7-8

133 6 0
                                    

🌳🌳🌳🌳🌳
       🌳🌳
     GUDU AJEJI
🌳🌳🌳🌳🌳
      🌳🌳

       Na

     Zahra Abdul

     (Momyn ahlan)

🌈kainuwa writers association✍🏻
Dashen Allah

Assalamu alaykum fans kuyi hakuri phone dina yasamu problem amma ga kadan kuyi manage

Bismillahi rahmanirrahim

🅿_7⃣➡8⃣

Dagota yayi ya hau jijjigata yana kiran sunanta safreena Dan Allah kitashi karki karaya a kwana 15 safreena kuka yasaka yana neman taimako amma babu mai taimako rungumeta yayi ya cigaba da mgn yana jijjigata amma ko motsi safreena batayi babu alamun sauran numfashi atare da ita

Gabaki daya ya rasa yadda zaiyi duk ya rude kallonta yasakeyi yana kuka safreena Dan Allah ki bude idonki karki mutu Dan Allah ki tashi kece karfin gwiwata na gudu ajejin nan Dan Allah kitashi

Ya kai kusan awa biyu awajan yana rungume da ita can kamar daga sama ya hango wasu halittun mutane maza su biyu jikinsu kayan fata ne daka gansu kaga qabilun jeji

Ihu ya hauyi yana kiransu bayin Allah taimako
Su kuma da sukaji ihu sun dauka wani naman jejin ne suka hau waige2
Can suka hango su khalifa wajansu suka karaso
Sai kallonsu suke SBD basu taba ganin halitta mai kyau kamarsu ba dayan cikinsu ne yasa hannu ya shafi fuskan khalifa yana murmushi khalifa kallon ikon Allah kawai yakeyi
Dayan ne shima ya miqa hannu zai shafi fuskan safreena da sauri khalifa ya buge hannunsa ya hade rai ya girgiza masa kai alamun aa ja da baya yayi

Mgn yake musu amma sun tsaya kallonsa SBD basu gane yaren da yakeyi shima kuma baya gane nasu da hannu ya musu alama da suna neman taimako

Mgn suka hauyi da Dan uwansa kamar fada fada
Bayan sun gama ne suka kalli khalifa suka masa alama da hannu sutafi

Tashi khalifa yayi ya dauki safreena kamar baby ahannu Wanda har yanzu bata motsi tafiya suka hauyi Wanda da kyar khalifa keyi SBD shima agajiye yake ga yunwa ga qishin ruwa
Sunyi tafiya kusan awa daya kafin su iso wani dan karamin kauye Wanda duka duka mutanen kauyen bazasu wuce 25 ba da yan bukkokinsu kanana
Sai kallonsu khalifa sukeyi da safreena wani Dan karamin bukka suka nuna masa ya kai safreena wajan
Bukkan yashiga yaga wata tsohuwa fuskanta duk ya yamutse murmushi ta masa
Sannan tayi masa nuni da gadon kara alamun ya kwantar da safreena akai ba musu ya kwantar da ita domin matar kamar mai magani ce

Fitowa yayi yana neman ruwa can ya hango wasu manya manyan tuluna da ruwa acike fal da wata gwangwani aciki dauka yayi ya hau shan ruwan nan kamar ba gobe  yan' kauyen sai kallonsa suke yana gamawa yafadi kasa asume da sauri suka daukesa suka kaisa wani bukka

Magani suka fara yi musu SBD gabaki daya kafarsu ta kumbura sannan wani waje ma harda yankan qaya

Dauda agaban wani mutum daka gansa gaka cikakken mugu marar imani da tausayi fuskarsa baqiqirim amurtuke ga tubi  babu alamun rahma shi karan kansa dauda rissinawa yayi agaban mutumin mai suna black snake

Dauda yafara mgn cikin rawar murya black snake taimako nazo kamin da mutanen ka wani dan iskan yarone ya gudu min da dukiyata shida wata yar'iskan yarinya na tura mutane sunfi aqirga amma sun kasa kamasu SBD gudu ajeji sukeyi wasu mutanen ma basu dawowa wai naman jeji ya cinyesu shine Nazo ka taimaka min wani abokina ne yabani lbrnka akan cewa idan kasa yaranka aiki mutum yasa aransa aikinsa yayi angana shiyasa nayi tattaki nazo tundaga abuja har lagos Dan Allah ka taimakeni black snake

Wanda aka kira da black snake ya kalli daya daga cikin yaransa yayi mgn yace idan harka yarda zaka raba dukiyar taka kashi uku mu dauki kashi biyu ka dauki daya zaro ido dauda yayi kafin yace haba dai ina ma laifi kuce arabata kashi biyu na dauki daya Ku dauki daya

GUDU A JEJIWhere stories live. Discover now