10

44 5 0
                                    

★★★★★★
       *_SIRRIN ƁOYE_*
                       ★★★★★★


              *_NA_*

*_UMMA MUHAMMAD NAJAMAGA_*




*_FREE PAGE_*

         *_Am repeating my self book ɗina  na kuɗi ne if you read without paying is your own cup if tea_*

*_my book is very cheap Naira #200 only you can transfer your card through this number 08146405540, or transfer through  this account number, 3053905686,UMMA MUHAMMAD POLARIS BANK show your evidence of payment through this number 08146405540_*


🅿️11



Gudun da motar take a cikin garin gumel  shine abunda yafi komai mamaki domin ganin motar gidan sarki ce.

      Gudun da suke a hanya koda suka zo cikin garin basu daina ba.

Daidai shigowar su cikin fada ta umarce shi da ya rage gudu.

      A hankali suka fara shiga cikin fadar.

Parking yayi a parking lots inda motocine iya ganin mutum, in mutum Bai San wajen saida mota ba tabbas zaice a cikin kwatono yake.

      Da Sauri direban ya zagayo ya buɗewa Aminatu ƙofa.

      Da Sauri ya zagayo ya buɗewa gimbiya itama ƙofar.

Tana sakko wa daga motan ta ɗauke direba da wani lafiyayyan mari.

      Duk wani Wanda yake gurin shuru yayi yana ganin ikon Allah.

Tabbas wannan direba ɗin ya haifeta Amman baici darajan girman shiba ta ɗauke shi da mari.

     Magana ta fara cikin isa da izza.

"Dan tsabar iskanci da buro uba har Saika buɗewa baiwa ta ƙofa sannan Ni to wallahi wannan shine aikin ka na ƙarshe a cikin fadar nan."

     In Banda hawaye babu abunda direba yake cikin kuka yace.

"Tabbas talauci babu abunda Bai sawa,nasan na haifeki Amman ki ɗaga hannu ki mare ni? Yauce Rana ta farko Dana fara Dana sanin aiki a ƙarƙashin ku,ni bani da talaucin da zan wulaƙanta kaina."

       Wani kallo tamai na shashasha marar hankali .

     Bayin dake wajen ne suka take mata baya da kayan ta.

Har zuwa wannan lokacin banji maganar Aminatu ba.

        Itama takewa gimbiya baya tayi.

"Ke dallah Malama dakata!!!."

   Gimbiya ta dakawa Aminatu tsawa.

      Kowa dake gurin saida ya tsorata ba iya Aminatu kaɗai ba.

"Dan uwar ki nace ki wuce ki karɓi wancan kayan kema ai baiwar ce basu kaɗai bane bayi kin wani tsatstsareni da ido shegiya dangin mayu."

       Karɓan jakan dake hannun ta tayi sannan suka ci gaba da tafiya.

Gimbiya sai wani ɗaɗɗaga kafaɗa take ita dole ishashshiyar nan.

       Direct part ɗin ta suka wuce.

Ga abinci nan a tsakiyar parlour an shirya shi iya ganin mutum.

    Daidai da kujerun pourloun saida aka sauya wa style.

      Saida ta gama kallon ko Ina sannan ta kalli bayin dake tsugunne a pourloun tace.

        "Naga  banga my nurul ƙalbi ba Ina yake?."

SIRRIN B'OYEWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu