page 1-2

370 11 2
                                    

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳

*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
Alhamdulillah! dukkan yabo da godiya su kara tabbata ga Allah Subhanahu wata'ala, salati da daukaka da tsira da aminci su kara tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad(S,A,W) da Iyalan gidansa da Sahabbansa.

Na dawo a karo na biyu fans fatan za ku karbi wannan book da hannu bibbiyu fiye da yan da kuka karb'a *Halitta Daga Allah Ne.*

Ummu nasmah'ta ina mugun yinki ngd sosai da kulawa Allah ya raya mana zuria, Allah ya ba ki ikon kammala shahararren book dinki mai dinbun fad'akarwa, wato *Nasmah ko Nasirah* ameeen.

Short story✍🏻

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

بسم ا لله لر حمن لر حيم

🅿_1⃣➡2⃣

Gudu su ke yi ba ji ba gani,
a wani tangareran jeji wani saurayi da budurwa, da ka gansu ka san gudun ceton rai suke, duk da sun galabaita matuka,
Barin ma budurwan janta kawai saurayin ke yi domin ya riƙe hannunta,
Su na cikin gudun ne yarinyar  tayi tuntube da wani dutse nan ta fadi kasa kanta ya bugu, tsantsan wahala kasa kuka tayi sai numfashinta da ke fita sama-sama, bakinta fari sol alamun wahala.

Da sauri cikin tashin hankali marar misaltuwa  ya hau jijjigata yana kiran sunanta
"SAFREENA ! SAFREENA !SAFREENA!."

Da kyar ta iya bude ido da baki tana magana numfashinta kamar zai dauke ta ce.
"YAYA KHALIFA, ba zamu tsira ba a wannan jeji, wannan gudun har yaushe zai kare yau kwanan'mu 14 muna gudu amma basu dai na bin'mu ba mu tsaya kawai ka basu takardun nan Mu huta da azaban wannan jeji, idan kuma ba haka ba za muyi mutuwar da babu gata acikin jejin nan"  ta saki wata wahalalliyar kuka mai ban tausayi, cikin kuka ta ke cewa.
"Ba zan tab'a yafe maka ba *BABA DAUDA* Allah ya isa! Allah ya isa! jinin Abbana da Momyna ba ka kashe a banza ba,  sannan wannan wahalar gudu a jejin da ka sa ka ni, shi kadai ya isheka azaba! Wallahi ko da na mutu a jejin nan za ka ga inda karshen ka zai yi muni wai Dan U....kasa karasawa ta yi, saboda kukan da ya ci karfinta.

Tausayinta ne sosai ya ci ka zuciyar Khalifa ya ce.
"ya isa haka Safreena ki tashi Mu bar wajan nan, Sannan ke a tunanin ki idan na basu wannan takardun zasu bar mu haka ne? wallahi kashemu za su yi, domin Dauda ba zai bari mu rayu ba kodan kar mu tona masa asiri gwanda Mu ci gaba da gudun ceton ran'mu, idan Allah yasa zamu rayu to ba Dauda ba ko namomin jejin babu abun da suka isa su yi mana."

         "Yaya Khalifa, zan sha ruwa, ba zan iya tafiya ba"
Shuru ya yi, yana nazari, juyawa ya yi ya kalli gabas, kudu, arewa, yamma, babu abin da ya kewaye su  ban da wasu bishiyoyi, wasu masu duhun gaske ya ce.
"Safreena babu ruwa anan, mu kara gaba ko zamu samu"  
Shuru ta masa kuma bata tashi ba.
"Ba za ki iya tafiyan ba da gaske?"
Ta gya ɗa masa kai alamun eh,
Durƙusawa ya yi ya ce "hau mu tafi"  ba musu ta hau bayansa ya ci gaba da gudu ya nayi yana juya baya.

***********
Bari Mu waiwaye tushen labarin.

Wacece SAFREENA.?
Wanene KHALIFA.?
_____

GUDU A JEJIWhere stories live. Discover now