15

100 7 4
                                    

★★★★★★
       *_SIRRIN ƁOYE_*
                       ★★★★★★


              *_NA_*

*_UMMA MUHAMMAD NAJAMAGA_*




*_LAST FREE PAGE_*

     🅿️15


         *_Am repeating my self book ɗina  na kuɗi ne if you read without paying is your own cup of tea_*

*_my book is very cheap Naira #200 only you can transfer your card through this number 08146405540, or transfer through  this account number, 3053905686,UMMA MUHAMMAD POLARIS BANK show your evidence of payment through this number 08146405540_*

             *_wannan shine last free page nawa Dan haka duk mai son ci gaba da karanta wannan littafin zai biya naira ɗari biyu ne vtu ko kati ko transfer ta account number ɗina,wannan ɗan ɗanone daga cikin littafin agaba za'a buga ƙwallon Dan haka naira ɗari biyu karta Hana muku jin ƙarashen wannan cakwakiyan tnk u my Fan's._*



     "Wato ke har kin kai matsayin da zaki karya min dokata ta fada ko?."

Dukan su shiru sukayi har gimbiyar.

      Domin ita dai gimbiya tasan bata Aikatawa shugaba laifi ba.

Maganar da shugaba ce taci gaba da yi ya dawo da ita daga duniyan tunanin ta.

      "Wannan masarautan mijin kice bata ubanki ba,baki da ikon da zaki wulaƙanta wani bare har kiyi kora daga aiki, wallahi da sawa zanyi ya Rama Marin shi,amman innayi haka bake na wulaƙanta ba masarauta na ciwa zarafi."

       Daga yanayin da shugaba take magana zaka gane ranta yayi mummunan ɓaci..

"Kuma ki tabbatar da kin dawo dashi yanzu yanzu, wallahi inba haka ba kin mari auren ki !."

      Ai gaba ɗaya gimbiya ji tayi kanta yana juya mata.

Duk maganganun da shugaba take babu wacce ta ɗaga mata hankali irin Kalmar saki data kira.

     Gimbiya haƙuri take ta baiwa shugaba.

Tare da alƙawarin insha Allah zata kiyaye.

      Itama shugaba zama tayi Amman kallon fuskanta zai tabbatar da har yanzu tana cikin ɓacin rai.

Shugaba shiru tayi ganin ta zauna Amman gimbiya bata gaishe ta ba.

     Lalle sai yanzu ta yarda maddibo bayyi dacen mace ba wallahi.

Ita kuwa Aminatu dake gefe a rakuɓe.

    Ganin shugaba ta gama faɗan yasa ta taso tazo gaban ta tace.

"Barka da wannan lokacin inna dafatan mun same ku lafiya,Allah ya ƙara sanya ya miki zuciya ."

      Tunda ta fara magana shugaba take kallon ta.

Bawai maganar da take yiba I tace ta burgeta aa ganin tsantsar dacewa da tayi da yarima Almustapha.

     Da sauri gimbiya ta karya baki tace.

"Allah ya taimakeki wannan I tace baiwar da nazo da ita daga masarautan mu."

      Shugaba da sai kallon Aminatu take yasa tace.

"Haba Ni nace ,saboda duk masarautan ku in kika cire ƴaƴan kilishi sune masu tarbiya."

      Ci gaba shugaba tayi da zancen ta...

"Da na ɗau alƙawarin bazan Bari ki kawo min kowacce yarinya gida,amman wannan dole na karɓe ta domin inda ƙuduri na akan ta.."

    Har shugaba ta ƙaraci faɗan ta babu Wanda yace koma,in banda haƙurin da suke ta bata.

Umartar su tayi da suje su huta.

       ********

Yana zaune cikin falon ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya...

       Sai jijjiga ƙafa yake da alaman yau sarautan Ake ji.

Ko kallon inda suke bayyi ba.

      Gimbiya ce ta kalli Aminatu tace.

"Kije ɗakin ki kiyi wanka ki huta zuwa yamma zamu fita anguwa."

      Mamaki abun ya baiwa ruƙayya Amman sai tayi fuska ta wuce.

    Itama duka ta maida hankalin ta kan mijin ta.

Kallon sa take inda ƙaunar sa ke ƙara ratsa mata zuciya.

     Da sauri ta Isa wajen shi.

Faɗawa jikin shi tayi zata fara aikin shagwabar tata.

     Dago fuska yayi tamkar zaki.

Buɗe baki yayi sannan yace.

    "Dal........".

  Bata Bari ya ƙara Saba ta jefa bakin ta cikin nashi.

Hmm daman fa mutumin a hannu yake.gashi da shegiyan sha'awa, aikuwa shiru kikije.

     Ɗaki suka faɗa inda aka fara aikin lada.

Ta shawo kan mijin ta kunsan ance daman mata da miji sai Allah,bare ita da tasan halin kayan ta yana fushi akan komai Amman banda wannan gurin.

*******

"Hhhhh yanzu shi kenan shi yariman bazai zo ayi komai a gaban shi ba?."

       Gimbiya  ce tace.

"Kyaleshi cewa yayi indai an ɗebi abunda Ake so zuwan mai zayyi."

    Dukan su dariya sukayi sannan ya kalleta yace.

"Ina wacce za muyi wa dashen?."

   Da hannu gimbiya ta nuna Aminatu.

Da mamaki Aminatu take kallon su.

     Gimbiya ce ta kalle ta tace.

"Kin wani zuba mana ido to Bari kiji in faɗa miki, zamuyi dashen ɗan mu a cikin mahaifar ki."

      Tunda gimbiya ta fara magana Aminatu take kuka.

Cikin kukan Aminatu tace.

"Kiji tausayi na wall... ."..

Gimbiya ba taji tsoran Aminatu ba ta fara mata bayani.



*_laifin daɗi ƙarewa to yanzu za'a shiga cikin littafin shin ana yiwa Aminatu wannan dashen? Shin shugaba tana sanin wannan abun ? Aminatu tana yarda ta haihu ko kuwa ? Shin asirin gimbiya da yarima yana tonuwa ? Duk wannan amso shin zaku same su cikin sauƙi idan kun biya naira #200_*.

     *_nagode muku kuma Ina jiran masiya wannan littafin._*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 08, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SIRRIN B'OYEWhere stories live. Discover now