★★★★★★
       *_SIRRIN ƁOYE_*
                        ★★★★★★

                *_NA_*

*_UMMA MUHAMMAD NAJAMAGA_*

*_wattpad:-kulsuum_muhd_sadeeq_*

🅿️8

"Daga yau ba sai gobe ba insha Allah zan aiwatar da wannan aikin kafin wancan jarababbiyar ta wai wai toki."
         Dukan su dariya suka sanya domin da shugaba suke.
"Yawwa Mommy shi yasa nake sonki nake alfahari dake wallahi."
          "Haba ! Ƴata in ban miki ba waye zai miki fatana dai muyi komai cikin *_SIRRIN ƁOYE_*  Wanda har abada asirin mu bazai to nuba.".      
     "Haba Mommy karki ji komai yanzu dai abunda ya rage ki samo mana yarinyar da zamuyi wannan aikin da ita."
" Karki ji komai my daughter nah."
      Hira suka ci gaba da yi irin ta uwa da ƴarta wacce suka shaƙu da juna.

*********

"Kinsan dalilin da ya sanya na Kira ki?.".
     
       Saida ta rausayar da kai sannan tace.

"Allah ya taimaka Fulani matar sarki saikin faɗa domin Ni baiwa ce kina da ikon aikata komai a kaina."

       Ai wannan furucin shine ya ƙarasa harda harɗe ƙafa sannan tace.

"Ai kinsan gimbiya maryam ƴata ko.?".

       Saida ta ƙara sun kuyar da kai sannan tace.

"Haba Fulani wa zai kasan ce cikin garin Kano yace baisan gimbiya maryam ba yarinya mai Adalci da tausayin Naga ba bare nida nake jakadiyar ki ai tamkar Tata haka nake.".

         Murmushi tayi shi yasa duk laifin da asabe take yake goguwa a gurin ta domin yadda take ƙaunar gimbiya.

"Yawwa to ita ce tazo zata tafi , Amman tana buƙatar baiwa guda ɗaya cikin bayin in nan.".

      "Allah ya ƙara miki nasara ince dai ba wani Abu bane ya faru.?".

     Murmushi tayi sannan ta kwashe duk yadda sukayi da gimbiya ta faɗa mata.

Itama dariya tayi sannan tace.

         "Wannan Abu mai sauƙi Amman Ina da shawara.".

"OK faɗi muji kinsan ke  akwai babban kai.".

       Cewar gimbiya dake sakkowa daga upstairs.

Dukan su dariya sukayi tazo ta zauna jakadiya ta gaida ta, sannan gimbiya tace.

         "Ke muke saurare  kinsan yau zan wuce da yamma.".

"Yawwa wannan abun yafi komai sauƙi Amman bada baiwa ba za muyi wannan aikin."

       Da mamaki dukan su suka bita da Ido suna son ƙarin bayani, itama Lura da hakan da tayi yasa taci gaba da jawabin ta.

"Abunda yasa wannan aikin baza muyi da bayi ba shine, duk wani munafurci da gulma yana gidan sarauta, bare mu da muke da mahassada a ƙarƙashin mu,baiwa ɗaya za mu ɗauka duka hankulan kishiyoyin ki zai yo kanmu, kinsan tambaya ta farko da zasu fara yiwa kansu ita ce ,da can gimbiya bata nemi yarinyar ba sai yanzu ? Lalle akwai wani *_SIRRIN ƁOYE_* mu da muke so mu aiwatar da komai cikin sirri Dan haka babu baiwa a wannan tsarin Ni ita ce shawara ta."

        Dukan su sunyi shuru da alama zancen ta ya shige su, Fulani ce tace.

"To yanzu ya za'ayi kinsan yau dai gimbiya zata tafi da yamma ko ? To a Ina zaki samo mana yarinyar.?"

      Dukan su kallon su suka maida ga jakadiya suna son suji mai zata ce.

"Indai wannan ne babu damuwa akwai wasu yara suna tare da maman su da baban su Amman masu ƙaramin ƙarfi ne, zanje nace umarnine daga fada Ni nasan wacce zan ɗakko."

SIRRIN B'OYEWhere stories live. Discover now