★★★★★
*_SIRRIN ƁOYE_*
                   ★★★★★



              *_NA_*


*_UMMA MUHAMMAD NAJAMAGA_*


               *_Wattapad 👉kulsuum_muhd_sadeeq🤙_*


🅿️7



"Mayyafaru my? Kimin bayani waye ya sanya minke kuka?"
      Cikin muryan wacce kuka ya ratsa ta fara magana ,
"Nida yaya bashar ne nida gidan ubana Amman ban isa innuna ra'ayi naba ? Kawai Dan muna zance da hasheem Ina ruwan shi wai nayi mai fitsara,"
     Tana ƙara sa maganar ta fashe da wani irin kuka.
Shima Saida yaja numfashi sannan yace,
     "Gaskiya baki kyauta ba ai yayun kine Bai kyautu kike masu fitsara ba ,Amman shima dukan da yayi miki Bai kyauta ba , please ki daina rashin kunya kinji ? Banso Ake taɓamin lafiyar jikin ki,"
Saida tagama shashshekar kukan ta sannan tace,
     "Shekanan Na haƙura kuma nadaina Amman Na fasa sati gudan da nace zanyi."

Cikin mamaki yace

      "Ban gane kin fasa one week ba ?"

"Eh !! Nafasa domin kasan abunda yakawo Ni ko ? To daga yau zuwa gobe zanyi bincike jibi kuma nadawo."

       "To yanzu inkin dawo meye amfanin zuwan naki gida ? Da ba sai ki sanya ba a kawo miki yarinyar.?"

Saida ta sauke numfashi sannan tace

     "Zuwan nawa shine babban mafita kana tunanin zamuyi wannan aikin a bayyanane?"

"Nima nasan hakan bazai yuyiba kamar yadda dawowar ki take daidai da tona asirin kanki,"

       "Ban gane Na to nawa kaina asiriba kenan Ni kaɗai nake buƙatar haihuwan ?"

"Ƙwarai kuwa domin Ni da zajiki ta tatawa da kin haƙura da wannan ƙudurin kawai ki dawo muyi normal life ɗin mu..."

        "Wallahi baka isaba Almustapha !!!!"

Tayi saurin katse shi cikin kuka ,
  
       "Wato kasan nice bana haihuwa ba kaiba ko ? Shine kake cewa nayi haƙuri kai duk lokacin da kashirya haihuwa Saika ƙara aure ko ?"

      "Haba my baki fahimci zance na bane shi......."

"Almustapha bazan taɓa yarda ba kawai abunda nake ɓukata shine goyan bayanka,amman banso naji ka ƙara cewa komai,"

     "To shi kenan my duk yadda kika ce haka za'ayi Amman nidai ko me yaje ya dawo babu ruwana a ciki?"

"Hmm !! Almustapha kana Abu tamkar ba namiji ba naji kuma na amince komai zai faru na shirya kar ɓan shi hannu biyu."

       "OK shekanan Allah ya taimaka."

"Ameeen "

       Itama ta furta

Daga nan suka fara waya irin ta masoyan da suka jiƙe a soyayyah,

     Duk wannan wayar da suke Ashe mahaifiyar ta na kanta a tsaye,

Koda ta ɗago idonta ta ganta bata damu ba saima gyara kwanciyar ta da tayi ,

       Bakin gadon mahaifiyar ta ta zauna sannan tace mata,

"Tashi zaune za muyi magana."

      Tashi zaune tayi tana fuskantar mahaifiyar tata,

"Kedawa kuke waya?"

           "Waye zayyi aure ?"

"Kuma wa za'ayi wa kishiya?"

       Gyara zamanta tayi suna fuskantar juna da mahaifiyar ta ta fara kora mata bayanin har yadda sukayi da doctor Saleem da furucin shugaba a kanta da kuma yadda sukayi da Almustapha da kuma abunda yakawo ta gida da ƙudurin da tazo dashi,

"Wallahi Fulani ban shirya Zama da kishiya ba ,ba Almustapha bane baya haihuwa nice fa ? Kina tunanin daga yayi aure ciki fa zai mata ta haihuwa nikuma shi kenan?."

      Ta ƙarasa cikin wani irin kuka mai abun tausayi

Shafa bayanta mahaifiyar tata take alamar tayi shiru

      Saida ta ɗauki dogwan lokaci tana kuka sannan tayi shiru mahaifiyar ta ta fara magana,

"Ƴata daina kuka !! Ban shirya amsa da ganin wannan baƙin cikin ba ,nagodewa Allah sannan na godewa doctor Saleem , Ni da kaina zan Nemo yarinyar da za muyi wannan *_SIRRIN ƁOYE_* n da ita Amman dole ya zamo yarinyar ta kasan ce marar gata."

     Rungumeta tayi sannan ta fara cewa

"Nagode mahaifiya ta mai share mun kukana gaskiya nayi dacen mahaifiya Allah ya barmin ke my mom my dear ."

      "Haba in ban miki ba wa zanyi wa ? Ke kaɗai ce ƴata mace da na mallaka a duniya."...

"Daga yau zuwa gobe

SIRRIN B'OYEWhere stories live. Discover now