★★★★★★
       *_SIRRIN ƁOYE_*
                       ★★★★★★


              *_NA_*

*_UMMA MUHAMMAD NAJAMAGA_*

🅿️10

*_FREE PAGE_*

         *_Am repeating my self book ɗina  na kuɗi ne if you read without paying is your own cup if tea_*

*_my book is very cheap Naira #200 only you can transfer your card through this number 08146405540, or transfer through  this account number, 3053905686,UMMA MUHAMMAD POLARIS BANK show your evidence of payment through this number 08146405540_*

      "Kee!! Dallah mahaukaciya wuce muje , komai akayi da talaka sai anga ba daidai ba, tsabar akunyan ci da dabban ci mai kike kallo ? Dallah wuce kafin yanzu na bada umarni wannan jirgin yayi gunduwa gunduwa dake jaka kawai."

Kamar ko wanne lokaci yanzu ma haka fuskan Aminatu take domin bazaka gane taji ciwon maganar ko bata jiba.

     Gidan baya aka buɗe wa gimbiya ta shiga.

Draivan ya kalli Aminatu yace.

"Ki shigo gidan gaba ki zauna."

Ko kallon inda yake ba tayi ba ta buɗe mota ta shiga gidan gaba ya fara tafi ya.

      Shuru suke babu mai cewa komai ga manyan motoci na take musu baya.

Karantun Alƙur'ani ya sanya musu, suratul mulk ita ya sanya.

      Baka jin komai sai sansanyar muryan Ahmad sulaiman.

Daga yadda bakin Aminatu yake motsi tabbas shi zai nuna maka karatun take bi domin har wani lumshe ido take.

"Ka!! Dallah mahaukaciya nace ka kashe wannan karatun da ka kunna ,domin zanyi waya da nurul ƙalbi."

      Kafin ta rufe bakin ta ya kashe karatun

Cabb lalle gimbiya tayi nisa da alama ko an kirata ba ji zatayi ba kawai saidai fatan Allah ya bata lafiya.

     "Hy!! My honey ya kake?."

Ko me akace daga ɗaya ɓarin oho.

"Ba wani missing ɗina da kayi  da ka damu Dani ai da ka zo tarya na."

       "OK shi kenan ka shirya tarya na kaji honey ."

"OK byee sa mun ƙara so.."

Kowa da abunda da yake saƙawa cikin ransa.

     Shi kuwa direba cikin zuciyar shi yake cewa.

"Gaskiya sarauta ta Sha ƙasa yanzu wai wannan ƴar sarki ce kuma matar ɗan sarki ko ? Amman kwatata babu aji babu class ,ko wannan yarinyar da suke tare tafita kama da ƴaƴan sarauta domin tunda suka zo baiji tace komai ba, abunda yasa yasan ba kurma nace da yace ta shiga mota ta shiga , gaskiya wannan itace ta dace da yarima... . ..."

     "Direba waikai wanne irin jaki ne ? Ina ta magana kayi shuru."

"Allah ya huci ran gimbiya maryam matar yarima Almustapha ita kaɗai ba kishiya  insha Allah."

Wani malalacin murmushi tayi.

     Bala'in da za tayi ma fasawa tayi.

Shi kuma ya Riga ya gano lagwanta shi yasa in ya mata laifi yake kwana lafiya.

      Gimbiya ce ta bada umarnin a ƙara gudu.

Duk wata mota in ta taho saita kauce domin ganin tambarin masaurautar gumel a jiki.

Adaidai wani local government daga shi sai gumel mai suna gagarawa,sukayi ciki da wata gurguwa.

       Basu kashe taba Amman ga dukkan alamu sunji mata ciwo a ƙafa.

Mutane har sun cika gurin kowa na tofa Albarka cin bakin sa.

     Duk inda hankali yakai ga tashi to na wannan direban ya tashi.

Da Sauri ya kama ƙofa ya murɗa zaifita yaji muryan gimbiya na cewa.

      "Dakata!!! Uban waye ya baka iznin buɗe mun mota Ina ciki.?"

"Yi haƙuri gimbiya bakiga ɓarnan da nayi ba ? Kinga ta can wallahi ko motsi ba tayi."

     Saida ta ya mutsa fuska sannan tace.

"Kai dallah Malam nagani jamin mota mu tafi , ko kashe ta nayi na kashe banza wannan miskiniyar talakan."

    Babu yanda ya iya haka ya shiga mota Amman zuciyar shi sai bugawa take.

     Daidai lokacin da yaja motan zasu gifta ta gefan matar.

Gimbiya ce ta ɗauki rafar dubu dubu guda biyu ta jefa akan matar dake kwance.

Umarni ta bashi kan cewa ya ƙara gudu..

Cabb yaufa mutane suke ganin abunda yafi ƙarfin su..

Da kuɗin da ta bata aka Kira ƴan sanda suka ɗauke ta aka nufi asibiti.

     Sun gane motar kuma sun ɗauki alƙawarin indai ta sake zuwa ta wuce saidai duk abunda zai faru ya faru domin sai sun ƙone ta.

*_ZANYI SHAFI 15 FREE KAFIN YA KOMA NA IYA WANDA SUKA BIYA ,_*

*_yi ƙoƙari ki siya Ni bazan yi Allah ya isaba  Amman kuma ku kyautata mu'amulata daku please👏_*
.

*_zangane soyayyan da kuke mun nida book ɗina ta hanyar biyan #200 nagode_*

SIRRIN B'OYEWhere stories live. Discover now