★★★★★★
*_SIRRIN B'OYE_*
               ★★★★★★★★



*_STORY & WRITING BY_*

*_UMMA MUHAMMAD NAJAMAGA_*

       *_Follow me on wattpad👇_*

*_kulsuum_muhd_sadeeq🤙_*

              *_Ummanajamaga@gmail.com_*


🅿️3

"Yawwa gimbiya wannan shawaran naki yayi Amman abunda zamu duba shine 'gwanda tun daga can Ku dauro auran ta dashi domin kar yaron Ku ya kasance cikin jinsi Na shegu." Murmushi tayi Wanda yafi kuka ciwo sannan tace "doctor karka manta dalilin bani son kishiya shiyasa na yarda Na amince da hakan , kenan yanzu innayi hakan zan yiwa kaina da kaina kishiya .? A'a abunda bazai iyuba  kawai zan kawo yarinya daga masarautar mu ayi dashen a cikin ta Amman batun kishiya ban amince ba gaskiya." Numfashi doctor ya sauke sannan yace "hmmm kinsan nasaba wannan aikin ko ? Ba'a kanku nafara ba kuma kowa zanyi wa suna bukatar shawara saboda b'acin Rana . Amman bakomai duk yadda kike so haka za'ayi ina jira sai kin kawo yarinyar." Kitt ya kashe wayan shi yayi jifa da ita yaci gaba da duba marassa lafiya , itama shuru tayi da waya a hannun ta sai jujjuya wayan hannun ta take ,gaba d'aya ta Lura ran doctor ya b'aci Amman kar ya manta Dan kar Amata kishiya yasa ta yarda ta amince da wannan batun.amman in Banda haka akwai matar data Isa ta had'a sperm d'inta Dana almustapha? Murmushi tayi sannan afili tace "abunda bazai iyuba !! Danni aka haifi almustapha ban shirya zama da kishiya ba 'kenan in har Na yarda da maganar doctor nayi kaina da kaina kishiya .? Ban shiryawa wannan ranar ba ban shirya kunsar tak'aici ba !kamar yadda Na haramta ga kowanne namiji haka Na haramta wa Almustapha ko wacce mace , wannan  maganar taka doctor bamai iyuwa bace  bazan amince da ita ba kwata kwata !!!!" Ta k'ara sa maganar cikin k'ara ji tamkar da wani take zaune acikin zuciyar ta tace "dazaman banza bari man inje gurin shugaba in gwada sa'a ta ,idan ta yarda cikin satin nan saina tafi!" Tashi tayi ta shirya cikin alkyabbar ta mai kyau ruwan k'asa wacce tayi daidai da kalan fatan jikinta , ahankali ta fito cikin porlourn cikin tafiyar ta ta Isa da izza' ta dage kannan sama ita Dole 'yar sarki sirikar sarki matar d'an sarki , wannan matsayi data ke jin kanta shi kebata tabbacin da wuya a samu mai sa'a irin ta,

Cikin sauri bayin dake cikin porlourn d'in suka zubewa a k'asa kowa yana kwasar gaisuwa Amman kallon inda suke baya yiba ,da sauri furere baiwar ta mai kula da duk wasu lamuran gimbiya ta take mata baya suka nufi b'angaren gimbiya' ganin yadda gimbiya ke Jan Riga yasa wasu bayi saurin rik'e mata Riga kowa ya rik'e gefe da gefan ,. Kofar falon shugaba suka tsaya da sauri masu kula k'ofar suka bude mata suna kwasar gaisuwa 'ciki ta shiga sukuma bayin ta suka tsaya waje suna jiranta,

Kanta ta sanya cikin porlourn da sallama a bakin ta shuru poulorn ba kowa sai bayin dake kula da wajen ' sai wata sanyin AC da ya ratsa porlourn ya had'u da k'amshin AC ya bada k'amshi mai dad'i , tsawa ta daka ma bayin gurin tana cewa "wai Ku wanne irin mahaukata ne ? Kuna ganina babu Wanda zai mun gamshashan bayani ? Ban.. ..".  "Lalle yau kika tabba ta marar da'a har ki shigo cikin d'akina kike zagi !? Nagode domin basu kika zaga ba Ni kika zaga' tsabar rashin da'a har ki shigo gurina kike zagi ? Gaskiya Almustapha bayyi dacen mace ba, ko Ku masarautar Ku ba'a girmama duk wani da. Yake k'arka shin masarauta? To mu koda Karen da yake nan to yana da 'yanci wannan shine rashin da'a marar tunani in kika k'ara irin haka zan b'ata miki.!"

Samun guri tayi ta zauna ' da sauri gimbiya ta zube k'asa tana naiman gafara domin itama tasan ta tafka rashin da'a, ko cikin masarautar su ba'a yarda da yin hakan ba , Saida shugaba tagama shan k'amshin ta sannan tace," wannan yazama shine abunda zaki nuna Wanda zaisa Na fusata dake har nayi fushi in kika bari hakan ta sake faruwa hmmm!!!." Gimbiya k'ara k'asa da kanta tayi sannan cikin yanayi Na nadama tace , "insha Allah wannan shine kuskure mafi muni da zan k'ara aikata wa." Dukan su shuru sukayi ita shugaba ma fruit d'inta take ci ko takan gimbiya bata sake biba, Saida gimbiya ta Lura tasan tabbas in ba ita tayi magana ba to shugaba bazata kula taba,cikin sanyin murya da nuna r'oko tace, "Allah ya k'ara miki tsawon rai nazo in nemi wata alfarma a gurin ki !" Shuru sukayi Na tsawon mintina , tasan tabbas Suna da sarauta mai k'arfi kuma wacce tafi wannan Amman gaskiya wannan masarautar tsarin  mulkin su daban yake domin ya sha banban da Na sauran masarautun domin komai nasu gwanin sha'awa domin sunfi aiki da addini sab'anin guntun masarautar da suke aiki da al'ada , maganar tace ta dawo da ita lokacin da tace mata, "Kina b'ata min lokaci in bakki da abun fad'a Tashi kiban guri zan gana da jama'a ta." Sauri tayi ta dawo daga dogwan nazarin da tatafi tace, "Allah ya k'ara miki nasara Ina neman alfarmar ki bani Dama naje Naga mahaifa Na koda Na tsawon kwana uku ne.?" Shuru sukayi su duka tsawon lokaci sannan shugaba ta fara magana, "yanzu Ni nake auren ki..?ko nice mijinki..? Ko zamana kike...? Kenan kema kin shiga sahun masu cewa mulkin masarauta a hannuna yake? To ba haka nake ba kuma kiya gaggawar janye wannan k'udirin naki akaina , Dole innuna ikona matsayina na mahaifiyar duk wani Wanda ke k'ark'a shin masarautar mu Dan haka ki cire cikin irin wannan zancen indai mijinki ya barki to Ni Ina ruwana Dan haka ki tambayi mijinki in ya barki fine nidai abunda nasani zan taka kowa ye indai Naga zai kauce hanya." Shuru sukayi su duka an rasa mai magana, sallamar sace ta sanya su duka suka juya, shine yake takowa zuwa cikin porlourn ,tun kafin ya k'ara so daman k'amshin turaren shi ya k'ara so zuwa hancin su, daret kusa da shugaba yaje ya zauna yana sakin murmushi Wanda yak'e k'ara fito da sirrin k'yan
Shi, Saida yagama yanga da isa da izza sannan yace,"shugaba barka da gida ya kike ya hutawa ya tsufa.?"murmushi tayi sannan tace,"ja'iri ai kune tsofi da kuka kusan kai shekaru hamsin babu haihuwa."dariya kawai yayi Dan yasan ya tab'o mata inda yake mata k'aik'ai,basar da zancen ya yi ta hanyar cewa,"uhm! Mai yafaru Na ganku a zaune Ku duku kunyi shuru.?"duk wani annurin fuskan shugaba Saida ya d'auke sannan  tace,"hmm nida matar kace tazo ta nuna min rashin da'a har kewaye Na Amman ba wannan ba domin Na yafe ta, Amman tana so taje garin iyayan ta shine tazo ta tambaye Ni , tunda gani Na auro ta tana biyamin bukata duk da ran duniya,kenan matar kama ta sanya Ni cikin sahun da matan ubanka suka sanya Ni ko ? To gatanan inka barta yanxu ma tayi tsuntsuwa ta ganta agaban mahaifan ta ,inka barta ka fad'a anan kowa yaji in kuwa baka barta ba ba Dole a tafiyar."murmushi yayi shidai baisan Randa maryam zata shiga ran shugaba ba,domin yayi inan yadda maryama
Kema shugaba biyayya ko shi da iyayen ta batayi wa,domin duk yaran masarautar su rayuwa suke ta 'yanci babu ruwan su da tsarin mulki,lokacin da zai auri maryam hatta mahaifin shi bai so ba domin tare sukayi karatu a turkiya kuma babu  Wanda baisan tagama lalatar taba domin kowa yasani yarima almustapha ba a budurwa ya sameta ba,shine dalilin da yasa hajiya ta k'ara tsanar ta kuma tana zagin ko asiri suke yiwa jikin nata, to agaba dai gaskiya zatayi halinta,saida ya sauke numfashi sannan yace,

"Hajiya Na barta taje tayi sati biyu."kallon shi hajiya take irin Na baka da hankalin nan sannan tafara magana,"Amman almustapha kaban mamaki ,yanzu matar taka ce zaka barta har sati biyu ? Koda yake banga laifin kaba domin wannan uwar guzumar babu abunda zata iya maka gwandama ta tafi kaima har ka huta,addu'a ta d'aya Allah yakawo yarinya k'arama wacce zata sauya rayuwan ka daga bak'i zuwa fari."dukan su babu Wanda maganar ta ta b'ata wa rai domin ita mutum ce da bata b'oye abun dake cikin ranta,gimbiya ma ba taji komai ba Amman taji zafin wai ya auri yarinya duk da tasan wannan abun bazai tab'a iyuwa ba wai siyawa d'an fari kare,domin indai da boka da malamai a duniya to saidai almustapha yayi kallo Amman shida mace hmm,"ok shikenan kije kiyi sati sai kidawo yaushe zaki tafi?."numfasa wa tayi tace "sai in tafi jibi idan Allah yakaimu." "Ok Allah yakaimu." Shuru sukayi inda ita tatashi tana godiya ta koma barin su ,sakkowa yayi daga kan kujera ya d'ora kanshi bisa kan cinyar shugaba wasu zafafan hawaye suna zubo mai, itama jitake tamkar tayi ta kukan domin tasan damuwar shi bata wuce shida mahaifin shi da matan uban,cikin sanyi murya yafara mata Magana....   "Yanzu shugaba abunda mai martaba yake mun yana ganin shine daidai yana nuna matarshi sun fini daman haka maraicin rashin mahaifiya yake da ciwo? Tabbas shugaba da bakya raye da tuni nashiga sahun tarihi Ni duk fadar nan in Banda ke babu inda zan sanya kaina naji dad'i."gaba d'aya ranta ya k'ara b'aci,cikin yanayi Na damuwa tace gayamun maike faruwa?." Saida ya sauke a jiyar zuciya yace "yanzu mai martaba ya Kira Ni turakar shi Ina shiga Na tadda Fulani da kilishi zaune...........





*_IF ALLAH SAID YES NO BODY CAN SAY NO_*

SIRRIN B'OYEWhere stories live. Discover now