya kaita sahu Na biyu akyau akalla zata kai shekaru 34 shikuma namijin zai kai shekara 36 domin baifi 2, year's ya bata ba kusan age mate suke

Fisgan motan yayi cikin matsiyacin gudu tamkar Wanda yake tafiya a cikin gida, duk inda ya wuce sai an zageshi saboda yadda yake tuk'in motar tamkar mahaukaci  .

Masha Allah Na furta domin ganin wata haddadiyar masarauta da suka nufa , tabbaas wannan masarautar k'arshe ce wajen had'u yana zuwa babu wata wata aka wangale mai gete ya Danna kanshi ciki ,

Welcome to JIGAWA aka rubuta jikin wani Babban allo akasa an rubuta. GUMEL EMIRATES COUNCIL gaskiya wannan masarauta ta had'u fiye da zaton mai karatu ,

Masha Allah parking lot yaje inda wasu arnan motoci suke kamar a kamfani domin babu Wanda zai iya fasalta iya yawan su gasu nan akasa iya ganin ka

Yana bude motan da sauri bayin dake gurin suka taso suka zube kowa Na kwasar gaisuwa , kawai hannu yake d'aga musu batare da yace komai ba ,itama ta b'angaren ta mata ne suka kewaye ta suna gaisuwa , sai wani kallon su take tamkar kashi wannan shi zai nuna maka tabbas batta da mutunci ,

Sun d'au hanya sun nufi part d'in su da sauri wata baiwa taxo ta fad'i a gabansu , bayani zata Fara gimbiya ta dauk'e ta da wani mari Wanda nima Saida Na rik'e kunci Na domin jin saukar Marin maman a fuskana, "ke wacce irin mahaukaciya ce dabba banza matsiya ciya ke har kin Isa muna tafi kisha gaban mu tamkar wasu sa'anin ki ? K ....."d'aga mata hannu almustapha yayi sannan ya kalli baiwar dake fidda ruwan hawaye yake tambayar ta maike faruwa? Cikin in Ina tafara magana ,"Allah ya taimakeka rankai dad'e daman shugaba tace a kiraka " gaba d'aya Saida cikin su ya k'ada cikin in Ina yace "ow. ..k. ..kice ...mat..  a gani.... nan" itama cikin tsoro tace lalle lalle tace kuwu ce yanxu ko Ranku ya baci ,.

Tamkar Wanda kwai yafashe musu haka suka nufi inda shugaba take ,

Tafiya suke Amman kowa da abunda da yake sakawa cikin zuciyar shi ,wani hadadden poulor suka nufa Wanda zamu iya kiranshi da aljannar duniya domin ya had'u k'arshe ,ita kanta k'ofar shiga poulorn tamkar da gold akayi ya duba da yadda suke d'aukan Ido, cikin wani tattausan carpet suka luma k'afar su poulorn bashshi da hayani domin ko kujerun babu sai wasu Cushings da aka jera Wanda ya k'ara k'awata gurin , tabbas ko iya nan aka Kira da masarauta to ya had'u k'arshe , gani nayi sun zube nakai dubana ga wacce aka zube wa domin duk sun sunkuyar da Kansu k'asa kowa da abunda da yake sak'awa , dattijiwar macace zaune wacce cikar kamala da haiba suka bayyana akan fuskan ta zaune ta d'ora d'aya kan d'aya da alama jiran su take , cikin sauri da in ina maryam tafara magana, "Allah yaja da ran shugaba ya k'ara miki tsawon rai yanzu asabe taje tace kina nai manmu Allah yasa ba laifi muka aikata miki ba...?" Ta K'ara sa maganar cikin rawan murya , d'ago idon da zayyi suka had'a Ido da shugaba ai cikin in Ina yafara magana ."Allah...yajada ran..ki uhm...daman....bat.tta..d..a.lpy...ne shine..mukaa..je siyan.. maganiiiiii......." Ya k'ara sa maganar tamkar zai saki ihuu domin yasan yau mai kwatar su sai Allah, saida tagama yi musu kallon wulak'annci sannan cikin Isa da izza tafara yi musu magana.

"Daga gidan uban wa kuke ? Uban waye yabaku izinin fita daga gidan nan batare da izini ba ? Kuma gidan uban wa kuka je..?" Gaba d'aya cikin su ne ya debi rawa , tsawar data daka musu ita ta sanya almustapha zabura da sauri yace "munje asibiti munga doctor. ....ko maryam zata haihu...." Gaba d'aya wutar suce ta d'auke jin yadda ya saki layi itakam maryam tasan kashin ta ya bushe yau, murmushi shugaba tayi sannan tace .!!

"Kaima daba girma kayiba harka San ciwan rashin haihuwa.  ? To Ina gamu Wanda da nake so Dan ma kuma naka ? Kaje ka auro wannan sa'ar uwar taka sannan kake jiran haihuwa ? Ban maka baki ba Amman da wuya wannan ta haihu ta tsofe a waje, Na baku nan da wata goma 12 indai matar ka bata haihu ba saina aura maka yara. Uku...." Da sauri maryam ta d'ago Amman suna had'a Ido da shugaba tayi sauri ta mayar da kanta k'asa umarni tabasu nasu Tashi su tafi ,cikin gaggawa suka fice kowa yana sauke ajiyar zuciya ,

Kuka ta sanya mishi suna zuwa kewayan su da hannu ya k'ori bayin dake wajen sannan ya jata jikin ta yana lallashi cikin kalami Na kwantar da hankali yafara magana, " haba my princess meye Na damuwa akan magan ganun wannan tsohuwar ? Ni bantaba burin auren mace sama da guda d'aya ba Amman gashi ana neman bijiromun da hakan," zabura yaga Tayi tazari waya ta Danna number doctor Saleem , yana dagawa tace "please doctor Na tab'a karantawa a wani littafi cewa ana dashe" takarasa maganar tamkar zata sau ihuu,murmushi doctor Saleem yayi sannan yace "ai duk wacce akayi wa dashe mahaifar ta Na lafiya Amman akwai mafita guda d'aya?" Cikin sauri tace "doctor indai wacce zan haihu ce in jinka kuma zan bita" cikin muryan shi mai dad'i yace

*_"mai zai Hana kisamu irin yaran nan marasa gata Ku yaudare su ayi dashen a mahaifarta har lokacin haihuwa yayi Amman fa aikin akwai hatsari...."_*

Bata bari ya k'ara sa ba tace lalle lalle yanzu yaxo gidan su suna son ganin shi , ba'a d'au lokaci mai tsayi ba yazo gidan yasamu guri ya zauna suma duka suka zauna domin jin maike faruwa, bayani yafara musu kamar haka..........


*_please follow me and following me on my wattpad please my dearest👏_*

SIRRIN B'OYEWhere stories live. Discover now