3-4

206 11 0
                                    

🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳

*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Fan's naji dadin comments amma Ku kara ngd Allah yabar qauna  💔💔

بسم ا لله لر حمن حيم

🅿_3⃣➡4⃣

Da haka dai har aka yi bikin Muhammad da Khadija suka tare akatafaren gidansu dake abuja a gwarimpa.

Babu yanda Muhammad bai yi da Dauda akan ya yi aure ba, amma ya ki ya ce shi bai ga matar da yake so ya aura ba.

Abin da Muhammad bai sani ba shi ne aure kwata-kwata baya gaban Dauda idan kuma wata bukatarsa ce to ya gwammaci ya je gidan karuwai ya dauki karuwa ya biyata ya biya bukatansa.

Babu kalar harin da Dauda baya kai wa Khadija da ta gano shi ta fadawa Muhammad, fada ya mata akan cewa
karta shiga tsakaninsa da Dan uwansa, hakuri ta basa daga nan ta shiga kulle kanta idan Muhammad baya nan.

Har ta fara laulayin ciki murna a wajan Muhammad baya misaltuwa ya yin da Dauda ya ji wannan lbrn, ji ya yi duniyar ta yi masa baqiqirim , yanzu idan Khadija ta Haifi namiji shi kenn duk wannan uban dukiyar zai zama mallakin dan'sa shi kuma miye makomarsa.

Babu kalar tuggu da munafurcin da Dauda bai shirya ba wajan ganin ya kawar da Muhammad da Khadija amma INA abun ya ci tura.

Har Allah ya sauketa lpy ta samu santaleliyar yarinyarta mace kyakkyawar gske mai kama da ita fara sol wato SAFREENA.

Lkcn da Dauda ya ga mace aka haifa ya danji sukuni kadan a cikin zuciyarsa.

Haka Khadija da Muhammad suka ci gaba rainon yar'su Safreena cikin kulawa da gata.

Har Safreena ta gama secondary skll dinta a wani skll mai suna
A,C,I,C academy abuja.

Safreena yarinya ce mai ji da kai kasancewar tana da kyau  ubanta kuma mai kudi sannan wulakancin a wajanta ba komai bane.

A wannan lkcn kuma Dauda babu abin da yake sha'awa kamar Safreena SBD dirin da  Allah ya mata,
Ta bukaci mahaifinta daya kai ta London domin ta yi university dinta a can, ba tare da bata lkc ba ya aminci SBD ita ke nan y'ar Dan Mommy bata sake haihuwa ba.

KHALIFA.

Driver ne a wajan Alhaji Muhammad Bello Badamasi 

Khalifa Dan garin katsina ne wani karamin local government mai suna dutsen Ma

Ya tashi a wajan Matar Babansa Wanda kwata-kwata, baya jin dadin zama dasu,
Tun yana karami yake sha'awar aikin   engineering.

Da buga-buga  yake yin kwadago yake biyan kudin makarantansa.

Har Allah yasa ya kammala degree dinsa anan dutsen ma.

Ya karanci abin da yake sha'awa wato engineer ya ta yawon neman aiki amma bai samu ba ga takuran da matar babansa take masa,
hakanne yasa ya kwashe kayansa yabar garin katsina
Ya koma abuja
A wata karaman unguwa farkon shigowa abuja wato maraba.

Nan ya samu wata garage da kyar ya roqa aka daukesa aiki  a wajan.

A cikin 2weeks ya yi wa ma'aikatan da ake ji dasu zarra,
Daga nan suka fara jin haushinsa su na masa baqin ciki.

GUDU A JEJIWhere stories live. Discover now